Godwin Obaseki: APC ta hana shi takara

Kwamitin da ke tantance 'yan takara na jam'iyyar APC a jihar Edo ya haramta wa gwamnan jihar Godwin Obaseki shiga zaɓen fitar da gwani wanda za a gudanar kafin tsayar da ɗantakarar gwamna.
Shugaban kwamitin, Jonathan Ayuba ne ya bayyana hakan yayin da ya ke bayar da rahoton ayyukan kwamitin ga shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole.
Ya bayyana cewa an haramta wa Obaseki tsayawa takarar ne sakamakon matsalar da ake ganin akwai tattare da takardun makaranta na gwamnan.
Sai dai a wani ɓangaren kuma, kafofin yaɗa labarai na Najeriyar sun ruwaito cewa Mista Obasekin ya ce ba zai ɗaukaka ƙara ba.
An dai kwana biyu zaman doya da manja tsakanin Obaseki da Shugaban Jam'iyyar APC Adams Oshiomhole, wanda hakan ya kawo rabuwar kai musamman a jam'iyyar APC reshen jihar Edo.
Gwamna Obaseki ne dai ya gaji Adams Oshiomhole bayan ya sauka daga gwamnan jihar a 2016.






