Sarauniya Elizabeth II: Hotunan rayuwar Sarauniyar Ingila

Asalin hoton, Yousuf Karsh / Camera Press

Bayanan hoto, Sarauniya Elizabeth II ta biyu ta zama basararakiya mafi dadewa a Birtaniya a shekarar 2015 tun bayan da ta zama sarauniya a shekarar 1952.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, An haifi Sarauniya Elizabeth a ranar 21 ga watan Afrilun shekarar 1926 a Landan. Ita ce 'ya ta farko ga Albert yariman York da kuma matarsa Elizabeth wadda aka fi sani da Lady Elizabeth Bowes-Lyon.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Sarauniya Elizabeth tare da kanwarta Margaret sun yi karatu ne a gida kuma ana iya ganinsu a nan suna wasa bayan kammala darasi.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Tun tana karama, Elizabeth kan daga wa jama'a hannu yayin da ta fito bainar jama'a.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Bayan murabus din Sarki Edward VIII a shekarar 1936 mahaifinta ya zama Sarki George VI, ita kuma ta zama sarauniya mai jiran gado.

Asalin hoton, Topical Press Agency / Getty Images

Bayanan hoto, A lokacin Yakin Duniya na II an dauke Elizabeth da 'yar uwarta zuwa Windsor, inda daga nan ne suka rika gabatar da shirin Children's Hour a kafar yada labarai ta BBC.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A shekarar 1947 ta auri Philip Mountbatten wanda dan uwanta ne kuma Yarima ne a kasar Girka da Denmark. Daga baya ya zama Yariman Edinburgh.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Yaronsu na farko Charles an haife shi ne a shekarar 1948.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Gimbiya Elizabeth tana gudanar da ayyuaka da dama - a nan tana mika kofin FA ne ga Billy Wright kaftin din kungiyar Wolverhampton Wanderers bayan sun doke kungiyar Leicester City a wasan karshe a filin wasa na Wembley.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Gimbiya da mahaifiyarta Sarauniya Elizabeth A shekarar 1951 a shekarar 1951 yayin da suke halartar bikin auren Lady Caroline Montagu-Douglas-Scott ga Mista Ian Hedworth Gilmour.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Mahaifin Elizabeth Sarki George VI ya rasu a ranar 6 ga watan Fabrairu na shelarar 1952 yayin da Elizabeth da Philip suke ziyara a kasar Kenya. Cikin gaggawa gimbiya ta dawo domin jana'izarsa. A nan suna tsaye daga bangaren hagu ita da mahaifiyarta, da kakarta, da Sarauniya Mary.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Elizabeth da gaggawa ta dawo gida, kuma an nada ta a matsayin sarauniya ne a cikin watan Yuni na shekarar 1953 a Westminster Abbey.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Baya ga ayyuakn ofis Sarauniya na zama tare da iyalanta - nan ita 'yarta ce Gimbiya Anne a ginin Windsor na Frogmore a shekarar 1959.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Ta koma filin wqasa na Wembley a shekarar 1966 don ta bai wa kaftin din tawagar Ingfila kyautar Jules Rimet ga kaftin din awagar 'yan wasan Ingila Bobby Moore bayan da ya jagorance su wajen lashe gasar cin Kofin Duniya, inda suka doke Jamus Ta Yamma a wasan karshe da ci 4-2.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Ma'auratan sun haifi yara hudu ne, kuma wannan hoto an dauke shi ne a Frogmore., Windsor. Daga hagu zuwa dama: Duke na Edinburgh (mijin Sarauniya), Yarima Edward, Sarauniya Elizabeth II, Yarima Andrew, Gimbiya Anne, da kuma Yarima Charles.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A watan Yuli na shekarar 1969 Sarauniya ta gabatar da Yarima Charles ga jama'ar Wales, jim kadan bayan bikin ba shi lakabin sarauta cikin kade-kade da bushe-bushe a Caernarfon Castle.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A lokutan mulkinta, an sha ganin Sarauniya tare da karnukan corgi. Alaka ta ginu ne tsakanin iyalan masarauntar da karnukan tun a shekarar 1933, lokacin da George VI ya sayo su a karon farko.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A shekarar 1977 'yan kasa sun yi murnar cikar Sarauniya shekara 25 a kan karagar mulki. Ta gaisa da mutane cikin nishadi annashuwa a lokacin da take rangadi a Birtaniya.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Sarauniya da Duke kenan suna daga wa jirgi hannu yayin da yake wucewa a lokacin da suke isa Barbados.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A watan Agustan 1979 dan uwan Sarauniya Lord Louis Mountbatten ya rasu bayan wata fashewar bam a kan jirgin ruwansa a kasar Ireland. Duke na Edinburgh ya koma Birtaniya daga kasar Faransa inda yake aikin horar da tuki a wata gasa jim kadan bayan samun labarin.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A shekarar 1981 babban dan Sarauniya Charles ya auri Lady Diana Spencer. Charles da Diana sun haifi yara biyu - William da Harry - kafin su rabu. Daga baya Diana ta rasu sakamakon wani hatsarin mota a birnin Paris na kasar Faransa.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Sarauniya da Duke na Edinburgh sun yi yawon bude-do sosai - nan suna kan Babban Bangon China ne a shekarar 1986.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A yayin bayaninta na Kirsimeti, Sarauniya ta bayyana shekarar 1992 a matsayin "shekarar annoba", inda ta nuna rashin dadinta ga yadda mutuwar aure ta yawaita da kuma gobara a Windsor Castle.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Bayan jam'iyyar Labour ta samu nasara a shekarar 1997, kalmar "Cool Britannia" na ci gaba da yaduwa. A nan Sarauniya tana gaisawa da rukunin mawaka 'yan Amurka Spice Girls wadanda wakarsu ta Wannabe ta zama lamba daya a kasashe 37 na duniya, ita ce kuma bakandamiyarsu.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Rasuwar Diana Gimbiyar Wales ta jawo suka daga kafafen yada labarai cewa Sarauniya ba ta fito bainar jama'a a kan kari ba.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A shekarar 2000 mahaifiyar Sarauniya ta yi bikin haihuwarta na shekara 100. - nan Gimbiya Margret ce da Sarauniya Elizabeth II.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Mutuwar mahaifiyarta wadda ta zo jim kadan bayan rauswar 'yar uwarta Gimbiya Margaret, ta sa an yi ta turo wa Sarauniya da sakonnin alhini a shekarar 2002 sanda ta yi bikin cikarta shekara 50 a karagar mulki a lokacin hunturu.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A shekarar 2005 Sarauniya Elizabeth shaida auren danta Yarima Charles a karo na biyu tare da Camilla Parker Bowles a Windsor Guildhall.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Elizabeth da mijinta Basaraken Duke na Edinburgh, Yariman Wales da Basarakiya Duchess ta Cornwell na huttawa a wajen shakatawa da ke gandun dajin tsaunin Braemar a Aberdeenshire. Wadannan 'yan sarauta sun kasance masu yawan kai ziyara wannan gandun dajin shakatawa tun zamanin Sarauniya Victoria, wadda ta fara kai ziyara wurin shekarar 1848.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A shekarar 2007 an dauki hoton Sarauniya ita kadai, tana fake wa ruwan sama lokacin da aka kaddamar da bude taron Kungiyar wasan kwallon hannu ta Lawn Tennis da Hedkwatarta a Roehamptom.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Sarauniya ta furta kalaman hikimar Groucho Marx kan lamarin da ya danganci tsufa a jawabin da ta gabatar wajen bikin zagayowar ranar haihuwarta shekara 80, cewa: "Kowa zai iya tsufa; abin da ya kamata daukacinku ku yi, shi ne, ku yi kokarin ganin kun rayu tsawon zamani." Bayan shekara guda, a shekarar 2007, Sarauniya ta yi bikin cikar zagayowar ranar aurenta 60 tare da Yarima Philips.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Mayun 2011 Sarauniya ta kasance mai sarautar Birtaniya ta farko da ta ziyarci Jamhuriyar Ireland. Ta ajiye furannin kallo a makabartar 'yan mazan jiya da ke Dublin, inda ta aiwatar da wani aiki da ke tattare da rudani a ziyarta. Abin da ta aikata yana da matukar muhimmanci saboda lambun (da ta dasa furannin kallon) an shirya shi ne don tunawa da mutane da suka yi yakin kwatar 'yancin mutanen kasar Ireland.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Al'amarin da ya fi faranta mata rai daga bisani cikin shekaru, shi ne auren jikanta Yarima William da Kate Middleton a shekarar 2011. A nan ne Yarima William da sabuwar amaryarsa Kate suka russuna a gaban Elizabeth.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Malfar Sarauniya saura kadan ta fadi daidai lokacin da ta iso gabar tsaunukan rundunar sojan sama ta RAF da ke Anglesley, inda suka ziyarci jikanta Yarima William, wanda aka tura shi aiki sansani daidai wannan lokacin.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Cikin shekarar 2011 Sarauniya ta kaddamar da ginin Rolls, wani kari fadada ginin gidan sarauta da aka yi wa Kotun Sarauta ta Shari'a da ke tsakiyar Landan.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A shekarar 2012 an ga Sarauniya ta yi bikin cikarta shekara 60 a karagar mulki, inda ruwa kamar da bakin kwarya ya cika kogin Peangeant da ke Thames.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Al'amuran da suka biyo bayan bikin daf-da-daf su ne gasar wasan olymfik da gasar wasannin nakasassu ta (Paralympics) da aka gudanar a Landan, inda aka gudanar da kayataccen bikin bazara a kasar. A nan ne Sarauniya ta kaddamar da bikin bude wasannin, inda aka ga ta tashi cikin lema a wajen bikin tare da James Bond (mashahurin mai shirin fina-finai).

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Shekaru sittin a baya ta taba kasancewa Basarakiyar farko da ta lashe gasar sukuwar dawakin sarauta ta Royal Ascot, a matsayinta na wadda ta mallaki bargar dawakai, ta lashe kofin zinaren gasar na 207, al'amarin da ya baibayeta da farin ciki ita da manajan tseren dawakinta, John Warren.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Da karfe 17: 30 (karfe biyar da rabi), ranar 9 ga Satumbar 2015, Elizabeth ta shafe kwanaki dubu 23,226 da sa'o'i 16 da kimanin mintuna 30 tana jan ragamar mulki inda ta zarta kakar babanta Sarauniya Victoria. Ta kwana guda a Scotland, inda ta yi godiya Ga masoya da suka yi mata fatan alheri a cikin kasar da kasashen waje saboda sakonninsu na "karamci masu sosawa da tausasa zukata." Tare da Yarima Philip ta yi tafiyar jirgin kasa mai rugugin hayaki daga Edingburgh zuwa Tweedbank, inda ta bude sabuwar iyakar Scotland na tashar jirgin kasa.

Asalin hoton, Steve Parsons/PA

Bayanan hoto, Sarauniya tare da iyalanta 'yan gidan sarauta sun yi bikin ranar haihuwarta cikin Yunin 2016. Elizabeth ta kasance Basarakiyar Birtaniya mafi jan zarenta a tsawon zamani, inda ta cika shekara 90 da haihuwa a watan Afirilu.

Asalin hoton, Lichfield / Getty Images

Bayanan hoto, "Lokacin da nake 'yar shekara 21, na yi alkawarin saraiyar da rayuwata wajen hidima ga mutanena, na kuma roki Ubangiji ya taimake ni in cimma burina na wannan kyakkyawar manufa. Kodayake wannan alwashin rantsuwa na yi shi ne cikin kuruciyata, lokacin da nake yanke hukunci gaba-gadi, ba na nadamar hakan, ko tunanin janyewa, ko da kalma guda daga cikinsa."

Dukkanin hotuna suna da hakkin mallaka.