'A bar Jihohi su biya albashi gwargwadon karfinsu'
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnan jihar Nassarawa a arewacin Najeriya ya bayar da shawarar cewa a bar kowace jiha ta tantance karancin albashi da za ta iya biyan ma'aikatanta.
An dade ana kiki-kaka kan albashi mafi karanci da gwamnatoci da kamfanoni za su biya ma'aikata a kasar ta Najeriya.
Bayan tattaunawa da kungiyar kwadago gwamnatin tarayyar kasar na ganin cewa Naira dubu 30 (Kimanin Dala 83) ne abinda ya dace a biya a matsayin karancin albashi.
Sai dai gwamnonin jihohi sun ce ba za su iya biyan hakan ba.
Gwamnan jihar Nassarawa, Umar Tanko Almakura ya ce a lokacin da wasu jihohin za su iya biyan sama da dubu 30 a matsayin karancin albashi ga ma'aikata, akwai jihohi wadanda a yanzu da kyar suke iya biyan Naira dubu 18, wato kimanin Dalar Amurka 50, wanda shi ne karancin albashin ma'aikata da ake amfani da shi a kasar.
Ya ce "Idan ka duba kudin da za a biya(Idan aka kara albashi), da kuma halin da ake ciki, jihohi da dama za su samu matsala sosai wurin biyan wannan kudi".
Gwamnan ya kuma ce za a samu matsala idan aka ce kananan jihohi su biya ma'aikata albashi daidai da na jihohi masu karfin tattalin arziki.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai