Hanyoyin sauƙaƙa raɗaɗin fitar haƙori ga jarirai

....

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Lokacin da jariri ya fara fitar da haƙori na ɗaya daga cikin muhimman matakai a rayuwarsa, amma kuma lokaci ne da ke zuwa da ƙalubale ga shi jaririn da iyaye.

Wasu jarirai kan yi kuka sosai a lokacin, wasu kuma su kasa barci, yayin da wasu ke nuna alamun rashin jin daɗi ta hanyar yawan saka hannu ko abubuwa a baki kamar yadda wata likitar yara Dr. Amina Bello ta bayyanawa BBC.

Wannan yanayi in ji lkitar kan sa iyaye cikin damuwa, suna neman hanyoyin da za su taimaka wa 'ya'yansu cikin sauƙi da aminci.

Dr. Amina ta bayyana cewa yawanci jarirai na fara fitar haƙori ne daga watanni shida, amma hakan na iya bambanta daga yaro zuwa yaro, inda ta bayyana alamomin da iyaye za su gane cewa yaransu sun fara fitar haƙori kamar haka:

  • Yawan saka hannu ko abu a baki
  • Yawan kuka fiye da yadda aka saba
  • Rashin iya yin barci yadda ya kamata
  • Kumburin dasashi
  • Zubar yawu fiye da ƙima
  • Rigima da rashin sukuni
....

Asalin hoton, Getty Images

Hanyoyin sauƙaƙa wa jariri raɗaɗin fitar haƙori

Dr. Amina Bello ta bayyana wasu hanyoyi masu sauƙi da iyaye za su bi domin rage wa jariri radadin da yake ji idan yana haƙori kamar haka;

Shafa dasashin jariri da abu mai sanyi

Likitar ta ce iyaye za su iya jiƙa ƙarama zani ko tsinma mai tsafta da ruwan sanyi ana shafa wa yaro a dasashinsa inda ta ce "Sanyin na taimakawa wajen rage kumburi da jin zafi a dasashi"

Amfani da abin wasa na cizawa (Teething Toy)

....

Asalin hoton, Getty Images

Dr. Amina ta ce bai wa jariri abin wasa na musamman da aka ƙera da yara ya dinga cizawa ya taimakwa wajen samun sauƙin ƙaiƙaiyi amma kuma likitar ta ce a tabbatar da cewa abin yana da tsabta a ko da yaushe kuma mai aminci kafin ba jariri.

Tausa dasashin jariri da hannu mai tsabta

Yi wa jariri tausa a dasashi na taimaka wa wajen sauƙaƙa raɗaɗi da ƙaiƙayi idan yarptausa a gumi da yatsu mai tsafta don rage kaikayi da jin zafi.

"Wannan na taimakawa jariri ya samu sauƙi cikin sauri." in ji likitar.

Guje wa amfani da magunguna ba tare da shawarar likita ba

Dr. Amina ta shawarci iyaye da kada su riƙa bai wa jarirai kowanne irin magani ko man shafawa ba tare da umarnin likita ba.

Ta ce, "Akwai wasu magunguna da ake shafawa a dasashin yaro, amma dole sai likita ya bada shawara kafin amfani da su."

Kula da tsafta da kuma yanayin barcin jariri

"Tsafta na da muhimmanci iyaye sun yi ƙoƙarin tsaftace hannaye da abin wasan taunawa da kuma zanin da ake jiƙa da ruwan sanyi kafin amfani." in ji likitan.

Ta ƙara da cewa "Tabbatar da cewa jariri na samun barci yadda ya kamata ta hanyar riƙe shi a hannu ko rungume shi, ko yi masa wanƙa na taimakawa rage damuwa da kaikayi

Abubuwan da ya kamata iyaye su guje wa

...

Asalin hoton, Getty Images

Likitar ta kuma yi gargadi kan wasu dabi'u da ake yi wanda ka iya cutar da jariri. Ta ce bai dace a ba jariri abu mai ƙarfi ko mai kaifi ya ciza ba, domin hakan na iya cutar da dasashinsa.

Haka kuma ta shawarci iyaye da su guji amfani da magungunan gargajiya marasa tabbacin inganci, domin wasu na iya haifar da illa ga lafiyar jariri.

Dr. Amina Bello ta jaddada cewa fitawar haƙorin jariri wani lokaci ne da ke wucewa, kuma yana buƙatar haƙuri daga iyaye.

"Abin da ya fi muhimmanci shi ne kulawa da jariri, tabbatar da tsafta, da kuma lura da duk wani canji da ba a saba gani ba," in ji ta.

Ga iyaye da dama, wannan lokaci na iya zama mai wahala, amma da fahimta da kuma bin shawarar masana lafiya, za a iya sauƙaƙa wa jarirai wannan mataki na rayuwa cikin kwanciyar hankali.