'Hukumar agaji ta bai wa mutane lalataccen abinci' a Ghana
Asalin hoton, Ghana
Hukumar kare afkuwar bala'i ta Ghana, NADMO ta amince cewa mataimakin shugaban kasar Mahamudu Bawumia, ya raba wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a arewacin kasar lalataccen man girki.
Man girkin wanda ya lalace a watan jiya, na cikin kayayyakin agajin da shugaban kasar ya raba.
Jami'an hukumar ta Nadmo sun ce an kebe man ne a wani dakin ajiya kuma kamata ya yi a ce an zubar da shi, amma sai aka yi kuskuren hada shi da kayayyakin agaji a lokacin da aka zuba su a mota.
A halin yanzu dai jami'an na yankin don karbo lalataccen man.
Sai dai kuma, wasu rahotanni na cewa ciwon ciki ya turnuke wasu mutane bayan sun ci abincin da a ka girka da man.
Mai magana da yawun kungiyar Nadmo, George Ayisi, ya shaida wa BBC cewa har yanzu ba a tabbatar da cewa halin da mutanen su ka fada na da alaka da man ba.
Mambobin jam'iyyar adawa ta kasar Ghana sun yi kira da a yi bincike kan yadda kuskuren ya faru.
Ambaliyar ruwan da aka yi a arewacin kasar Ghana ta kashe mutane fiye da 30, ta kuma raba dubban mutane da gidajensu.
Asalin hoton, Ghana
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai