Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Duk wanda bincike ya biyo ta kansa ba zai sha ba - Malami
Ministan shari'a na Najeriya, Abubakar Malami ya ce idan har bincike kan rashawa da cin hanci ya tarar da tsohon Shugaban kasar, Goodluck Jonathan, babu makawa za a iya bincikar sa.
Malami ya ce aikin binciken masu laifi karkashin shugabancin Shugaba Muhammadu Buhari babu zabe a ciki.
Abubakar Malami ya bayyana haka a kashi na biyu na hirar da editanmu na Abuja, Naziru Mika'ilu ya yi da shi.
Ku saurari yadda hirar tasu ta kaya.