Mai kamfanin Twitter ya tsananta wa ma'aikatansa  

Elon Musk ya fada wa ma’aikatan Twitter cewa dole su jajirce wajen yin aikin “ tsawon sa’oi ko kuma su bar kamfanin, a cewar rahotanni.

 

A cikin wani sakon imel  da ya aike wa ma’aikatansa sabon shugaban kamfanin  sada zumunta ya nemi ma’aikata da su amince da matakin idan suna son su ci gaba da aikinsu kamar yadda jaridar Washington ta ruwaito.

Wadanda suka ki sa hannu har ranar Alhamis za a ba su albashin sallama na watanni uku, in ji Mista Musk.

  

BBC ta ta tuntubi  Twitter a kan alamarin

 

A sakon da ya aikewa ma’aikatansa ta imel wanda  ita ma jaridar The Guadian ta gani , Mr  Musk ya ce sai kamfanin ya ‘’tashi tsaye haikan’’  idan yana son ya cimma nasara.

 

" Wannan na nufin za su shafe tsawon sa’oi suna aiki ba ji ba gani. Za a kyautatawa wadanda suka nuna kwazo ," in ji shi

An fada wa ma’aikatan cewa ana son su amince da wannan sako kafin yammacin ranar Alhamis idan suna son su kasance a cikin  sabon Twitter.

 

Ya kara  da cewa: " Duk shawarar da kuka yanke ina godiya ga kokarinkin da kuka rika yi domin kamfanin ya ci gaba."

Tun farko attajirin da ya fi kowa kudi a duniya ya sanar da sallamar rabin ma’aikatan Twitter bayan ya sayi kamfanin  a kan dala biliyan 44.

Mista Musk ya ce  "ba shi da wani zabi" a kan korar yayin da kamfanin  ke asarar dala miliyan 4 a kowace rana. Ya dora alhakin wannan komabaya a kan " kungiyoyi masu fafutuka da ke matsawa  kamfanonin masu talace talace " game da matukar raguwa a kudaden shigarsa".

 

Haka kuma an samu wasu manyan shugabannin kamfanin da suka sauka daga mukamansa  bayan  da ya sayi kamfani.

A makon daya gabata dan kasuwan ya fadawa ma’aikatansa cewa za a daina amfani da tsarin  nan na aiki a gida kuma za a shiga cikin wani “”hali na matsi" nan gaba a cewar rahotani.

 

A sakon imel din da ya turawa ma'aikatamsa,mamalakin kamfanin sada zumunta ya ce ma’aikatan za su rika aikin ofis na tsawon saoi 40 a kowani mako a cewar kafar yada labarai ta Bloomberg

 

Mista Musk ya kara da cewa  "ranar wanka ba a boyan cibi"  kuma tafiyar hawainiyyar da tattalin arzikin duniya ke yi  zai shafi kudin da kamfanin yake samu

 

Sai dai Sarah Kunst wadda kwarariyar ce a harkar fasaha  ta ce dailin da yasa Twitter ke fusnkantar matsaloli shi ne cewa  tsarin da Mista Musk ya bi  wajan sayen kamfanin ya bar kamfanin da bashi

 

Ta kuma ce dabi'arsa tun bayan da ya sayi kamfani ta wasu masu tala -talace  sun dakatar da kudadensu.

 

"A yanzu yana neman ya huce haushinsa a kan ma'iakatan ta hanyar sanya musu fargaba ta rashin tabbas a aiki da kamfanin.," in ji ta

 

Ta kuma kara da cewa akwai alamar tambaya  a kan yada za a aiwatar da  wannan tsari na tsawon sa'oin da ma’aikata za su rika aiki.

 

  " Shin za ka iya  aika da imel kawai ga ma’aikata da ke maka aiki kuma kawai sai ka sauya kwantiragin aikinsu ba tare da izinin wasu ba? Wannan abin a jira a gani ne