Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyara birnin Jos a yau Alhamis, biyo bayan harin da aka kai ranar Lahadi da ta gabata wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 25.
Shugaban ya ce manufar ziyarar ita ce jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.
Ya ce, “Babban abin da ya rataya a wuyana a wannan lokaci shi ne tsayawa tare da al’ummar Plateau, waɗanda ke ƙoƙarin yaɗa tsoro ba za su yi nasara ba. Za mu ci gaba da ƙarfafa matakan tsaro tare da tabbatar da an yi adalci.”
Ziyarar na zuwa ne kwanaki huɗu bayan harin, inda shugaban ya soke wata tafiya da ya shirya zuwa Ogun da wasu jihohi domin ayyukan more rayuwa da kasuwanci da bunƙasar tattalin arziki.
Jihar Plateau, inda Jos take, ta daɗe tana fama da rikice-rikice masu alaƙa da bambancin ƙabilu da addinai, da kuma rikicin makiyaya da manoma.
Har yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin harin na baya-bayan nan.
Mahukunta sun sanya dokar hana fita na kwanaki biyu a ranar Litinin domin dawo da zaman lafiya, amma an sake samun tashin hankali a ranar Laraba a yankin Angwan Rukuba bayan sassauta dokar.