Da gaske matsalar tsaro ta fi ƙaruwa gabanin zaɓe a Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Ƴan Najeriya na ta muhawara kan kalaman da shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Godswill Akpabio ya yi cikin wannan mako game da alaƙar matsalar tsaro da zaɓen ƙasar na 2027 da ke tafe.

Yayin da yake jawabi a lokacin ƙaddamar da sabuwar shalkwatar hukumar haraji ta ƙasar a Abuja, babban birnin ƙasar, Sanata Akpabio ya yi zargin cewa matsalar tsaron da ke ƙara tsananta a ƙasar maƙarƙashiya ce kawai ake shirya wa shugaban ƙasar, Bola Tinubu.

Ya ce: ''Ina tabbatar ma, (shugaban ƙasa), mako biyu bayan ka ci zaɓen (2027), za a daina kai harin bama-bamai. Mutane na ɗaukar nauyin kai hare-haren ne domin kawar da hankalinka daga aikin da kake yi.''

''Kana ƙoƙari sosai duk da irin maƙarƙashiyar da ake yi wa gwamnatinka,'' in ji shi.

Baya ga shugaban majalisar dattawan akwai wasu ma da ke ganin ƙaruwar matsalar tsaron da ƙasar ke fuskanta a wannan lokaci na da alaƙa da zaɓen 2027 da ke tafe.

Sai dai a gefe guda wasu na sukar Sanata Akpabio da masu tunani irin nasa da cewa maimakon su mayar da hankali wajen yaƙi da matsalar, sun ɓuge da siyasantar da batun tsaro, wani abu da masana ke gargaɗi game da shi.

Da gaske matsalar tsaron na da alaƙa da zaɓe?

Asalin hoton, Getty Images

Dr Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Security mai nazari kan sha'anin tsaro a Najeriya ya ce bisa bincike da tattara bayanai da kamfaninsa ke yi sun tabbatar da samuwar alaƙar matsalar tsaro da zaɓukan Najeriya.

''Haka batun yake, alƙaluman da muke tattarawa sun nuna haka, kuma tun shekarar 2007, duk lokacin da aka buga gaggar siyasa akan samu ƙaruwar matsalar tsaro a ƙasar'', in ji shi.

Masanin tsaron ya ce siyasa na da ɓangarori guda biyu, na cikin gida da kuma siyasar ƙasashen waje.

''A cikin gida akwai waɗanda ke kafa ƙungiyoyi da amfani da su wajen tayar da rikici, haka ma mazauna ƙetare'', in ji shi.

Dr Kabiru Adamu ya bayar da misali da ɗage zaɓe da aka yi saboda dalilai na tsaro a lokacin mulkin tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan.

Me ya sa ake samun ƙaruwar matsalar gabanin zaɓe?

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masanin tsaron ya ce wasu daga cikin ƙungiyoyin da ke tayar da hankali a ƙasar na da alaƙa da siyasa.

''Sannan kuma wasu daga cikin ƴansiyasar na da hannu a kafuwa da ayyukan wasu daga cikin waɗannan ƙungiyoyi domin cimma burinsu na siyasa'', in ji shugaban kamfanin na Beacon Security.

Masanin tsaron ya bayar da misali da cewa idan wani ɗan siyasa ya fahimci cewa yana da matsalar karɓuwa a wani yanki, to zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin ba a yi yaƙin neman zaɓe ba, ko ma ba a yi zaɓe ba.

Dr Kabiru Adamu ya jaddada cewa akwai hannun wasu ƴansiyasa a ayyukan wasu ƙungiyoyin masu riƙe da makamai a Najeriya.

''Wani misali da kowa zai yarda da hakan shi ne, duk lokacin da aka sace ɗalibai a makarantu, za ka ga gwamnati ta yi tuntuɓa an kuma saki ɗaliban ba tare da cutar da su ko halaka su ba''.

''Wannan kaɗai ya isa a fahimci cewa ƴan siyasa na da laƙa da wasu daga cikin waɗannan ƙungiyoyi, sun sansu sun kuma san inda suke'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Rashin tsaron kan yi tasiri a lokacin zaɓe?

A duk lokacin da aka samu wata matsala ta tsaro, akan ji mutanen yankin da abin ya faru da ɗora alhakin hakan kan shugabanni.

Haka ma ƴansiyasa kan yi amfani da matsalar wajen sukar shugabannin da suke adawa da su musamman a lokutan yaƙin neman zaɓe.

To ko matsalar na yin tasiri a zukatan masu kaɗa ƙuri'a a lokacin zaɓe?

Dr Kabiru Adamu ya ce ko shakka babu matsalar tsaro na yin tasiri a lokacin zaɓe.

''Tsarin siyasar ƙasar haka yake, gwamnati na son nuna wa jama'a cewa tana samun ci gaba a matsalar tsaro, yayin da a gefe guda ƴan hamayya kan yi amfani da matsalar wajen sukar gwamnati'', in ji shi.

''Don haka zaɓi ya rage wa masu kaɗa ƙuri'a, idan sun yarda da gwamnati su bi ta, in kuma sun yarda masu suka su bi su'', a cewar masanin tsaro.

Ya kuma ƙara da cewa masu sukar ka iya ƙara rura wutar rikicin, don nuna wa jama'a nakasun gwamnatin.

''Misali a Zamfara an yi lokacin da aka hana gangamin yaƙin neman zaɓe a wasu yankuna, kuma daga baya, bayanai suka fito cewa wasu ƴansiyasa ne suka kitsa batun'', in ji shi.

Masanin tsaron ya kuma ce matsalar tsaron kan sanya hukumar INEC ɗage zaɓuka, saboda dalilai na tsaro.

''Hakanan akan yi amfani da tsaro don juya akala/ ko sakamakon zaɓen'', in ji shi.

'Bai dace gwamnati ta fake da siyasa wajen kasa magance matsalar tsaro ba'

Duk da cewa matsalar tsaro na da alaƙa da siyasa, amma Kabiru Adamu ya ce bai kamata gwamnati ta kafa hujja da siyasa wajen kasa magance matsalar ba.

''Wannan kuskure ne, kuma rashin ɗaukar haƙƙi da muhimmanci ne, dokokin Najeriya sun ɗora wa gwamnati haƙƙin kare ƴan ƙasa, don haka ba zai zama hujja ba don an ce akwai siyasa, gwamnati ta yi sakaci game da batun ba'', in ji shi.

Masanin tsaron ya ce wajibi ne gwamnati da masu riƙe da madafun iko su magance matsalar tsaro.

''Babu dalilin da zai sa gwamnati da masu riƙe su kasa magance matsalar tsaro saboda kawai suna zargin akwai siyasa a ciki'', in ji shi.