Arsenal ta gamu da turjiya kan Kvaratskhelia, Man U da Liverpool na zawarcin Tchouameni

Asalin hoton, Getty Images
Adam Wharton na son barin Crystal Palace a wannan bazarar, inda dan wasan tsakiyar mai shekara 22 ke son komawa wata kungiyar da ke buga UEFA Champions League. (The Sun)
A wani labarin kuma, Brighton & Hove Albion sun sassauta matsayinsu kan sayar da dan wasan Kamaru Carlos Baleba, kuma ana sa ran za su amince da tayin da ya yi kasa da fam miliyan 100 da suka bukata a bara. (The Sun)
Arsenal na nazarin yiwuwar daukar Elliot Anderson daga Nottingham Forest, yayin da Manchester City, Manchester United da kuma Chelsea ke zawarcin dan wasan. (CaughtOffside)
Manchester United da Liverpool na zawarcin dan wasan Faransa na Real Madrid Aurelien Tchouameni. (Fichajes)
Haka kuma Liverpool da Arsenal sun gamu da turjiya wajen kokarin daukar dan wasan gefe na Paris Saint-Germain Khvicha Kvaratskhelia. (Teamtalk)
An kuma bai wa Manchester United damar daukar dan wasan Sifaniya Ferran Torres daga Barcelona a wannan bazarar. (Teamtalk)
Juventus na kokarin daukar dan wasan Poland Robert Lewandowski kyauta idan ya bar Barcelona a bazarar nan. (La Gazzetta dello Sport)
Juventus din na kuma sha'awar tsohon dan wasan Ingila Mason Greenwood, amma Atletico Madrid na matsa kaimi wajen daukarsa daga Marseille. (La Gazzetta dello Sport)
Kocin Sifaniya Luis Enrique na shirin kin amincewa da tayin Manchester United tare da sabunta kwantiraginsa a Paris Saint-Germain, lamarin da zai zama koma baya ga kungiyar ta Ingila. (i newspaper)
Tottenham Hotspur na iya komawa ga Sean Dyche domin ceton kungiyar daga nutsewa daga gasar Premier, idan Roberto De Zerbi ya dage cewa sai bayan kakar wasa zai karbi aikin. (The Telegraph)
A karshe, Everton na shirin ba David Moyes sabon kwantiragi, sakamakon yadda ya sauya fasalin kungiyar daga masu fuskantar barazanar nutsewa zuwa masu fafutukar samun gurbi a Turai a kakar nan. (The Guardian)











