Wane ne Pete Hegseth, tsohon mai gabatar da shirye-shirye a Fox News da ya zama sakataren tsaron Amurka?

.....

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

Tsohon mai gabatar da shirye-shirye a Fox News, wanda yanzu ya zama ɗaya daga cikin masu kare yaƙin Amurka da Iran, ya nuna irin salon sa na tsauri da rashin sassauci a wannan sabon matsayi.

Fiye da makonni uku ke nan da fara yaƙin da Amurka ta kira Operation Epic Fury kan Iran, wani farmaki da aka ƙaddamar tare da haɗin gwiwar Isra'ila domin lalata makaman roka na Iran da kuma kawo ƙarshen duk wani yunƙuri na mallakar makaman nukiliya.

A cikin wannan yanayi, Sakataren Tsaron Amurka Pete Hegseth ya bayyana cewa wannan farmaki na "murƙushe abokan gaba," yana kuma kiran su da "'yan ta'adda marasa jarumta."

A yanzu yana da shekara 45, kuma shi ne na biyu mafi ƙarancin shekara da ya taɓa riƙe muƙamin Sakataren Tsaro a tarihin Amurka. Duk da haka, naɗin nasa ya janyo ce-ce-ku-ce da dama.

Daga ciki har da zargin fallasa bayanan sirri game da hare-haren Yemen ta hanyar wata manhajar sadarwa, da kuma zarge-zargen rashin da'a da suka taso a lokacin tantance shi kafin karbar muƙami.

Tambayar da ake yi ita ce: wane ne Pete Hegseth, kuma ta yaya tsohon mai gabatar da shirye-shirye a Fox News ya kai ga zama Sakataren Tsaron Amurka?

....

Asalin hoton, Getty Images

Matashin da ba ya shiru

An haifi Pete Hegseth a watan Yunin shekarar 1980 a jihar Minnesota, inda shi ne na farko a cikin ƴaƴa uku a gidansu. Mahaifinsa, Brian, malamin koyar da ƙwallon kwando ne a makarantar sakandare, yayin da mahaifiyarsa, Penelope Hegseth, ta kasance babbar mai ba da shawara kan sana'a, kuma an ce ta fito daga gida mai tsattsauran ra'ayin Kiristanci.

Hegseth ya karanci kimiyyar siyasa a jami'ar Princeton, inda ya riƙa rubuce-rubuce a mujallar masu ra'ayin mazan jiya ta jami'ar mai suna Princeton Tory. Tun a wancan lokacin ne yake da ra'ayin jam'iyyar Republican mai tsauri, inda yake da wani shafi mai suna "Rent," wanda a ciki yake muhawara da ƙungiyoyin mata da kuma na 'yan LGBTQ, yana nuna adawa da zubar da ciki, da batun luwadi, da kuma manufofin "haɗa kai"

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A lokacin karatunsa, ya fi karkata ga motsa jiki da horon soja. Ya shiga shirin horas da jami'an soja na jami'a, wato Reserve Officers' Training Corps (ROTC), wanda daga baya ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarsa ta aiki.

Bayan kammala karatu a 2003, ya fara aiki a rundunar sojin Amurka a matsayin jami'in sojojin ƙasa, inda ya kasance mai goyon bayan yaƙin da aka kira Global War on Terror da tsohon shugaban Amurka George W. Bush ya ƙaddamar.

Ya yi aiki a sansanin Guantanamo Bay da kuma a Iraƙi, inda ya samu lambar yabo ta Tagulla. Daga baya an tura shi Kabul a Afghanistan, inda ya yi aikin horas da sojoji kan dabarun yaƙi da masu tayar da ƙayar baya.

Bayan ya bar aikin soja, ya koma Amurka inda ya jagoranci wasu ƙungiyoyin tallafawa tsoffin sojoji na wani lokaci. Sai dai wani rahoton mai fasa ƙwai da mujallar The New Yorker ta samu ya nuna cewa wasu daga cikin abokan aikinsa sun zarge shi da yawan shan giya da kuma halayen da ba su dace ba a wuraren aiki.

Mai gabatarwa mai cike da taƙaddama

Tun tsakiyar shekarun 2010, Pete Hegseth ya zama shahararre a gidan talabijin na Fox News saboda yanayin shigarsa da yadda yake shafe gashinsa zuwa baya.

Ya shiga wannan gidan talabijin ne a 2014, da farko a matsayin ƙwararre, sannan daga baya a matsayin mai gabatar da shiri. A wannan matsayi, ya yi amfani da dandamalin nasa wajen tattaunawa kan batutuwan soja da tsoffin sojoji, ciki har da kare sojojin da aka same su da laifin aikata laifukan yaƙi.

....

Asalin hoton, EPA

Pete Hegseth ya auri Jennifer Raucht, wata mai shirya shiri a Fox & Friends, a shekarar 2019.

Kafin wannan, ya riga ya yi aure sau biyu. Aurensa na farko ya ƙare a 2009 bayan ya amince da yin soyayyar sirri da dama. Daga baya, ya samu yara uku da matarsa ta biyu. Duk da cewa yana tare da matarsa ta biyu, ya kuma haifi ɗa tare da Jennifer Raucht, wacce daga baya ya aura.

A lokacin rikicin saki da matarsa ta biyu, mahaifiyarsa ta bayyana shi a cikin wani imel a matsayin "mutumin da ya tsani mata" (misogynist). Daga baya ta ce ta riga ta roƙe yafiya ga ɗanta a wani imel daban.

Shigarsa Pentagon

A cikin shekaru takwas da ya yi a matsayin mai gabatarwa tare da shirin ƙarshen mako na Fox & Friends, Pete Hegseth ya jawo hankalin ɗaya daga cikin masu kallo na yau da kullum na shirin, wato shugaban Amurka, Donald Trump.

Bayan da Trump ya lashe zaɓen shugabancin ƙasa karo na biyu, ya ɗauki Hegseth daga mai gabatarwa a gidan talabijin na Fox news zuwa Pentagon, inda ya naɗa shi Sakataren Tsaro. Wannan shawara ta ba da mamaki ga mutane da dama.

A watan Janairu na 2025 ne majalisar dattijai ta amince da naɗin Hegseth a mukamin Sakataren Tsaro amma hakan ya zo da ƙalubale kaɗan yayin da tantance shi ya zo da zarge-zargen cin zarafi ta hanayar lalata da kuma yawan shan giya.

Hegseth dai ya ƙaryata dukkan waɗannan zarge-zargen.

An kuma yi la'akari da ra'ayinsa kan addini ma.

Masu sukar sa sun yi ƙoƙarin danganta zanen jikinsa, wanda suka nuna alamomin yaƙar ko mamaye aƙidar da ba ta Krista ba da ra'ayin siyasarsa mai tsauri. Hegseth ya ce waɗannan tamburan kawai suna nuna bangaskiyarsa ta Kirista.

Wasu kuma sun yi tambaya ko yana da isasshen ƙwarewa don tafiyar da babbar hukumar tsaron gwamnatin Amurka, , wacce ke da kasafin kuɗi kusan dala tiriliyan 1 kuma ke ɗaukar ma'aikata miliyan uku.

....

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images

Pete Hegseth ya fuskanci ce-ce-ku-ce na farko ba da jimawa ba bayan an rantsar da shi. A wancan lokaci, a saka wani ɗan jarida bisa kuskure a cikin wani zauren aikewa da saƙonni inda Sakataren Tsaron ya bayyana cikakkun bayanai na shirin kai hari kan ƙungiyar Houthi mai samun goyon bayan Iran a Yemen.

Mambobin Majalisar Dokoki da wasu sun nemi a kore shi, suna cewa ya sa rayukan sojojin Amurka cikin haɗari kuma ya saba ƙa'idoji. Amma duk da haka, Hegseth ya ci gaba da riƙe mukaminsa..

Hegseth ya sake wa wasu sansanonin soja suna kuma ya rage haɗin gwiwar tsaro da jami'o'i, ciki har da jami'ar da ya yi karatu a ciki, jami'ar Harvard.

A ƙarƙashin jagorancinsa, Pentagon ya sake rubuta ƙa'idojin mu'amala da kafafen watsa labarai.

Amma Sakataren Tsaron yana son nuna cewa shi, kamar yadda yake son a girmama soja ta Amurka, ba mutum ne da zai ja da baya ba.

Mutumin da ba ya tsoro a fagen daga

Yayin da rikice-rikice ke ci gaba a Gabas ta Tsakiya, tambayoyi kan yiwuwar hannun Amurka a harin da aka kai wata makaranta a Iran sun kai ga Pete Hegsett.

A ranar 12 ga Maris, 'yan majalisar dattawa na Democrat a Amurka sun aiko masa da wasiƙa suna neman bayani kan harin da jami'an Iran suka ce ya yi sanadiyar mutuwar mutum 168, ciki har da kusan yara 110.

Jaridar Amurka ta ruwaito cewa masu binciken sojoji na ƙasar na da yaƙinin cewa sojojin Amurka sun kai hari kan makaranta ne da gangan ba a farkon hari da suka kai Iran tare da haɗin gwiwar Isra'ila.

Pete Hegsett ya ce Amurka ba ta nufin harin fararen hula kuma ana gudanar da bincike kan lamarin.

Idan an tabbatar, wannan zai zama daya daga cikin harin da ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula mafi tsanani a shekarun da Amurka ke cikin Gabas ta Tsakiya.

Am matsayinsa na sakataren tsaro a Amurka, Hegseth na gabatar da kansa a matsayin jarumi a fagen dage.

Matthew Walling, darektan ayyukan tsaro na Amurka, ya ce Pete Hegsett yana magana da karfi da isa da nuna jarumta, kuma wannan yana daga cikin hoton da yake nunawa duniya.