Waɗanne buƙatu Trump ya gabatar ga Iran, me ya sa Tehran ta yi watsi da su?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Paulin Kola
- Lokacin karatu: Minti 4
Iran ta yi watsi da buƙatu 15 da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar na son kawo karshen yaƙi da ake gwabza wa, a cewar gidan talabijin na ƙasar.
Gidan talabijin ɗin ta ambato wani babban jami'in ƙasar na cewa ita ma Tehran ta gindaya sharuɗa biyar da take son a aiwatar kafin kawo karshen rikicin, ciki har da biyan diyya na lalata kayayyaki.
Ba su yi kama da buƙatun Trump ba, wanda gidan talabijin na Isra'ila Channel 12 ya wallafa bayan amincewa da su da jami'an Amurka suka yi. Sun haɗa da cewa dole ne Iran ta dakatar da shirin mallakar makaman nukiliya da kuma sake buɗe mashigar Hormuz mai muhimmanci.
An fara yaƙin ne ranar 28 ga watan Fabrairu bayan da Amurka da Isra'ila suka kaddamar da hare-hare ta sama, inda daga bisani Iran ta soma kai hare-hare ga ƙawayen Amurka a yankin Gulf.
A ranar Talata, Trump ya ce Iran ta "matsu" a tattauna sannan masu shiga tsakani na Iran sun bai wa Amurka "babban abin da suke son a yi".
Tattaunawar ta ta'allaka kan mai da iskar gas da kuma mashigar Hormuz, a cewar shugaban Amurkar ba tare da bayar da ƙarin bayani ba.
Sai dai kakakin majalisar dokokin Iran ya yi watsi da tayin tattaunawar.
"Babu wata tattaunawa da ta gudana da Amurka, maganar ƙarya ce kawai don dagula hada-hadar kuɗaɗe da kuma kasuwannin mai da kuma son fita cikin tsaka mai wuya da Amurka da Isra'ila suka shiga," kamar yadda Mohammed Bagher Ghalib ya rubuta a shafin X.
Me buƙatun Trump suka kunsa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cewar gidan talabijin na Isra'ila, dole ne Iran ta cika wasu sharuɗa kafin a kawo karshen yaƙin.
Sun ta'allaka kan cewa Iran za ta soke shirinta na samar da makaman nukiliya - wanda abu ne da ba a goyi baya ba da kuma Iran ta yi watsi da shi.
Buƙatar Trump ta bayyana cewa dole ne Iran "ta amince cewa ba za ta sake samar da makaman nukiliya ba", ta kuma yi alkawarin cewa za ta wargaza tashoshin nukiliya da kuma miƙa albarkatun uranium ɗin ta ga Hukumar sa ido kan ayyukan nukuliya ta Majalisar Ɗinkin Duniya IAEA.
A cewar buƙatun da Amurkar ta gabatar, akwai buƙatar Iran ta amince wajen rage shirinta na makaman linzami.
Har ila yau, Amurka na kuma son Iran ta daina bai wa ƙawancen ƙungiyoyi da take alaƙa da su a yankin kuɗaɗe - Hezbollah a Lebanon, Hamas a Gaza da kuma Houthi a Yemen.
Ana kuma son Iran ta sake buɗe mashigar Hormuz don ya koma aiki kuma kowa ya samu damar amfani da mashigar. Rufe mashigar - wadda kashi biyar na mai da iskar gas ke bi zuwa duniya - ya janyo ƙaruwar farashi da kuma fargabar cewa tattalin arzikin duniya zai samu tawaya.
Ba ya ga haka, za a ɗage dukkan takunkumi kan Iran, in ji Amurka.
An kakabawa Iran takunkumai a watan Nuwambar bara bayan da Tehran ɗin ta soke shirin masu zuwa sa ido lokacin da Amurka da Isra'ila suka yi ruwan bama-bamai a cibiyoyin nukuliyar Iran da dama da kuma sansanonin soji.
Waɗanne sharuɗa ita kuma Iran ta gabatar?
Iran ya bayyana jerin sharuɗa biyar da ta ce sai an cika su kafin a kawo karshen yaƙi, a cewar gidan talabijin na ƙasar.
Sun haɗa da dakatar da mamaya da kuma kisan gilla da Amurka da Isra'ila ke yi.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da jami'ansa sun sha cewa za su "yanke kan abokan gaba". An kashe manyan jami'an Iran da dama tun a ranar farko ta fara yaƙi lokacin da wani gagarumin hari a Tehran ya janyo rasuwar jagoran addinin ƙasar Ayatollah Ali Khamenei.
Sauran sharuɗan Iran sun haɗa da "ɗaukar matakai na ganin ba a sake takalar Jamhuriyar Musulunci da yaƙi ba", duk da cewa ba a san abin da za a amince da shi ba sannan waɗanne ƙasashe za su shiga tsakani - ko kuma sa ido.
A ɓangaren tattalin arziki, Iran na son a biya ta diyyar kayayyaki da aka lalata mata a yaƙi, da kuma barin ƙasar ta kasance ita kaɗai ke iko da Mashigar Hormuz.
Abu mafi muhimmanci kuma shi ne, Tehran na son Isra'ila ta kawo karshen hare-hare da take kai wa ƙawayenta a Gabas ta Tsakiya.
Isra'ila ta matsa ƙaimi wajen kai hare-hare kan Hezbollah, inda ta sanar ranar Talata cewa sojojinta za su faɗaɗa hare-hare a Lebanon har sai an daina kai hari arewacin Isra'ila.
Jami'in da bayyana sharuɗan wanda ba a faɗi sunansa ba, ya ce waɗannan sharuɗa ƙari ne kan waɗanda Iran ta gabatar a baya lokacin tattaunawar Geneva, wadda aka yi a watan Fabrairu, jim kaɗan kafin fara yaƙin.
Shin an kusa kawo karshen yaƙin?
Akwai yiwuwar jakadun zaman lafiya na Trump ne za su jagoranci duk wani yiwuwar tattaunawa, waɗanda suka haɗa da Steve Witkoff da kuma Jared Kushner.
Tayin tattaunawar ta Amurka ta yi kama da irin wanda jakadun suka yi amfani da shi domin kawo karshen yaƙin sama da shekara tsakanin Isra'ila da Hamas a Zirin Gaza.
Idan ana son kwaikwayon irin hanyar, dole sai an sanar da tsagaita wuta domin bai wa masu shiga tsakani damar zama don duba daftarin da Amurka ta gabatar.
Gidan talabijin na Isra'ila Channel 12 ya ce shugabannin ƙasar ba za su ji daɗin dakatar da hare-haren da suke kai wa Iran ba a wannan lokaci - Netanyahu ma na da irin wannan ra'ayi na tsagaita wuta lokacin da ake tattaunawar Gaza.
Ministan tattalin arziki na Isra'ila Nir Barkat ya faɗa wa BBC cewa zai yi wuya Iran ta amince da buƙatun Trump.
"Na yi imanin cewa a karshen wannan tattaunawa, za mu cimma burin mu, ko da an cimma yarjejeniya ko akasin haka," in ji Barkat.
Babu dai tabbacin waye zai jagoranci shiga tattaunawa daga ɓangaren Iran.
Trump bai faɗi wanda yake tattaunawa da Amurka ba - kawai ya ce "muna magana da mutanen da suka dace".
Ba a ga sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei ba - tun bayan gadar mahaifinsa.
Babu alamun cewa za a saka sabon jagoran addinin Iran Mojtaba Khamenei cikin tattaunawar ba, wanda ba a gani a fili ba tun bayan samun rauni a harin da ya kashe mahaifinsa ranar 28 ga Fabrairu.
Buƙatar tattaunawar na zuwa ne a daidai lokacin da dubban sojojin Amurka suka nufi Iran.
Ba a dai san me za su je yi ba, sai dai rahotanni sun ce za a iya amfani da su wajen buɗe Mashigar Hormuz ko kuma ƙwace yanki a Iran.











