Abin da muka sani kan 'kisan' Birgediya Janar Oseni Braimah

Asalin hoton, Nigerian Armed Forces

    • Marubuci, Tunde Ososanya
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
    • Aiko rahoto daga, Lagos
  • Lokacin karatu: Minti 6

Bayanai na ci gaba da fitowa dangane da batun kisan babban kwamandan ƙaramar rundunar sojin Najeriya ta 29 Join Task Force Brigade da ke aiki ƙarƙashin rundunar Operation Hadin Kai, Birgediya Oseni Braimah.

Rahotonni sun ce kwamandan rundunar ya mutu ne lokacin wani hari da mayaƙan Boko Haram suka kai wa sansanin sojin da yake jagoranta a garin Benisheikh na yankin ƙaramar hukumar Kaga a jihar Borno.

Ɗaya daga cikin jagororin al'ummar yankin, Zanna Lawan Ajimi ya shaida wa BBC cewa Birgediyar Janar Braimha na daga cikin sojojin da ƴanta'addan suka kashe a lokacin gurmurzun.

"An kashe shi a harin. Mun tabbatar da haka daga majiyar soji da kuma jami'an haɗin gwiwa na farar hula JTF, waɗanda suka kai ɗauki bayan faruwar lamarin. Akwai farar hula ɗaya da shi ma ya rasu, yayin da guda ya samu rauni,'' a cewar Ajimi.

"Sun kai hari garuruwan Benisheikh da Ngamdu, da ke yankin ƙaramar hukumar Kaga. Sojojin sun samu nasarar kashe ƴanbindigar da dama a garin Ngamdu."

To sai dai cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran ayyukan soji a shalkwatar tsaron ƙasar, Manjo Janar Michael Onoja ya fitar a ranar Alhamis ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfi 12:30 da dare a cikin shalkwatar ƙaramar rundunar sojin da ke garin Benisheikh.

Sanarwar ta ce dakarun ƙasar sun samu nasarar daƙile wani mummunan hari da ƴan'adda suka kai wa ɗaya daga cikin sansanonin soji a jihar Borno.

Manjo Janar Onoja ya ce ƴanbindigar sun yi yunƙurin shiga sansanin, inda ya ce sojojin rundunar ta 29 Task Force Brigade sun mayar da martani da abin da ya kira ''ƙwarin gwiwa cikin ƙwarewa da ƙarfin makamai,'' inda suka tilasta wa ƴanta'addan ja da baya.

Janar Onoja ya ce Birgediya Janara Braimah ya jagoranci dakarunsa wajen far wa ƴanbindihgar lamarin da ya ce ya sa ƴanbindigar ''haƙura da muradinsa tare da tserewa suka bar wasu daga cikin makamansu''.

"Sai dai abin takaici, lamarin ya haifar da rasa rayukan wasu ƙwarazan sojoji da suka mutu a ƙoƙarinsu na kare ƙasarsu,'' in ji shi.

Asalin hoton, JORIS BOLOMEY/AFP via Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Manjo Janar Onoja bai bayyana sunaye da adadin sojojin da suka mutu ba. Sai dai ya gargaɗi al'umma kan yaɗa labaran mutuwar sojoji.

"Bisa ƙa'ida da tsarin aikin soji, muna martaba dakarun da suka mutu, don haka muna kira ga al'umma da kafofin yaɗa labarai su riƙa bari rundunar soji na sanar da iyalan waɗanda suka mutu a hukumance, kafin fitar da kowane ƙarin bayan,'' in ji shi.

"Haka kuma muna kira ga al'umma su yi wasi da rahotonni marasa tushe da ba a tabbatar ba da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta, saboda hakan na karya gwiwar sojoji a yaƙin da suke yi da matsalar tsaron ƙasa,'' in ji sanarfwar.

Manjo Janar Onoja ya ce harin alama ce na yadda ƴanta'adda suke jin haushin kashe-kashen da ake yi wa mambobinsu da sojoji ke yi a baya-bayan nan, da kuma ƙaruwar hare-haren da sojojin ke yi musu.

Kawo yanzu dai babu wata ƙungiyar da ta ɗauki alhakin kai harin.

A watan Nuwamban shekarar da ta gabata, ƙungiyar ISWAP ta kashe Birgediya Janar Musa Uba bayan kama shi a wani kwanton ɓauna.

Kafin kisan Birgediya Janar Braimah, jami'in soji mafi girman muƙami da ake kashe shi ne Birgediya Janar Uba a 2025.

Ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi da suka haɗa da Boko Haram da ISWAP na kai wa sansanonin soji a arewa maso gabas hare-hare.

Jihar Borno da ke yankin ta kasance cibiyar ayyukan waɗannan ƙungiyoyi na fiye da shekara 10.

A watan da ya gabata, wasu jerin hare-hare bama-bamai a birnin Maiduguri sun kashe fiye da mutum 20 da raunata wasu da dama, lamarin da ya haifar da ƙarin fargabar tsaro a yankin.

Amurka, wadda ta fara haɗin gwiwa tsaro da Najeriya, ta umarci ƴanƙasarta a Najeriya su riƙa kula da wuraren da za su je, saboda matsalolin tsaro da suka haɗa da ayyukan ƴanta'adda da tashin hankali da garkuwa da mutane.

Jihar Borno na daga cikin wuraren da Amurka ta buƙaci ƴanƙasarta da su kauce wa zuwa.

Tinubu ya jajanta wa iyalan sojojin da suka mutu

Asalin hoton, X/Bola Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jajanta wa al'ummar ƙasar kan kisan da aka yi wa sojoji a harin na garin Banisheikh.

"Ina miƙa saƙon ta'aziyyata ga iyalan jajirtattun sojojinmu ƙarƙashin jagorancin Birgediya Janar Oseni Omoh Braimah, waɗanda suka rasa rayukansu wajen kare ƙasarmu a jihar Borno," kamar yadda shugaban ya bayyana a wani bayani da ya fitar a ranar Alhamis.

Sai dai Shugaba Tinubu da rundunar sojin ba su fito ƙarara suka tabbatar da kisan Birgediya Oseni Braimah ba, kodayake ba su musanta rahotonnin mutuwar tasa ba.

Amma wasu mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa Birgediya Janar Oseni Braimah na cikin waɗanda aka kashe.

Kafar yaɗa labarai ta AFP ta bayar da rahoton kashe babban sojan, inda ta kafa hujja da bayanai daga majiyoyin tattara bayanan sirri.

Ƙaruwar ayyukan masu iƙirarin jihadi a Najeriya

Masu bincike sun tabbatar da ƙaruwar matsalar tun shekarar da ta gabata.

Birnin Maiduguri ya fuskanci hare-haren ƴan ƙunar baƙin-wake a watan Disamban bara -- wanda ya kashe mutane da dama, da hare-hare a birane da ƙauyukan jihar.

A ranar Laraba, Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta buƙaci ma'aikatanta da ba na dole ba su bar Abuja saboda ''ƙaruwar taɓarɓarewar tsaro a ƙasar''.

Yayin da ƙungiyoyin ta'addanci suka mayar da hankali ga yankin arewa maso gabashin Najeriya, masu iƙirarin jihadi daga ƙasashen yankin Sahel na samun ƙarin wurin zama a yammacin ƙasar, inda ake samun ayyukan ƴan fashin daji waɗanda ke mamayar ƙauyuka da tasar manoma da makiyaya da masu haƙar ma'adinai.

A makon nan kaɗai an samu rahotonnin mutuwar aƙalla mutum 90 sanadiyyar hare-hare, ciki har da wanda aka kai jihar Kebbi, da ƴansanda suka ɗora alhakinsa kan ƙungiyar Mahmuda, mai alaƙa da Al-Qaeda.

Sauran hare-haren sun haɗa da wanda aka ɗora alhakinsa kan ƴan fashin daji, da ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya ta ce sun riƙa kai farmaki kan ''ƙauyuka ɗaya bayan ɗaya'' har na tsawon kwana uku ba tare da samun ɗaukin sojoji ba.

Fada Illah Vincent Iko, jagoran ƙungiyar CAN na ƙaramar hukumar Shanga a jihar Kebbi ya ce aƙalla mutum 1,900 aka raba da muhallansu sakamakon hare-haren.

Jihar Kebbi - wadda ke kan iyakar Najeriya da Benin da Jamhuriyar Nijar - ta riƙa fuskantar ƙaruwar hare-haren masu iƙirarin jihadi tun 2025 .

Cibiyar ACLED mai lura da rikice-rikice ta ce an samu ƙaruwar hare-haren ƴanbindiga masu alaƙa Al-Qaeda da IS a jihar ta Kebbi.

A jihar Kwara mai maƙwabtaka, mayaƙan ƙungiyar JNIM mai alaƙa da Al-Qaedan ita ma - ta ɗauki alhakin kai wani hari jihar cikin watan Oktoban bara.

Masu bincike sun ɗauki shekara suna gargaɗin yaɗuwar ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi daga yankin Sahel zuwa yammacin Afirka.

A watan Disamban bara, Amurka, tare da taimakon Najeriya ta kai harin bom kan mayaƙan ISSP masu alaƙa da IS a jihar Sokoto.

Mayaƙan ISSP sun fi gudanar da mafi yawan ayyukansu a ƙasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso.

A farkon wannan shekara, Amurka ta tura sojojinta 200 zuwa Najeriya somin samar da horo da dabarun yaƙi ga sojojin ƙasar da ke yaƙi da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi.

Ƙarin rahoto daga Makuochi Okafor