Zakara mai jan kai da cikakken wata a hotunan Afirka na mako

Ga wasu hotuna na wasu abubuwan da suka faru a nahiyar Afirka ko na ƴan nahiyar a wasu ƙsashen duniya a wannan makon.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu rawa ƴan kabilar Xhosa na takawa a bikin bude taron gasar wasan zamiya akan ruwa a kasar Afirka ta Kudu ranar Litinin.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gasar Corona Open J-Bay ana gudanar da ita a kowace shekara a lardin Eastern Cape.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Washegari, wata mata da aka dauki hotonta akan titin birnin Ouagadougou, babban birnin Burkina Faso - kasar da kusan duka manyan maza da mata suka mallaki babura.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani jami'in soja a Ivory Coast yana zantawa a gaban 'yan jarida ranar Laraba - dangane da takaddamar tsare wasu sojojin Ivory Coast a makwabiyarta Mali.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Gabanin bikin babbar Sallah ta Musulmai, ana duba hakoran wata akuya a kasuwar dabbobi da ke Mogadishu babban birnin Somaliya ranar Juma'a.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A wannan rana a babban birnin Ethiopia, Addis Ababa, kasuwa ta cika makil saboda shirye-shiryen sallah...

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Babbar Sallah na nufin bikin layya inda ake yanka dabbobi. Ga wani zakara a wata kasuwa a babban birnin Najeriya, Abuja ranar Juma'a.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A Najeriya, an yi Sallah ranar Asabar - aka kuma sheƙa ruwa kamar da bakin ƙwarya a birnin Ikko a daidai lokacin Sallar Idi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ƙasar Mali ma an yi bikin Sallah ranar Asabar - wadannan yara sun ci gaye a lokacin Sallar Idi a wani kauye mai suna Djiakaking a yankin Segou da ke tsakiyar kasar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An shiga ranar Litinin ana bukukuwan Sallah a birnin Kano da ke arewacin Najeriya, inda aka ga yara a wuraren nishadi suna jin dadi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu masu wasanni da ake kira Afuma daga Togo, ya tsaya akan sanduna a kasar Poland ranar Asabar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mazan da ke tsaye a kan sanduna sun hallarci bikin Ulica wanda ake share kwanaki uku akan titunan birnin Krakow da ke kasar Poland.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A wannan rana, wani dan dambe daga kasar Uganda mai suna David Onama a harabar dambe ta UFC da ke birnin Las Vegas, inda ya samu nasara akan Garrett Armfield.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yara a arewacin Kenya na shiga kwale-kwale zuwa makaranta ranar Laraba a lokacin da ruwa yawan ruwa a tabkin Turkana ya hana su zuwa a kasa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sai dai kuma wannan yanki na fama da fari, kuma ranar Talata, jama'a sun taru a karkashin bishiya domin ziyartar wani asibitin jin kai saboda takalar matsalolin lafiya da ke da nasaba da rashin saukar ruwan sama.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani mutum kenan yana duba awo a wajen wani dillalin sharar karafuna a babban birnin Zimbabwe, Harare, inda yawaitar rashin aiki yi ya saka mutane da yawa neman wasu hanyoyi na daban na samun kudaden shiga.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An ga rana na faduwa ranar Lahadi a kusa da kogin Nile a birnin Khartoum, babban birnin kasar Sudan.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Donald Ramphadi yana wasa a gasar Wimbledon a wasan kusa da karshe na rukunin maza da ke amfani da keken guragu ranar Juma'a - sai dai wata matsala daga kekensa ta sa ya fita daga gasar.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sannan Ons Jabeur 'yan Tunisia ta gaza zama tauraruwar mata a wasan karshe na gasar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Duk da haka mutanen kasar ta sun mata maraba a matsayin jaruma bayan komawarta Tunusiya ranar Laraba.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A yammacin wannan rana kuma an ga cikakken wata a sararin samaniyar babban birnin Tunis.