Kwankwaso ya koma jam'iyyar ADC bayan fita daga NNPP

Asalin hoton, Rabiu Kwankwaso/FB

Lokacin karatu: Minti 3

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya koma jam'iyyar haɗaka ta ADC tare da magoya bayansa bayan ficewarsa daga jam'iyyar NNPP.

An gudanar da bikin komawarsa ne a gidansa da ke Kano, inda shugabannin jam'iyyar da ɗimbin magoya bayansa suka hallara domin tarbar sa.

Tsohon gwamnan ya kuma buƙaci magoya bayansa su yi rajistar jamʼiyyar, tare da samun katin zaɓe na ƙasa.

A ranar Lahadi ne Kwankwaso ya sanar da ficewarsa daga NNPP, yana mai cewa matakin na daga cikin kokarin haɗa kai da wasu jam'iyyu domin kawo sauyi a ƙasar.

Ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a samar da hadin gwiwa tsakanin manyan 'yan adawa, domin tinkarar kalubalen da Ƙasar ke fuskanta da kuma inganta shugabanci.

Sai dai har yanzu ɓangaren NNPP ba su fitar da wata sanarwa mai karfi kan ficewar tasa ba.

Wane tasiri Kwankwaso zai yi a ADC?

Asalin hoton, Atiku Abubakar/FB

Yayin da jam'iyyar ƙawancen ƴan hamayya ta ADC ke ci gaba da samun karɓuwa daga wasu ƴansiyasar ƙasar ana ganin zuwan Kwankwaso zai yi matuƙar tasiri ga jam'iyyar.

Dr Kabiru Sufi ya ce tasirin da zai yi shi ne zai iya kawo ɗimbin ƙuri'un da ake ganin akwai a jihar Kano.

Jihar Kano ce kan gaba a yawan samar da ƙuri'u a zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya.

''Kuma mafi yawan ƙuri'un da ake samu daga a zaɓukan shugaban ƙasa da suka gabata, Kwankwaso da na matuƙar tasiri wajen samar da su'', kmar yadda ya bayyana.

A zaɓen 2023 da ya gabata Kwankwaso - wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a NNPP ya samu fiye da ƙuri' miliyan guda daga jihar, wadda tafi kowa yawan al'umma.

Don haka ne Dr Kabiru Sufi ya ce tasirin da zuwansa ADC zai yi wa jam'iyyar shi ne samun ƙuri'un Kano, ''kada ta yi sakaci da jam'iyya mai mulki ta kwashe su''.

Masanin siyasar ya ci gaba da cewa da wannan ake ganin Kwankwaso da Nasir El Rufa'i za su iya bayar da gudummawa daga Arewa maso Yamma.

Me ya sa bai shiga APC ba?

Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An dai jima ana alaƙanta Kwankwaso da komawa jam'iyyar APC mai mulki tun kafin rantsar da gwamnatin Tinubu.

A wata ganawa da Kwankwaso ya yi a Tinubun a Faransa gabanin rantsar da shi a 2023 da alƙawarin da ya yi na aiki da ƴan adawa, ya sa aka riƙa tunanin zai shiga ƙunshin gwamnatin idan an rantsar da ita.

Haka aka riƙa wannan hasashe a tsawon shekara uku da gwamnatin Tinubu ta kwashe amma har yanzu Kwankwason bai shiga APC ba.

Ficewarsa daga NNPP ya sabunta wannan zargi, to amma Dr Sufi ya ce ko kaɗan Kwankwanso ba zai shiga APC ba.

Ko a sanarwarsa ta ficewa daga NNPP kwankwaso ya ce zai koma wata jam'iyya ce da za ta ba shi damar kawo sauyi a siyasar Najeriya.

''Dama ban yi tunanin zai shiga APC a wannan gaɓa ba, saboda abubuwan da suka faru a baya-bayan nan'', in ji shi.

Masanin siyasar ya ci gaba da cewa ana ganin rashin daidaitawa da gwamnan Kano na daga cikin dalilan da za su hana Kwankwaso shiga jam'iyya mai mulki.

''Inda a ce sun tafi tare zai fi armashi amma kuma sai bayan gwamna ya tafi shi kuma Kwankwaso ya shiga APCn daga baya shigar ba za ta yi kwarjinin siyasa ba'', in ji shi.

Kwankwanso a siyasar Najeriya

Asalin hoton, Rabiu Kwankwaso/FB

Bayanan hoto, Kwankwaso na da tarin magoya baya

Tsohon gwamnan jihar Kanon, Rabi'u Musa Kwankwaso na ɗaya daga cikin ƴan siyasa a arewacin Najeriya da suka daɗe suna tasiri, musamman saboda yadda ya shiga zuciyar matasa.

Ana dai ganin tun bayan Malam Aminu Kano ba a sake samun wani ɗan siyasa ba da ya fito da wani tsari na siyasa a arewa da ya saka wa suna, kuma yake da mabiya na ga-ni-kashe-ni, sai Kwankwason.

Kwankwaso ne jagoran aƙidar siyasa mai suna ɗarikar Kwankwasiyya da mabiyanta ke saka jar hula.

Bayan kammala wa'adinsa ne ya tsayar da mataimakinsa, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ba a daɗe ba, suka samu saɓani aka raba-gari.

Wannan ya sa a lokacin da Ganduje yake neman wa'adi na biyu, Kwankwaso ya tsayar da Abba Kabir Yusuf a zaɓen 2019, amma Ganduje ya kayar da shi bayan an yi zaɓen cike gurbi a garin Gama.

Har ila yau, Kwankwaso ya tsayar da gwamnan Kano mai-ci, Abba Kabir Yusuf inda ya kayar da ɗantakarar gwamna mai barin gado, Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC mau mulkin jihar a lokacin.