Al'adun ƙabilar Maasai da ke Kenya da mai hura wuta cikin hotunan Afirka

Asalin hoton, GERALD ANDERSON/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Wasu maza ƴan ƙabilar Maasai na yiwa jikinsu kwalliya a sansanin Sekenani ranar Laraba a Kenya
Lokacin karatu: Minti 3

Asalin hoton, GERALD ANDERSON/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A ranar ne kuma, wani mutum yake ƙoƙarin kunna wuta da busasshiyar ciyawa a wani yanki.

Asalin hoton, MIKE COPPOLA/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Tems mawaƙiya ƴar Najeriya yayin da ta halarci bikin Met Gala na shekara ta 2025 a New York ranar Litinin.

Asalin hoton, AHMAD HASABALLAH/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Ranar Lahadi yayin da wani mutum ke wucewa ta gefen dandalin baje-kolin kayan da aka yi da hannu a Aswan da ke ƙasar Masar.

Asalin hoton, AHMAD HASABALLAH/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A birnin kuma a ranar, an ɗauki hoton wani mutum a cikin runfar kwandunan da aka saka da hannu.

Asalin hoton, NURETTIN BOYDAK/GETTY IMAGE

Bayanan hoto, A Giza wani mutum yana murmushi a kusa da raƙuminsa.

Asalin hoton, MARIO TAMA/GETTY IMAGE

Bayanan hoto, Ranar Talata a Rome babban birnin ƙasar Italiya - wata ƴar Najeriya mai hidimar majami'a na waya yayin da wasu takwarorinta ke wucewa a gefe.

Asalin hoton, THOMAS MUKOYA/REUTERS

Bayanan hoto, Bayan kwanaki biyu, an kammala zaɓen sabon Fafaroma. Ma'aikata a Nairobi na ware jaridun da suke ɗauke da hoton sabon Fafaroma Pope Leo XIV. Shugaban ɗarikar Katolika ɗan Amurka na farko.

Asalin hoton, JEROME FAVRE/EPA

Bayanan hoto, Wani farin hayaƙi na tashi lokacin da aka ɗauki hoton Lamine Cissoko yana kiɗa da kora yayin bikin Africa Festival a makarantar koyar da harshen Faransanci ranar Laraba a Dakar da ke ƙasar Senegal.

Asalin hoton, JEROME FAVRE/EPA

Bayanan hoto, A ranar, shi ma Zobel Raul ɗan ƙasar Kamaru ya nuna tasa bajintar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan matar ta buɗe fukafukai ranar Litinin yayin da ta ke zanga-zangar haƙar mai da iskar gas a birnin Cape Town da ke Afrika ta Kudu.

Asalin hoton, ALEX GRIMM/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Ɗan ƙasar Senegal Ninou Diatta lokacin da ya ke farin ciki ƙungiyarsa ta yi nasara lokacin da ta fafata da Chile a gasar kofin duniya ta Fifa Beach Soccer a Seychelles ranar Talata.

Asalin hoton, GERALD ANDERSON/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Raƙumin daji yana kallon tsuntsu yana wucewa a Maasai Mara da ke ƙasar Kenya

Asalin hoton, LUIS TATO/AFP

Bayanan hoto, Lokacin da wani mai wa'azi ya shiga shauƙi y na tsakiyar magana da masu kamun kifi a Bujumbura da ke Burundi ranar Juma'a.