Hotunan yadda aka yi sallar Idi a faɗin duniya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana bai wa yara mata da maza kyautuka bayan kammala sallar Idi a garin Lviv na Ukraine, yayin da Rasha ke ci gaba da luguden wuta a kan ƙasar
Lokacin karatu: Minti 3

Musulmai a faɗin duniya na bukukuwan Idin Ƙaramar Sallah ko kuma Eid al-Fitr a Larabce, wato ɗaya daga cikin biki mafiya girma a kalandar Musulunci.

Eid al-Fitr - wanda ke nufin "bikin kammala azumi" - akan yi shi ne bayan kammala azumin watan Ramadana duk shekara, wanda shi kuma rukuni ne cikin rukunnan Musulunci.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dubun dubatar Musulami sanye da hirami suke yin sujjada a Masallacin Ka'aba

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A birnin Moscow na Rasha, ana iya ganin Musulmai na shirin yin sallar Idi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ɗaruruwa ne suka fito yin sallar Idin a filin Idi na Tononoka da ke birnin Mombasa na ƙasar Kenya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An kuma gudanar da sallolin a cikin wani filin wasa da ke Port Sudan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙananan yara sun bi sawun manya a Masallacin Essalam da ke Rotterdam na ƙasar Netherlands

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Falasɗinawa a unguwar Jabaliya da ke Zirin Gaza sun gudanar da sallolin nasu ne cikin ɓaraguzan wani masallaci sakamakon hare-haren Isra'ila a yaƙin da take yi da Hamas

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Iyalai sun taru a Masallacin Ƙudus, wuri na uku mafi tsarki a Musulunci - bayan Makka da Madina

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wan yaro yana hamma yayin sallar Idi a wani filin wasa da ke ƙasar Ƙatar

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Musulmai na yi wa juna barka da sallah a dandalin Martim Moniz da ke birnin Lisbon na Portugal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mata ma sun fito sallar a Burgess Park da ke birnin Landan

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A dandalin Plebiscito ma da ke birnin Naples na Italiya, masallata sun fito

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu mata na ɗaukar hoto bayan kammala sallar Idi a babban masallacin Hagia Sophia na birnin Istanbul ɗin Turkiyya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan gudun hijirar Afghanistan suna yin sallah a wani masallaci da ke wajen birnin Peshawar na Pakistan