Yadda yaƙi na tsawon lokaci a Gabas ta Tsakiya zai sauya salon tafiye-tafiyen jiragen sama

Hayaki na tashi a Tehran.
Yadda yaƙi na tsawon lokaci a Gabas ta Tsakiya zai sauya salon tafiye-tafiyen jiragen sama
    • Marubuci, Theo Leggett
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Transport correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 5

A baya, ba a jin ɗuriyar ɓangaren sufurin jiragen sama yadda ya kamata a Dubai, kuma filin jirgin saman ba shi da tagomashi. Hanyoyin da jirage ke bi wajen tashi cike suke da kasa da ƙura. Amma zuwa shekarar 1960, abubuwa sun fara kyautatuwa, inda jirage ke tsayawa a wajen don shan mai a hanyarsu ta zuwa wuraren da suka fi cigaba a duniya.

Amma zuwa yau, Dubai na ɗaya daga cikin wurare da ɓangaren sufurin jiragen sama ke ji da shi. A 2024, sama da matafiya miliyan 92 suka yi amfani da filin jirgin sama na Dubai, mai cike da ƙayan alatu, gine-ginen zamani da kuma kantuna.

Wannan ya sa filin jirgin saman zama mafi cunkoso a duniya ga fasinjojin ƙasa da ƙasa - inda ya zarta filin jirgin sama na Heathrow da ke birnin Landan, wanda ya samu fasinjoji miliyan 83.

Ba ya ga Dubai, akwai kuma filayen jiragen sama a Abu Dhabi da kuma Qatar waɗanda su ma ke samun yawan fasinjoji a yankin Gulf - inda sama da fasinjoji miliyan 87 suka yi mu'amala da filayen.

Waɗannan filayen jiragen sama uku da ke yankin Gulf, na samun tashin jiragen sama kusan 3,000 a rana idan ba a samu wani cikas ba, inda kamfanonin jirage na Emirates da Etihad da kuma Qatar Airways suka mamaye sufurin.

Sai dai yaƙin da ake yi a Gabas ta Tsakiya ya shafi ɓangaren sufurin jiragen saman matuka. Da farko, an hana jiragen sama da dama tashi da kuma ɗaiɗaita ɗaruruwan fasinjoji.

Lamarin ya shafi sufurin jiragen sama ba kaɗan ba.

Zane da ke nuna jiragen da ke tashi.

Akwai kuma batun mai. Yayin da aka katse samar da mai a yankin bayan da Iran ta rufe mashigar Hormuz, lamarin ya janyo damuwa sosai. Yankin ya kasance yana samar da kusan rabin man da jiragen sama ke amfani da shi a Turai, kuma fargabar ƙarancinsa ya janyo farashin tikitin jiragen sama ninƙawa tun fara yaƙin. Wasu kamfanin jiragen sama sun ma fara dakatar da zirga-zirga.

Yayin da waɗannan abubuwa za su mamaye ɓangaren a yanzu - kuma zai iya janyo ƙaruwar tikitin jiragen sama a cikin watanni masu zuwa - akwai kuma tambayar yadda makomar ɓangaren zai kasance a tsawon lokaci.

Ruɗani a cikin filayen jiragen sama

Yaƙin da ya ɓarke tsakanin Isra'ila-Amurka da Iran ya janyo rufe sararin samaniya a faɗin Gabas ta Tsakiya. Lamarin ya janyo jiragen da suka soma tashi juya wa su koma.

Dubun-dubatar fasinjoji sun maƙale a cikin filayen jiragen sama na Dubai, Abu Dhabi da kuma Qatar, yawancin mutane sun yada zango ne kawai a wurin don sake samun wani jirgi su nufi wani wuri.

Iran dai ta riƙa kai hare-haren ramuwa a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma Qatar, abin da ya janyo fargaba ga waɗanda suka maƙale a filin jirgin sama da kuma otel-otel.

Yawancin fasinjoji da dama daga faɗin duniya sun kasa yin tafiye-tafiyen da suka shirya yi, saboda jiragensu za su bi ɗaya daga cikin filayen na yankin Gulf. Sun shiga ruɗani inda suka yi ta neman mafita.

Zane da ke nuna yadda jirage ke juyawa bayan katse zirga-zirga.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kamfanonin jirage na Emirates da Etihad sun fara gudanar da aikace-aikace na wucin gadi donmayar da fasinoji gida, daga baya Qatar Airways ta bi sahu. Wasu jirage daga wajen yankin su ma sun fara zirga-zirga. Wasu gwamnatoci, ciki har da Birtaniya sun samar da jirage don taimakawa mutane barin yankin.

Tun lokacin, al'amura sun ɗan fara lafawa, inda duka kamfanonin jiragen uku suka koma zirga-zirga sannu a hankali a yankin.

A cewar ƙwararru, sama da jirage 30,000 aka soke a yankin Gabas ta Tsakiya baki ɗaya tun fara yaƙin tsakanin Isra'ila da Iran.

Matafiya da dama sun bayyana labaransu a shafukan sada zumunta da kuma gidan yaɗa labaru na irin abubuwan da suka fuskanta.

Ɗaya daga cikinsu shi ne, Ian Scott, wanda ke tafiya daga Melbourne zuwa birnin Venice inda zai bi ta Doha. An tilasta jirginsu komawa suna cikin tafiya, inda ya shafe tsawon kwanaki yana zama a otel, kafin ya zaɓi shiga mota na kwanaki biyu ta sahara zuwa Oman. Daga can ya samu jirgi.

Yanzu ya ce a nan gaba, zai kauce wa zirga-zirga ta yankin Gulf, ko da an dakatar da yaƙi - saboda ya yi imanin cewa matsalolin yankin ba za su kawo karshe nan kusa ba.

Nasarar ɓangaren sufurin jiragen sama na yankin Gulf

Irin martanin matafiya kamar Ian ne zai saka masu kula da sufurin jiragen sama a yankin shiga damuwa.

Duk da cewa Dubai ta zama ɗaya daga cikin wuraren da aka fi zuwa yawon buɗe ido da kuma kasuwanci a duniya, amma kusan rabin matafiya da ke zuwa ba su je don su zauna ba. Za su iya sauya jiragen da za su shiga.

A bara kashi 47 na matafiya da suka je Dubai, sun bi wurin ne don yada zango da kuma samun wani jirgi don karasa inda suke son zuwa, sai kuma Abu Dhabi mai kashi 54 da kuma Doha mai kashi 74.

Wannan shi ne muhimmancin filayen jiragen sama na yankin na Gulf. Fasinjoji na bi ta wurin don samun jirage su karasa tafiyarsu.

Yankin yana da jirage da fasinjoji ke son mu'amala da su da kuma tsari mai kyau.

Zayed International Airport.

Asalin hoton, NurPhoto via Getty Images

Bayanan hoto, Filin jirgin sama na Zayed wanda aka fi sani da Abu Dhabi, yana ɗaya daga cikin filaye masu cunkoson fasinjoji a yankin

Wani ƙwararre kan harkar tafiye-tafiyen jiragen sama, Andrew Charlton ya ce "Yankin Gulf wuri ne da yake da fasahohi na zamani, inda mutum zai iya bi ta wurin don zuwa ko'ina a duniya," in ji shi.

Ya ce hakan ne ya saka ɓangaren sufurin yankin samun cigaba saboda yadda mutane ke amfani da wurin, har ma ya fara gogayya da kasuwannin China da Indiya.

Kamfanonin jiragen yankin sun zuba jarin da suke so a harkar don ya tafi daidai da zamani da kuma irin tsarin da suke so.

Jirgi na tashi.

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

Bayanan hoto, Rikicin Gabas ta Tsakiya ya jefa ɓangaren sufurin jiragen sama na yankin cikin wani hali

Abin da ya sa farashin tikiti zai ƙaru

Tambayar ita ce wani irin lahani wannan rikici ya yi wa ɓangaren sufurin jiragen sama na yankin Gulf - sannan ko tsarin harkar a yankin ya samu lahani na har abada.

A cewar Charltonc, abubuwa za su kyautatu ne idan aka cimma matsayar dakatar da faɗan. Idan aka samu nasara, in ji shi, kamfanonin jiragen za su samu farfaɗowa cikin sauri saboda "za su koma kasuwa da farashin tikiti mai sauki".

Sai dai idan aka ci gaba da yaƙi, "muddin fasinjoji suka fara duba wasu hanyoyi na zirga-zirga, da kuma jiragen da za su iya yin irin aikin waɗannan na yankin Gulf, to lamarin zai sauya," in ji shi.

Fasinjoji a cikin filin jirgin sama na Dubai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙwararru sun yi gargaɗin cewa kamfanonin jiragen sama na Turai ba su da ƙarfin maye gurbin na yankin Gulf