Wane ne sabon shugaban kamfanin Apple, mai ƙera wayar iPhone?
Asalin hoton, Justin Sullivan /Getty Images
Tim Cook zai ajiye aiki a matsayin shugaban kamfanin Apple bayan shekara 15, inda zai miƙa ragamar jagorancin kamfanin ga shugaban sashen injinayanci da kayan aiki na kamfanin John Ternus, a wani abu da ke alamta buɗe sabon babi ga kamfanin.
Cook ya shugabanci kamfanin tun shekarar 2011, bayan da wanda ya kafa kamfanin Steve Jobs ya yi murabus saboda lafiyarsa, jim kaɗan kafin mutuwarsa.
Ternus zai soma aiki ne a ranar 1 ga watan Satumba.
Ya shafe tsawon shekaru 25 yana aiki a kamfanin na Apple.
Cook zai ci gaba da aiki har watan Agusta, inda za su yi aiki tare ta Ternus domin miƙa masa mulki.
Bayan yin murabus, zai ci gaba da tallafa wa kamfanin ta hanyar taimakawa a wasu ɓangarori na gudanar da kasuwanci, ciki har da yin hulɗa da masu ruwa da tsaki a faɗin duniya.
Matakin ya biyo bayan shafe watanni ana hasashen cewa kamfanin na Apple, wanda a baya-bayan nan ya cika shekara 50 da kafuwa, na shirin yin sauyi a shugabancinsa.
A wani rubutu da ya wallafa a shafin intanet na Apple a ranar Litini, 20 ga watan Afrilu, Cook ya ce jagorantar kamfani ita ce dama mafi girma da ya taɓa samu a rayuwarsa.
A lokacin shugabancinsa, ƙima da darajar kamfanin ya ƙaru matuƙa, tare kuma da faɗaɗa na'urorinsa da ayyukansa.
Wane ne Tim Cook kuma ta yaya ya sauya kamfanin Apple?
Asalin hoton, Justin Sullivan/Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ƙarƙashin shugabancin Cook, ribar kamfanin Apple na shekara-shekara ya nunka sau huɗu, kuma kamfanin ya kara samun tagomashi a kasuwannin duniya.
Sai dai duk da irin maƙudan kuɗaɗen da kamfanin ya samu, masu suka sun ce Apple ya samu koma-baya a fannin ƙirƙire-ƙirƙire, irin wanda aka samu a zamanin Jobs.
Dipanjan Chatterjee, babban mai sharhi a kamfanin Forrester da ke bincike kan kasuwannin duniya, ya yaba wa Cook wajen samar da kuɗaɗe da daidaito a kamfanin Apple, sai dai ya ce ya gaza wajen samar ƙirƙiro sabbin na'urori, kamar wayar IPhone.
Kamfanin ya dogara ne kan wayar da yake samarwa, a yayin da yake kokarin lalubo wani babban abu da zai kawo masa ci gaba, in ji Chatterjee.
Naɗin Ternus na nuna cew Apple na buƙatar samun na'urori iri-iri.
Ba kamar Jobs da Ternus ba, shi Cook bai soma aiki a Apple da ilimin samar da na'urori ko injiniyanci.
Ya soma gina kansa ne a mastayin ɗan kasuwa, inda ya riƙe muƙamai a wannan fannin a kamfanonin IBM da Compaq.
Ya fi ƙwarewa a wajen gudanar da ayyuka, da cinikayya, a maimakon samar da sabbin fasahohi, wani abu da ake ganin shi Jobs ya ƙware a fannin.
Kuma ana ganin fannin da ya fi ƙarfi ne za a fi tunawa da shi, inda wasu ke kallon shi a matsayin ɗaya daga cikin shugabannin da suka fi samun nasara a zamaninsa.
Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
- 2007: Steve Jobs ya ƙaddamar da wayar iPhone, wanda ake latsawa, mai ɗauke da manhajoji, da wurin shiga intanet, da kuma na'urar sauraron sauti iPod. A shekarun da suka biyo kuma, Apple ya ƙaddamar da wayoyin iPhone ƙanana, inda aka yi ta inganta fasahar.
- 2010: Manhajar Find My iPhone, wadda a baya sai an biya kuɗi kafin amfani da ita, kuma ta kasance ɗaya daga cikin manhajojin Apple da suka yi fice, na taimakawa wajen gano wayoyin iPhone idan suka ɓace.
- 2015: Agogon Apple ya haɗa fasahar duba lafiya da kuma yanayin motsa jiki.
- 2015: Rediyon iTunes na wayoyin iphone ya bunƙasa zuwa wata farfajiyar sauraron waƙoƙi na intanet wato Apple Music.
- 2018: Kamfanin Apple ya kasance kamfani na farko da aka sayar da hannun jarinsa ga jama'a da ya kai darajar dala triliyan ɗaya. A yanzu darajar sa ta kai dala triliyan 4.
- 2019: Manhajar Find my, ya koma Find My Friends, wanda ke bayar da damar nemo sauran nau'rorin kamfanin Apple da suka ɓace.
- 2019: Apple TV ya sake sauya fasali zuwa Apple TV+, wanda ya mayar da hankali kan kallo kai tsaye ta intanet.
- 2024: A wannan shekarar Gilashin kallo na Apple Vision Pro ya ja hankalin jama'a sosai, sai dai kuma ya gaza wajen samun karɓuwa sosai.
Shin John Ternus ne mutumin da Kamfanin Apple ke buƙata?
Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
Ternus ya yi aiki kan dukkanin manyan na'urorin kamfanin Apple da aka fitar tsawon fiye da shekaru 25, inda ya taimaka wajen fitar da dukkanin samfurin iPad da aka yi, da wasu samfurin wayar iPhone, kuma ya taimaka wajen ƙaddamar da na'urar sauraro wato AirPods da kuma agogo na Apple Watch.
A wata sanarwar haɗin gwiwa da aka fitar ranar Litinin, Ternus ya bayyana Cook a matsayin abin koyi gare shi, yayin da shi kuma Cook ya bayyana shi a matsayin mai hangen nesa, wanda ke da tunani irin na injiniyanci da zuciyar ƙirƙira da hankali irin na shugabanci.''
Gil Luria, shugaban kamfanin DA Davidson & Co, ya ce naɗa shugaba mai ƙwarewa a fannin samar da kayyyakin aiki na nuna burin Apple na mayar da hankali kan sabbin na'urorinsu - cikin har da wayoyin da ake iya lanƙwasawa da kuma na'urorin da ake iya sanyawa kamar tabarau mai ɗaukar hoto da sauti.
Apple ya kuma fuskanci suka kan jan-ƙafa wajen soma amfani da ƙirƙirarriyar basira, inda a maimakon samar da nashi, ya riƙa amfani da fasahar abokan hamayya kamar Google da Open AI.
Wane ne ya mallaki Apple?
Apple kamfani ne da aka sayar da hannun jarinsa ga jama'a, inda manyan masu zuba hannun jari kamar su Vanguard da BlackRock ke da mafi yawa na hannayen jarinsa.
Farashin hannun jarin ya kama daga dala 270.29 zuwa dala 274.27.
Arthur Levinson, wanda shi ne mutum ɗaya da yafi kowanne zuba hannun jari, kuma ya shafe tsawon lokaci a matsayin shugaban kwamitin zartaswa, a yanzu zai zama babban darakta mai zaman kansa, yayin da Cook kuma zai zama shugaban zartaswa.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai