Yadda Man City ta lashe kofin Carabao bayan doke Arsenal

Nico O'Reilly ne ya ci wa Man City ƙwallayenta biyu a ragar Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nico O'Reilly ne ya ci wa Man City ƙwallayenta biyu a ragar Arsenal
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester City ta kawo ƙarshen fatan da Arsenal take da shi na ƙoƙarin lashe kofi huɗu a bana bayan hana mata kofin Carabao a fafatawar ƙarshe da suka yi a Cup Wembley.

Nico O'Reilly ne ya ci wa Man City ƙwallayenta biyu a ragar Arsenal inda aka tashi wasan 0-2.

Nasarar ta ba Pep Guardiola dama zama koci na farko da ya lashe kofin Carabao sau biyar.

Arteta da Arsenal kuma za su ci gaba da jiran neman lashe kofin farko tun na FA a 2020.

Arsenal yanzu na harin lashe kofin Premier inda ta ba City tazarar maki tara a teburin gasar.

City yanzu ta rama fushin ficewa daga Gasar Zakarun Turai da Real Madrid ta doke ta.

Yanzu kofi na 16 kenan da Guardiola ya lashe a Manchester City, yayin da ake rade-radi kan makomarsa a ƙungiyar.