Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal na son Alvarez, Man U na bibiyar Tonali
Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich ta Jamus ta ce ba ta da niyyar sakin ɗan wasan gaba na Faransa, Michael Olise mai shekara 24, duk da rahotannin da ke cewa Liverpool na son sayensa kan kuɗin da ya haura fam miliyan 170. (Talksport)
A wani bangare kuma, Manchester United na shirin tuntuɓar Newcastle domin neman ɗan wasan tsakiya na Italiya, Sandro Tonali mai shekara 25, a ƙarshen kakar wasa. (Mail)
Haka kuma, Manchester United ta saka sunan ɗan wasan baya na hagu na Arsenal, Myles Lewis-Skelly mai shekara 19, cikin jerin 'yan wasan da take son siya a bazara, sakamakon rashin samun damar buga wasa akai-akai. (Daily Express)
Kungiyoyin Paris St-Germain da AC Milan na bibiyar halin da Marcus Rashford ke ciki, wanda ke zaman aro daga Manchester United, kuma a shirye suke su dauke shi idan Barcelona ta kasa kulla yarjejeniya ta dindindin da shi. (CaughtOffside)
Aston Villa ma na iya yunkurin sayen Rashford idan har ba ta samu nasarar daukar Jadon Sancho mai shekara 26 ba, wanda shi ma ke zaman aro daga Manchester United. (SportsBoom)
Arsenal na nuna sha'awar daukar dan wasan gaba na Atletico Madrid kuma ɗan kasar Argentina, Julian Alvarez mai shekara 26. (Football.London)
Liverpool na duba yiwuwar daukar dan wasan gaba na Senegal, Iliman Ndiaye mai shekara 26, daga Everton. (Teamtalk)
Haka kuma, Ndiaye da dan wasan tsakiya na Everton, James Garner mai shekara 25, na cikin jerin 'yan wasan da Manchester United ke son dauka a wata yarjejeniya da ka iya kai fam miliyan 100. (Fichajes)
Newcastle na ganin yiwuwar daukar Ben White mai shekara 28 daga Arsenal domin maye gurbin Kieran Trippier mai shekara 35. (Sports Boom)
Paris St-Germain ba ta sa ran Arsenal za ta nemi ɗan wasanta Khvicha Kvaratskhelia mai shekara 25 a bazara, yayin da Arsenal din ke sha'awar Anthony Gordon na Newcastle. (Sky Sports)
Atletico Madrid na shirin karfafa gabanta ta hanyar sayen Ferran Torres na Barcelona mai shekara 26. (Fichajes)
Dan wasan baya na hagu na Barcelona, Alejandro Balde mai shekara 22, na jan hankalin kungiyoyi da dama ciki har da Manchester United da Manchester City da Aston Villa. (Mundo Deportivo)
A ƙarshe, Sunderland na iya fuskantar ƙalubale wajen rike Lutsharel Geertruida mai shekara 25, wanda ke zaman aro daga RB Leipzig, sakamakon sha'awarsa da kungiyoyi da dama ciki har da Liverpool da Tottenham da Everton da Aston Villa da Crystal Palace ke nunawa. (Teamtalk)