Liverpool za ta Fafata da Man U kan Wharton, Newcastle za ta sayar da Wissa
Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta bi sahun Manchester United a yunkurin dauko dan wasan Ingila Adam Wharton daga Crystal Palace, wadda ke son akalla fam miliyan 80 kan dan wasan mai shekara 22.(Talksport), external
Tottenham ta cimma yarjejeniya a matakin farko don siyan dan wasan bayan Argentina Marcos Senesi a bazara lokacin da ake sa ran dan wasan mai shekaru 28 zai bar Bournemouth a karshen kwantiraginsa. Sai dai duk da haka, yarjejeniyar ta dogara ne a kan ci gaba da kasancewar Spurs a gasar firimiya. (Talksport), external
Newcastle United ta nuna alamun a shirye ta ke ta saurari tayin da ake yi wa dan wasanta Yoane Wissa, mai shekara 29, duk da cewa a bara ta biya Brentford fam miliyan 50 kan dan wasan Jamhuriyar Dimokraddiyar Kwango .(The I), external
Arsenal na zawarcin dan wasan ingila a tawagar matasan kasar, Jeremy Monga wanda ke taka leda a Leicester City. (Telegraph - subscription required), external
Tsohon kocin Liverpool Jurgen Klopp ba ya cikin wadanda ake son a nada a matsayin wanda zai ja ragamar Real Madrid a bazara (El Chiringuito - in Spanish), external
Newcastle ta dauki zawarcin da Bayern Munich ke yi wa dan wasanta Anthony Gordon, mai shekara 25 da muhimanci, sai dai za ta nemi kudi kusan fam miliyan 80 kan dan wasan tawagar Ingila . (The I), external
Dan West Ham , Konstantinos Mavropanos na shirin barin kungiyar a wannan bazara, inda dan wasan tawagar Girka mai shekara 28 na jan hankalin Borussia Dortmund duk da cewa sun nuna damuwa kan kudin da yake son a biya shi . (Florian Plettenberg), external
Dan wasan Austria David Alaba, mai shekara 33 na gab da barin Real Madrid idan kwantaraginsa da kungiyar ya zo karshe a bazara. (Fabrizio Romano), external
Ajax na son dan wasan Real Madrid da Sfaniya Dani Ceballos, mai shekara 29,. (AS - in Spanish), external
Shugaban Bayern Munich Uli Hoeness na son golan Jamus Manuel Neuer, mai shekara 40, ya kara shekara guda a kungiyar tare da horas da Jonas Urbig, mai shekara 22. (Sky Sports Germany)
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai