'An yi kuskuren ba da kyautar Nobel' - 'Yan Eritrea
Asalin hoton, TT
'Yan kasar Eritrea a Scandinavia na gudanar da zanga-znagar adawa da kyautar Nobel kan samar zaman lafiya da ake shirin bayarwa ga firai minista Abiy Ahmad.
A yau ne aka mika wa Abiy Ahmed kyautar, bayan Kwamitin Nobel ya zabi firaminista shi a matsayin wanda ya ci kyautar ta bana, saboda kawo karshen rikici da tsattsamar dangantaka tsakanin kasarsa da makwabciyarta Ethiopia da aka shafe fiye da shekaru ashirin ana yi.
Masu zanga-zangar a Oslo sun ce alfanon sasanci tsakanin Eritrea da Ethiopia basu tabbata ba, don haka firami minista Abiy bai cancanci kyautar ta Nobel ba.
Daruruwan mutane ne ke zanga-zangar da suka gana da wani dan majalisar dokokin kasar Norway a birnin Oslo, na dauke da kwalaye dake cewa: "Kyautar Nobel ta tabbatacciyar zaman lafiya ne, ba siyasa ba."
Wani daga cikin masu zanga-zangar ya sheda wa BBC cewa tun da aka rattaba hannu a kan yanrjejeniyar zaman lafiyar a bara, babu wani sauyin da aka samu a fagen siyasar Eritrea.
Ya kara da cewa har yanzu ba a sanya alamomi ba a iyakokin kasashen da aka rufe.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama na yawan sukan gwamnatin Eritrea wadda ba zaben ta aka yi ba.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai