Ya kamata mu rage kasuwanci da kasashen Turai — Dangote
Asalin hoton, Getty Images
Manyan shugabannin kamfanoni da 'yan kasuwa a Afirka, sun gudanar da babban taro tare da wasu tsofaffin shugabannin kasashen nahiyar a birnin Legas, cibiyar kasuwancin Najeriya.
Taron ya zo da zimmar kafa kungiya mai karfi wacce za ta bunkasa harkokin kasuwanci a Afirka, a maimakon dogaro da kasashen ketare.
'Yan kasuwar sun ce ana shigo da akasarin kayayyaki ne daga kasashen Turai da China, abin da ke kawo tarnaki ga bunkasar kasuwanci a nahiyar Afirka.
Dangote wanda shi ne ya jagoranci taron, ya ce ya dace manyan kamfanoni Afirka su hada kai da gwamnatocinsu ta yadda za a samar da ayyukan yi.
Ya ci gaba da cewa: "Hakan zai kawo karfafa kasuwanci a tsakanin kasashen Afirka, maimakon dogaro da nahiyar Turai".
Har ila yau, ya ce kasuwancin da ake yi a tsakanin kamfanonin Afirka bai wuce kaso 18 cikin 100 ba, don haka akwai bukatar karfafa kasuwanci a tsakanin manyan kamfanonin Afirkan.
To sai dai ya ce idan har ana so a cimma wannan bukata, to dole ne kamfanonin su rinka yin kaya masu inganci.
Karanta wadansu karin labarai masu kayatarwa
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai