'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga 19 a Mexico
Asalin hoton, AFP
'Yan sanda a Mexico sun ce sun kashe 'yan bindiga goma sha tara, a musayar wuta da suka yi da su a jihar Sinaloa dake arewacin kasar.
Jami'an 'yan sanda biyar sun samu raunuka a bata kashin.
A daren Juma'a ne a ka fara bata kashin a garin Villa Union, lamarin kuma ya lafa bayan 'yan sanda sun yi ta tsere da 'yan bindigar a mota a Aguaje.
Jami'ai sun ce wannan, ya na daya daga cikin arangama mafi muni da aka yi a kudancin Sinaloa a 'yan watannin nan.
Yankin ya yi fama da rikice-rikice na wata babbar kungiyar masu hada-hadar miyagun kwayoyi a Sinaloa tun bayan da aka kama shugabanta a bara.
Wani rahoto ya ce 'yan bindigan sun kashe wasu mutane uku ne, sannan kwatsam, 'yan sanda dake kusa suka musu dirar miliya.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai
{{rankTranslation}}