Kalli ƙayatattun hotunan Afirka na mako daga 11 zuwa 17 ga watan Maris 2022

Ga kayatattun hotunan na wannan makon daga sassan Afirka da ma wasu wuraren:

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Yara sun hau wata bishiya a arewa maso gabashin Mozambique ranar Asabar bayan da guguwar Gombe mai tafiya kan kilomita fiye da 200 kan kowace sa'a ta kayar da ita.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, 'Yan wasa daga Burkina Faso na wasanni ranar Laraba a wani biki da aka yi a Abidjan wanda 'yan wasa daga kasashe takwas na duniya suka halarta.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ga wasu damisa biyu da aka ceto daga Argentina kuma daga baya aka kai su jihar Free State ta Afirka ta Kudu ranar Asabar. Bayan sun shafe fiye da shekaru 15 ana tsare da su cikin waniu tarragon jirgin kasa, a yanzu suna iya watayawa a cikin dawa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A daidai wannan ranar wata mata ta shiga wani bikin mabiya addinin Hindu a birnin Durban na Afirka ta Kudu domin nuna godiya ga abin bautarsu Kali.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wata tauraruwar fim a Afirka ta Kudu Thuso Mbedu yayin da ta ke shanawa a bikin baje fina-finai da aka yi a birnin Los Angeles ranar Lahadi.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Kashegari an tallata kayayyakin sakawa a jikin mutum-mutumi na roba a wata kasuwa da ke birnin Legas ta Najeriya...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Litinin kuma an dauko hoton manyan kayan marmari kamar wadannan manyan abarban da aake sayarwa a birnin.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Laraba kuwa ga hoton yadda ake sayar da man girki a wata kasuwa da ke Lilongwe, babban birnin Malawi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A daidai wannan ranar ce masu babura suka yi layi a gaban wani gidan mai da ke Bukavu na kasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo - wura daya da ya rage ba a kara farashin man fetur ba a sanadiyyar mamayar da Rasha ke yi wa kasar Ukraine.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani mai tallan alawa na taimaka wa 'yan makaranta tsallaka wani titi a birnin Abidjan na kasar Koddibuwa ranar Laraba.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A wannan ranar ta Laraba dai ga wani yaro yana wasa a wata makarantar da wani mutum mai suna Diébédo Francis Kéré ya tsara - mutumin Afirka na fari da ya taba lashe lambar yabo ta Pritzker ta wadanda suka yi fice a zane-zanen gine-gine.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A birnin Benghazi na Libya kuwa, a ranar Talata wani yaro da ya dau wanka ne ke shanawa a bisa wani babur...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Taron mahaya babura mai suna "easy riders" da kungiyar masu hawa babura (Benghazi Motorcycles Club), wanda aka kafa a 2014 ya yi armashi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Dan wasan kwallon kafa na Arsenal, Thomas Partey na darawa bayan da ya jefa kwallo a ragar kungiyar Leicester City a gasar firimiyar Ingila da aka yi a ranar Lahadi.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Talata wasu masu busa algaitar zamani a Laberiya na wasa domin zagayowar ranar cika shekara 213 da haihuwar Joseph Jenkins Roberts, wanda jikan bayin da suka dawo kasar ne daga Amurka kuma ya zama shugaban kasar na farko. Ya mutu ne a ranar 24 ga watan Fabrairun 1876.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu masu kada wata garaya a birnin Addis Ababa na Habasha na wasa domin tunawa da Bishof Merkorios, wanda shi ne ya babban fadan cocin kasar na Ethiopian Orthodox Church...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An rika daukar hotunan 'selfie' yayin bikin birne bishof din wanda ya mutu yana da shekara 83, wanda kuma a 2018 ya koma kasar da zama bayan ya tafi gudun hijra ta shekara 27.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kana a ranar ta Lahadi, wasu mata suna hada wata bukka a wani sansanin masu bukatar tallafi a wajen garin Baradere na Somaliya. 'Yan Somaliya kusan miliyan bakwai ne ke fuskantar matsanancin karancin abinci da ruwan sha.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu masunta a tafkin Tangayika na zaune bisa wasu katakai da suka kera da kansu domin kama kifu a birnin Bujumbura na Burundi

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Tun da farko, wadannan masuntan sun tura kwale-kwalensu zuwa kan tudu bayan da suka dawo daga kamun kifi wanda suka yi cikin dare

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ga kuma wannan matar da ta halarci bikin zagayowar ranar sanya kayan gargajiya na kasar Tunisiya wanda aka yi ranar Lahadi.

Images subject to copyright.