Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/02/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a 27 ga watan Fabrairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Abdullahi Bello Diginza

  1. Mun mayar da Sokoto birnin yawon buɗe ido - Aliyu

    Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu

    Asalin hoton, Sokoto State Government

    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu

    Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya bayyana cewa aiki ne a gabansa, shi ya sa sukar da yake sha daga wasu mutane ba za su hana shi gudanar da ayyukan ci gaban jihar ba.

    Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin taron bude-baki da shugabannin kungiyar ‘yan kasuwa na jihar a ranar Alhamis.

    Aliyu, wanda ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kammala shirin bayar da bashi ga ‘yan kasuwa da zaran an kammala gyaran wani bangare na kasuwar Sokoto da gobara ta lalata, ya ce a shirye yake ya tallafa wajen bunkasar harkokin kasuwanci a jihar.

    A cikin sanarwar da ya fitar ta hannun daraktan yada labarai da hulda da jama’a, Abubakar Bawa, Gwamna Aliyu ya ce “ci gaban da muka samar a bayyane yake, ta ko ina. Misali, yadda ake mayar da birnin Sokoto wurin yawon bude ido.

    “Mun fahimci cewa mutane daga wasu wurare suna zuwa da daddare domin kallon birnin har ma suna daukar hotuna,” in ji Aliyu.

    Daga nan ya ce gwamnatinsa na maraba da suka mai ma’ana daga mutane masu fatan alheri.

  2. Gwamnatin Guinea ta ce ta buƙaci a dakatar da maido da ƴan kasarta daga Jamus

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Shugaban Guinea, Mamady Doumbouya

    Gwamnatin Guinea ta ce ta buƙaci a dakatar da mayar da ƴan ƙasarta daga Jamus, a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan korar da aka yi wa ƴan ƙasar a baya-bayan nan.

    A yayin wani taron manema labarai a jiya Alhamis, ministan harkokin wajen ƙasar Morissanda Kouyaté ya amince cewa, ƴan ƙasar Guinea kusan 6000 ne ke zaune a ƙasar ta Turai cikin yanayi da ya saɓawa ƙa'ida, amma ya dage cewa sun cancanci a mutunta su.

    Rahotannin korar mutanen sun yi ta yawo a shafukan sada zumunta, tare da yin kira ga gwamnatin Guinea da ta ɗauki mataki.

    Wani mai magana da yawun ma'aikatar harkokin cikin gida ta Jamus ya shaida wa AFP cewa an kori ƴan ƙasar Guinea 30 a watan Janairun wannan shekara, baya ga korar 169 a shekarar 2025.

    A wata hira da manema labarai na cikin gida, Jakadiyar Jamus a Guinea Irene Biontino ta ce baƙin hauren da aka kora ba su da cikakkun takardun da za su ci gaba da zama a ƙasarta.

  3. Amurka ta gargaɗi Sudan ta Kudu game da jinkirin tabbatar da zaman lafiya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta yi kakkausar gargaɗi ga Sudan ta Kudu game da jinkirin tafiyar da harkokin mulki da zaman lafiya.

    Amurka ta yi wannan gargaɗi ga gwamnatin rikon ƙwaryar Sudan ta Kudu kan gazawarta na ci gaba da cika alƙawuran da ta ɗauka ga al'ummarta da kuma ƙasashen duniya.

    Ofishin kula da harkokin Afirka ya ce akwai buƙatar ɗaukar matakin gaggawa idan har ana son ci gaba da samun goyon bayan Amurka.

    Gargaɗin ya mayar da hankali ne kan yarjejeniyar zaman lafiya ta 2018, wadda ta kawo ƙarshen yaƙin basasa na shekaru da dama.

    Amurka ta yi kira da a sabunta tattaunawa, wanda ke nuna cewa mataimakin shugaban ƙasar na farko Riek Machar, shugaban ƙungiyar ƴan adawa ta Sudan People's Liberation Movement-in-Opposition (SPLM-IO), yana ci gaba da kasancewa a tsare yayin da ya ke fuskantar shari'a.

    Amurka ta kuma soki yadda ake amfani da kuɗaɗen jama'a ba bisa ƙa'ida ba, tare da yin kira ga gwamnati da ta ba da fifiko ga biyan albashi da inganta kiwon lafiya da bunƙasa ilimi da samar da agajin jin kai, da kuma haɓaka ababen more rayuwa.

  4. Hatsarin jirgin ƙasa ya kashe mutum ɗaya a Italiya

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Aƙalla mutum ɗaya ne ya mutu, wasu 39 kuma aka ce sun samu munanan raunuka, bayan da wani jirgin ƙasa mai amfani da lantari ya kauce hanya a birnin Milan na arewacin Italiya.

    Jirgin mai cike da cunkoson jama'a yana tafiya ne a kan titin Vittorio Veneto na Milan a lokacin da ya ci karo da gefen wani gini.

    Ana tunanin jirgin ya kaɗe mutumin da ya mutu ne , kuma yawancin waɗanda suka jikkata fasinjoji ne.

    Motocin ɗaukar marasa lafiya da dama suna wurin kuma akwai rahotannin mutane da suka maƙale a cikin tarkacen jirgin.

    Fasinjoji sun bayyana jin wani ƙara a ƙarƙashin jirgin, jim kaɗan kafin jirgin ya faɗi.

  5. India da Isra'ila sun yi alƙawarin inganta dangantakar tsaro da fasaha a tsakaninsu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaminista Narendra Modi ya ce Indiya da Isra'ila za su zurfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro da musayar bayanan sirri yayin da ya kammala ziyarar kwanaki biyu a Isra'ila.

    A wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar ranar Alhamis, Modi da takwaransa na Isra'ila Benjamin Netanyahu sun bayyana cewa, ƙasashensu za su yi ƙoƙarin cimma ingantaciyar yarjejeniyar cinikayya tsakaninsu.

    Modi ya ce "Mun ɗauki matakin haɓaka haɗin gwiwar da ke tsakaninmu zuwa wata hulɗa ta musamman," in ji Modi a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

    Wannan dai ita ce ziyarar ta biyu da Modi ya kai Isra'ila tun shekarar 2017 kuamana kallonta a matsayin manuniya ga manufofin Indiya a yayin da take ƙoƙarin daidaita alaƙar da ke tsakaninta da Isra'ila da sauran ƙasashen gabas ta tsakiya.

  6. Alƙalin da ke sauraron shari'ar El-Rufai ya ɗauki hutu

    ....

    Asalin hoton, El-Rufai/X

    Mai shari’a Justice Belgore, wanda ke sauraron ƙarar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El‑Rufai ya shigar na tauye masa haƙƙinsa ya sanar da cewa zai tafi hutu, lamarin da ya sa ya mayar da ƙundin shari’ar ga babban alƙalin babban birnin tarayya domin a sake ba wani alƙali daban ya ci gaba da sauraron ƙarar.

    Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da mai ba da shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya fitar

    Tun a ranar Laraba 25 ga Fabrairu ne kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa yau, 27 ga watan Fabrairu domin sauraron ƙarar wanda ke neman kotu ta tilasta kare masa haƙƙoƙinsa da yake zargin an tauye.

    Shari’ar na neman a ɗauki mataki kan hukumomin tsaro da suka haɗa da ICPC da EFCC da DSS da kuma Babban Lauyan Tarayya, bisa zargin take masa haƙƙinsa.

    An tsare El-Rufai ne tun bayan da ya kai kansa ofishin EFCC da kansa domin amsa gayyatar da aka yi masaa ranar Litinin 16 ga Fabrairu 2026, kafin daga bisani a daren 18 ga watan aka sauya masa wuri zuwa hannun ICPC.

  7. An kashe ƴan Ghana 55 a yaƙin Rasha da Ukraine

    ...

    Asalin hoton, Ghana Foreign Affairs Ministry/Facebook

    Bayanan hoto, Ministan harkokin wajen Ukraine Andrii Sybiha da takwaransa na Ghana Samuel Okudzeto Ablakwa

    Ministan harkokin wajen Ghana ya bayyana cewa ƴan Ghana 55 ne aka kashe a lokacin da suke faɗa a Ukraine, daga cikin ɗaruruwan ƴan Afirka da aka ce an yaudare su don su taya Rasha yaƙi.

    Ministan Sam Okudzeto Ablakwa ya ce "An sanar da mu cewa ƴan Ghana 272 da ake kyautata zaton yaƙin ya rutsa da su tun daga shekarar 2022, inda aka kashe 55, an kuma kama 2 a matsayin fursunonin yaƙi," in ji shi a shafinsa na X.

    Ya bayyan lamarin a matsayin "abin takaici da ban tsoro", yayin da ya ke magana bayan ganawa da takwaransa na Ukraine a Kyiv. Ablakwa ya rubuta cewa "Ba za mu iya rufe ido kan wadannan alƙaluman masu ratsa zuciya ba. Waɗannan ba lambobi ba ne kaɗai, suna wakiltar rayukan mutane ne," Ablakwa ya rubuta.

    Ukraine ta faɗa a ranar Laraba cewa sama da ƴan Afirka 1,780 daga ƙasashen Afirka 36 ne aka gano suna taya Rasha yaƙi.

    Ablakwa ya ce gwamnati ta himmatu wajen bin diddigi tare da wargaza duk wata makarkashiyar ɗaukar ma'aikata ba bisa ƙa'ida ba ta intanet.

  8. An gano manyan kaburbura biyu shaƙe da gawawwaki a Gabashin DR Congo

    ...

    Asalin hoton, Göktay Koraltan / BBC

    Hukumomi a ƙasar Jamhuriyar Dimokraɗiyar Kongo sun ce sun gano maka-makan kaburbura biyu ɗauke da tarin gawawwaki a kusa da birnin Uvira da ke gabashin ƙasar.

    A baya bayan nan dai yankin ya kasance a ƙarƙashin ikon mayaƙan M23.

    Gwamnan lardin Kivu ta kudu ya ce aƙalla gawawwaki 171 aka gano a kaburburan.

    Ya ƙara da cewa ana zargin an kashe mutanen ne saboda zaton cewa suna goyon bayan sojojin gwamnati ko ƙungiyoyin mayaƙan da ke mara mata baya, duk da cewa ba a tabbatar da wannan zargi ba.

    Ƙungiyar M-23 ba ta fitar da wata sanarwa ba har yanzu dangane da zarge-zargen.

    A baya dai an taɓa zargin ɓangarorin da ke rikici da juna da aikata kashe-kashe mutane da dama.

    Rahotanni sun ce mayaƙan da ake zargin na samun goyon bayan Rwanda sun ƙwace Uvira na ɗan lokaci a wani farmaki na bazata a watan Disamba, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 1000 tare da raba kusan mutane 250,000 da muhallansu.

  9. Kotu ta ba da belin Malami

    ...

    Asalin hoton, Abubakar Malami

    Babbar kotun tarayya da ke Abuja ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Joyce Abdulmalik, ta amince da belin tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami tare da ɗansa Abdulaziz Malami, kan kuɗin naira miliyan 200,

    Sai dai kotun ta umarce su da a tsare su a gidan yarin Kuje har sai sun cika sharuddan belin da aka gindaya musu.

    Mai shari’ar ta bayar da belin ne bayan ta saurari hujjojin neman beli da lauyansu, Joseph Daudu ya gabatar.

    Kotun ta ce dole ne kowannensu ya gabatar da mutane biyu a matsayin masu tsaya musu, inda ɗaya daga cikinsu dole ne yana da fili a unguwar Maitama ko Asokoro.

    Haka kuma sai an ajiye takardun mallakar filin tare da fasfo din masuntsaya musu a wurin Mataimakin Magatakardan kotu.

    Kotun ta kuma umarci Malami da ɗansa su miƙa fasfonsu da hotunansu ga kotu.

    An sanya ranar 4 ga Maris domin fara shari’ar.

    Hukumar tsaro ta farin kaya,DSS ce ta gurfanar da su kan tuhume-tuhume guda biyar da suka shafi zargin tallafawa ta’addanci da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

  10. 'Rashin lantarkin Najeriya na da nasaba da ƙarancin isar gas a tashoshin samarwa'

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da sauye-sauyen gwamnati kan samar da lantarki a Najeriya, NISO ta bayyana cewa matsalar ƙarancin wutar lantarki da ake fuskanta a ƙasar na da nasaba da ƙarancin isar gas zuwa tashoshin samar da wuta.

    A cewar hukumar, matsakaicin ƙarfin samar da wuta a yanzu na kusan megawatt 4,300 ya dogara ne da ƙarancin gas da ake samu a tashoshin samarwa.

    Hukumar ta ce tashoshin ne ke suke samar da mafi yawan wutar lantarki a ƙasar, don haka duk wani tangarda ko ƙaranci a isar gas yana tasiri kai tsaye kan ƙarfin samar da wuta da kuma yawan wutar da ke shiga kamfanin rarraba wutar.

    Hukumar ta yi alƙawarin ci gaba da aiki tare da masu ruwa da tsaki don ganin an dawo da cikakken isar wuta da zarar isar gas ta inganta kuma ƙarfin samarwa ya dawo yadda ya kamata.

    Duk da cewa wannan yanayi na iya haifar da matsala ga masu amfani da wuta, NISO ta yi kira ga jama’a da su fahimci halin da ake ciki a yanzu.

  11. Fadar shugaban Najeriya ta yi wa Atiku shaguɓe kan komawar Fintiri APC

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Fadar shugaban ƙasa ta yi wa tsoho mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar shaguɓe bayan sauya sheƙar gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, zuwa jam’iyyar APC, tana mai cewa matakin babbar koma baya ne ga burinsa na takarar shugaban ƙasa.

    Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafin sada zumunta nsa na X ranar Juma’a.

    Ya ce sauya sheƙar Fintiri na nuna cewa Atiku ba shi da cikakken farin jini a jiharsa ta asali.

    Sanarwa ya ƙara da cewa "gwamna Finitri ya ɗauke wa Atiku duk wata ƙarfinsa ta jiharsa zuwa jam’iyyar shugaba Bola Tinubu ta APC.

    A cewar sanarwar, "ɗan takarar da ba shi da ƙarfi a garinsa ba zai iya tallata kansa ga sauran yankuna ba."

    Fadar shugaban ƙasar ta kuma shawarci Atiku da ya yi tunanin yin ritaya daga siyasar jam’iyya, tare da komawa “gidansa na biyu” da ke hadaddiyar Daular Larabawa musamman a birnin Dubai.

    Sanarwar ta kuma bayyana cewa yayin da zaɓen shugaban ƙasa ke ƙaratowa cikin ƙasa da shekara guda, sauya sheƙar Fintiri na daga cikin manyan matsalolin da ka iya shafar shirin Atiku na sake tsayawa takara, tana mai cewa wannan lamari babbar barazana ce ga burinsa na siyasa.

  12. Tinubu ya amince da sabunta wasu manyan titunan ƙasar uku

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Najeriya, Bola Tinubu ya amince da sabunta wasu manyan titunan tarayya a jihar Neja.

    Titunan da za a sabunta sun haɗa da itin Mokwa–Bida mai tsawon kilomita 120 da na Mokwa–Makera mai tsawon kilomita 63, da kuma titin Bida–Lanbata mai tsawon kilomita 123.5 wanda idan aka hada Jimillar tsawo da nisan titunan guda uku zai kai kilomita 306.5.

    A cikin wata sanarwa da ministan ayyuka David Umahi ya fitar ta hannu mai taimaka masa a harkokin yada labarai, shugaba Tinubu ya amince har da tsawaita titin Bodo–Bonny domin haɗawa da Titin Gabashin kasar zuwa amma

    Sanarwar ta ce za a kuma sanya fitilun tituna masu amfani da hasken rana a titunan.

    Minista David Umahi a sanarwar ya nuna godiya ga Shugaba Tinubu bisa ƙoƙarinsa na sake gina irin waɗannan titunan da suke cikin muhimman hanyoyin tattalin arziki na ƙasa, waɗanda za su ƙara haɗin kai da kasuwanci, da ci gaban ƙasa.

  13. Sojojin Najeriya sun daƙile yunƙurin satar mutane a hanyar Enugu zuwa Otukpo

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun daƙile wani yunƙurin satar mutane a hanyar Enugu–Otukpo, inda suka ceto mutum uku ba tare da wani rauni ba.

    A cikin sanarwar da ta fitar a shafina na X, rundunar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 25 ga Fabrairun 2026, lokacin da sojoji ƙarkashin Operation WHIRL STROKE suke gudanar da sintirinsu na dare daga sansaninsu da ke Otukpo.

    A yayin sintirin ne sojojin suka samu sahihan bayanai kan motar fasinjoji da ta saci mutanen inda sojojin suka tafi wurin nan take, suka bi sawun motar inda suka kama masu satar mutanen a hanyarsu ta tserewa.

    Sanarwar ta ce ba a samu wata arrangama tsakanin sojojin da masu garkuwa da mutanen ba saboda sun tsere inda suka bar mutanen da suka sace.

    Kakakin rundunar ya shawarci direbobi da su lura da rashin motsin motoci a tazara mai kimanin kilomita biyu da kuma dakata wa don tantance yanayi idan akwai abin da bai dace ba.

  14. China ta buƙaci a shiga tattaunawa kan yaƙin Afghanistan da Pakistan

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma’aikatar harkokin wajen China ta bayyana matuƙar damuwa kan tashin hankalin da ke ƙaruwa a kan iyakar Afghanistan da Pakistan inda ta buƙaci ƙasashen biyu su “warware duk wata matsala da bambance-bambance da nufin kawo ƙarshen yaƙin ta hanyar tattaunawa da sulhu.

    Ma’aikatar ta ce China tana “ƙoƙarin shiga tsakani wajen sasanta rikicin ta hanyoyi nata, kuma a shirye take ci gaba da taka rawar gani don rage tashin hankali da inganta dangantakar ƙasashen biyu.”

    Mai magana da yawun ma’aikatar, Mao Ning, ya ce "samun ƙaruwa a rikicin zai haifar da lahani da asara ga kasashen biyu."

    China ta nuna cewa kawo ƙarshen rikicin “yana cikin muhimman muradun ƙasashen biyu da al’ummominsu, kuma zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.”

  15. Ani yi zanga-zanga kan hukuncin gwamnatin Habasha na cire wasu yankuna daga ikon Tigray

    ...

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Manyan zanga-zanga sun ɓarke a yankin Tigray na Habasha bayan gwamnatin tarayya ta yanke hukuncin cire wasu ƙananan yankuna guda biyar daga ƙarƙashin ikon gudanarwar Tigray a zaɓukan ƙasa masu zuwa.

    Masu zanga-zangar sun taru a Mekelle da sauran birane, suna sukar matakin a matsayin “hukunci mai haɗari” da kuma “sanarwar shiga yaki.”

    Majalisar Tarayya ta yanke hukunci cewa yankunan da ake taƙaddama a kansu da suka hada da Korem Ofla, Raya Alamata, Humera, Adi Remets, da Tselemti ba za su kasance ƙarƙashin ikon Tigray ba.

    Hukuncin ya haifar da ƙiyayya daga yankin Tigray da jam’iyyun siyasa, da ƙungiyoyin farar hula, waɗanda suka bayyana shi a matsayin abin da bai dace ba da sabawa yarjejeniyar Pretoria da ta kawo ƙarshen yakin Tigray a 2022.

    A gefe guda kuma jam’iyyar adawa ta NaMA ta yi maraba da hukuncin, tana cewa tana goyon bayan matsayar Majalisar Tarayya.

  16. Amurka ta yanke wa ɗan ƙasar hukuncin ɗaurin rai da rai kan lalata da yara a Burkina Faso

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta yanke wa wani ɗan ƙasar mai suna Fode Sitafa Mara da ke da shekara 41 hukuncin ɗaurin rai da rai bayan an same shi da laifin lalata da wasu ’yan mata biyu ƙanana yayin da yake aiki a ofishin jakadancin Amurka da ke Burkina Faso.

    Ma’aikatar shari’ar Amurka ta ce an yanke masa hukuncin ne ranar Laraba bayan shari’ar makonni biyu da aka gudanar a watan Oktoban 2025 a wata kotun tarayya da ke Maryland.

    Alƙalai sun same shi da laifuka huɗu na cin zarafin ƙananan yara mata ta hanyar lalata da kuma yunƙurin jan hankalinsu tare da yunƙurin hana gudanar da bincike.

    Masu gabatar da ƙara sun bayyana cewa laifukan sun faru ne tsakanin shekarun 2022 da 2023 a Ouagadougou, inda yake aiki a ofishin jakadancin Amruka a Ouagadougou.

    Shaidu sun nuna cewa an aikata laifukan ne a wani gida da aka tanada domin ma’aikatan diflomasiyya na Amurka.

    Rahotanni sun ce waɗanda aka cutar sun kasance ’yan mata masu shekaru 13 da 15 a lokacin da lamarin ya fara, kuma sun fito daga marasa galihu. ne

    Masu gabatar da ƙara sun ce mutumin ya yi amfani da halin da suke ciki wajen cin zarafinsu tsawon kusan shekara guda.

  17. Shugabannin MDD sun yi tsokaci kan rikicin Afghanistan da Pakistan

    Gutterresh

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, da shugaban hukumar kare haƙƙin bil’adama, Volker Türk, sun yi tsokaci kan halin da ake ciki a rikicin da ya barke tsakanin Afghanistan da Pakistan.

    Guterres ya yi kira ga ƙasashen biyu da su bi doka da ƙa’idojin kasa da kasa ba tare da tangarda ba, musamman ma dokokin jin ƙai na kasa da kasa.

    A nasa bangaren kum, Türk ya yi kira ga Afghanistan da Pakistan da su shiga tattaunawa don shawo kan rikice-rikicen kan iyaka da harin jiragen saman da ke kashe mutane,

  18. Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri ya koma APC

    Gwamnan Adamawa

    Asalin hoton, Ahmadu Fintiri/X

    Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya sanar da sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar APC a hukumance.

    A jawabin da ya yi wa al’ummar jiha a ranar Juma’a, gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne tare da duka mambobin majalisar zartarwarsa da manyan jiga-jigan jam’iyyar adawa ta PDP, kamar yadda jaridun ƙasar suka ruwaito.

    Sauya shekar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ganin sauya sheƙar wasu gwamnoni da jiga-jigan jam’iyyun adawa zuwa jam’iyyar APC mai mulki a Nigeria.

    Har yanzu dai babu cikakken martani daga shugabannin jam’iyyar PDP na ƙasa dangane da matakin gwamnan.

    A baya-bayan nan ne dai Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kai ziyarar aiki jihar, tare da ƙaddamar da wasu ayyukan da gwamnan ya gabatar, matakin da wasu ke ganin tamkar zawarcin gwamnan ne.

    Matakin gwamnan na zuwa ne kwana biyu bayan kakakin majalisar dokokin jihar, Bathiya Wesley, ya fice daga PDP tare da wasu mambobin majalisar 13.

  19. Iran ta yi tayin shiga tsakanin rikicin Pakistan da Taliban

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce ƙasarsa a shirye take ta taimaka wajen “sauƙaƙa tattaunawa” tsakanin Pakistan da Afghanistan bayan da rikici ya barke tsakanin kasashen biyu..

    Ya kuma yi kira ga ƙasashen biyu da su “warware bambance-bambancensu ta hanyar kyakkyawar makwabtaka da tattaunawa.”

    A baya, Iran ta riga ta ba da tayin shiga tsakanin ƙasashen biyu a matsayin mai shiga tsakani yayin da zaman dar-dar kan iyakar ƙasahen ke ƙaruwa

  20. Yaƙi ya ɓarke tsakanin Pakistan da Taliban

    yaƙi

    Asalin hoton, Getty Images

    Jiragen yaƙin Pakistan sun kai hare-hare cikin ƙasar Afganistan, inda suka yi ruwan bama-bamai a wasu sassan Kabul da Kandahar da Paktia, yayin da ƙasashen biyu ke ci gaba da gwabza faɗa tsakaninsu.

    Pakistan ta ce ta kai hare-hare ta sama da ƙasa kan yankunan Taliban da hedkwatar soji da wata cibiyar adana makamai.

    Wani saƙon da ministan tsaron Pakistan, Kwaja Asif ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ya ce yanzu sun fara yaƙi da Afghanistan yana mai cewa haƙurinsu ya ƙare. Tun da farko Taliban ta ce dakarunta sun kai hari kan jami'an tsaron kan iyakar Pakistan.

    Wasu majiyoyi na Taliban sun ce aƙalla sojojin Pakistan 10 aka kashe, Pakistan kuma ta ce ta kashe dakarun Afgahnistan sama da 70.