Rufewa
Masu bin shafin namu nan muka kawo ƙarshen labaran.
Sai gobe idan Allah ya kai mu
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 24 ga watan Fabrairun 2026.
Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammad
Masu bin shafin namu nan muka kawo ƙarshen labaran.
Sai gobe idan Allah ya kai mu

Asalin hoton, Reuters
Aƙalla mutum 20 ne suka mutu a kudu maso gabashin jihar Minas Gerais da ke Brazil sakamakon mamakon ruwan da aka tafka tun yammacin jiya zuwa yau Talata, lamarin da ya jano ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa.
Yawancin waɗanda suka mutu sun fi yawa a birnin Juiz, inda jami'ai suka ce mutum 15 sun mutu sai wasu shida a garin Uba.
Ana ci gaba da aikin ceto, inda ma'aikata ke neman gwamman wadanda suka bata bayan gidajensu sun ruguje da tsakar dare.
Shugaban Brazil Luiz Inácio Lula da Silva ya aike da sakon ta'aziyya da jaje ga iyalan wadanda lamarin ambaliyar ta shafa.
Ya ce gwamnati za ta yi mai yiwuwa domin taimakawa mutanen, an kuma kaddamar da neman mutane a Juiz de Fora.
A sakon da ya wallafa a shafin X, shugaba Lula ya ce zai maida hankali kan bai wa mutanen da suka rasa muhallansu matsugunai, da abinci da barguna da magani.
Rahotanni sun bayyana mutane 440 ne suka muhallansu a jihar Juiz de Fora, inda gwamnatin jihar ta samar da sansanin wucin gadi, da sutura da ruwa mai tsafta da abinci da sauran kayan buƙatu.

Asalin hoton, EPA
Wani diddigi da sashen Rasha na BBC ya yi tare da abokan hulɗarsa suka yi, ya nuna cewa sojojin Rasha fiye da 200 ne suka mutu cikin shekara huɗun da ƙasar ta kwashe tana yaƙi da Ukraine.
BBC ta cimma ƙididdigar ne ta hanyar lissafa jerin saƙonnin ta'aziyya da wasu alƙaluman gwamnati.
A shekarar da ta gabata, BBC ta ƙirga saƙonnin ta'aziyya kusan 50,000, amma akwai dubbai da ba a kai ga fitar da su ba.
Masu sharhi na ganin cewa akwai yiwuwar adadin sojojin da suka mutu ya zarta alƙaluman da BBC ta fitar.
Gwamnatin Rasha ba ta wallafa alƙaluman waɗanda suka mutu a baya-bayan nan ba.

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni daga Lebanon sun ce Israila ta yi gargadin za ta kai wa Lebanon mumuman hari idan ƙungiyar Hezbollah ta shiga yaƙi tsakanin Amurka da Iran.
Ministan harkokin wajan Lebanon Joe Roggi ya ce alamu sun nuna cewa Israila za ta iya kai wa wasu muhiman wurare hari kamar filin jirgin sama.
A ranar Alhamis ne ake sa ran Iran da Amurka za su sake tattaunawa, duk da cewa Amurka na ci gaba da tura ƙarin sojoji zuwa yankin.
Ƙungiyar Hizbullah na samun goyon bayan Iran kuma a baya ta riƙa kai wa wasu wurare na Amurka hari

Asalin hoton, Umar Namadi/FB
Gwamnanatin jihar Jigawa a Najeriya ta ce tana iya bakin ƙoƙarinta don ganin an saki yarinyar nan Walida Abdulhadi ƴar asalin jihar da ake zargin wani jami'in DSS da sace ta tare da sauya mata addini.
Cikin wata sanarwar da sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar, Hamisu Mohammed Gumel ya fitar ya ce gwamnatin jihar na ɗaukar lamarin da matuƙar muhimmanci, sakamakon irin tausayin da labarin ke ɗauke da shi.
Batun Walida na ci gaba da ɗaukar hankalin ƴan Najeriya, inda ƙungiyoyin fararen hula ke ci gaba da kiraye-kirayen yi wa yarinyar adalci.
Tun da farko dai an zargi wani jami'in DSS ta sace yarinyar daga jihar Jigawa tare da tilasta mata aurensa har ta haihu da kuma sauya mata addini.
A watan da ya gabata ne dai wata kotu a ƙasar ta bayar da umarnin sakin Walida tare da sada ta da iyayenta, to sai dai har yanzu tana ci gaba da tsare a hannun hukumar DSS.
Gwamnatin jihar ta ce ma'aikatar shari'ar jihar na biye da batun yarinyar domin tabbatar da an bi duka matakan shari'ar da suka dace cikin doka.
''Ma'aikatar na aiki da hukumomin da lamarin ya shafa domin kare ƴancin yarinyar'', a cewar sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa gwamnan jihar da kansa tare da wasu manyan gwamnatin jihar sun tuntubi hukumomin da lamarin ya shafa domin tabbatar da adalci cikin lamarin.

Asalin hoton, X/Nigeria Presidency
Shugaban Najeriya ya sanar da naɗin Olatunji Rilwan Disu a matsayin sufeta-janar na ƴansandan kasar, bayan ajiye aikin tsohon mai riƙe da muƙamin Kayode Egbetokun.
Cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar, ta ce "bisa la'akari da matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar, da kuma dogaro da dokokin ƙasa, Shugaba Tinubu ya amince da naɗa Mataimakin Sufeta-Janar na ƴansandan Najeriya Tunji Disu a matsayin mai riƙon muƙamin Sufeta-Janar na ƴansanda, inda zai fara aiki nan take.
"Kamar yadda dokar aikin ƴansanda ta 202 ta tanada, Shugaba Tinubu zai kira taron Majalisar Ƴansanda ta Najeriya nan ba da daɗewa ba domin duba cancantar naɗin AIG Disu, inda bayan haka ne za a tura sunansa zuwa ga majalisar dattijai," a cewar sanarwar.

Asalin hoton, Reuters
Shugabannin ƙasashen yamma sun yi yaba wa jajircewa da tsayin daka da Ukraine ta nuna a daidai lokacin da aka cika shekara huɗu da mamayar da Rasha ta yi wa ƙasar.
Firaministan Birtaniya, Keir Stammer ya jinjina wa abin da ya kira tirjiyar da Ukraine ta nuna .
Shi kuwa shugaba Emmanuel Macron na ƙasar Faransa ya bayyana harin na Rasha a matsayin gazawar sojoji da tattalin arziki da kuma dabarun yaƙi.
Shi ma a jawabinsa, shugaba Vlodimyr Zelensky ya ce idan aka yi waiwaye kan mamayar da aka yiwa ƙasarsa tare da la'akari da halin da suke ciki a yanzu, za a iya cewa sun yi ƙoƙari wajan kare yancin ƙasarsu

Asalin hoton, Getty Images
Firaministan Senegal ya gabatar da wasu sabbin dokoki da za su iya ninka hukunci ga masu auren jinsi a ƙasar zuwa ɗaurin shekara 10.
Ousmane Sonko ne ya gabatar da ƙudirin a majalisar dokokin ƙasar da ke birnin Dakar bayan amincewar majalisar m inistocin ƙasar a makon da ya gabata.
Ƙudirin na zuwa ne bayan kama wasu maza 12 a wannan wata bisa zarginsu da neman jinsi.
A wani labarin makamancin wannan kuma hukumomin Uganda sun kama wasu mata biyu bisa zarginsu da sunbatar juna a bainar jama'a.
A ƙarƙashin dokokin Uganda auren jinsi babban laifi ne da ka iya janyo wa mutum hukuncin ɗaurin rai da rai ko ma hukuncin kisa.

Asalin hoton, NASS
Majalisar dokokin Najeriya ta ɗage zamanta zuwa ranar 5 ga watan Maris mai kamawa.
Tun da farko an tsara majalisar za ta koma zama ranar 24 ga watan Fabrairu.
Sai dai cikin wata sanarwa da akawun majalisar, Kamoru Ogunlana ya fitar, ya ce majalisar ta ɗage komawar ne domin bai wa kwamitocinsa damar kammala ayyukan da ke gabansu na kare kasafi.

Asalin hoton, Nigerian police force/X
Babban sufeton ƴansandan Najeriya Kayode Egbetokun ya sauka daga muƙaminsa.
Wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta shaida wa BBC cewa Kayode Egbetokun ya ajiye aikinsa ne a ranar Talata.
Har zuwa yanzu, rundunar ƴansandan ƙasar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan lamarin.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce game da makomar shugabancin rundunar, kodayake babu cikakken bayani a hukumance kan dalilin ajiye aikin.
A watan Yunin 2023 ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da Kayode Egbetokun a matsayin wanda yake son naɗawa muƙamin sufeta-janar na ƴansandan ƙasar, inda a ƙarshen watan Oktoban shekara ta 2023 Majalisar ƴandsanda ta ƙasar ta tabbatar da nadin nasa.

Asalin hoton, Getty Images
Wata mummunar gobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar Yobe inda ta ƙone wani ɓangare na kasuwar da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Gobarar ta lalata rumfuna a kasuwar wadda ke hada-hada mako-mako, lamarin da ya jefa, ɗimbin mutanen da suka dogara da kasuwar wajen harkokin rayuwarsu cikin mawuyacin hali.
Gobarar dai ta tashi ne jiya da yamma daf da lokacin buɗa bakin azumin ramadan, inda ta mamaye rumfuna 135 wadanda aƙasarinsu na kwano da katako ne wasu kuma na itace da kara.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Yobe, Dr. Muhammad Goje ya tabbatar da aukuwar wannan gobara.
Ya ƙara da cewa gobarar ba ta shiga shaguna ba kuma ba a rasa rai ko ɗaya ,a a gobarar.
Dr Muhammad Goje ya ƙara da cewa wannan tashin gobara a kasuwar Fika itace ta uku da aka samu a kasuwanni daban-daban cikin kasa da wata daya a jihar ciki harda kasuwar Bukarti, inda rumfuna kusan dari suka ƙone, sai kuma kasuwar Fuchimiran a ƙaramar hukumar Geidam, inda rufunan da gidajen mutane da dama suka kone.

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma jigo a jam'iyyar haɗaka ta ADC, Atiku Abubakar, ya ce iyalan tsohon gwamnan Kaduna, Naisr El-Rufa'i da abokansa da masu hulɗa da shi sun damu matuƙa kan lafiya da walwalarsa yana mai cewa idan wani abu ya faru da shi, gwamnati ce ke da alhakin hakan.
Atiku ya bayyana hakan ne a shafinsa na X.
Ya ce "dole ne gwamnati ta fito ta fayyace wace hukuma ce ke tsare da El-Rufai, ko EFCC ko ICPC ko DSS ko wata hukumar tsaro ta daban."
A cewarsa, "ɓoye bayanai a irin wannan yanayi na tsare mutum yana ƙara haifar da shakku a zukatan jama'a, alhali ‘yan ƙasa na da haƙƙin sanin gaskiya.
Atiku ya jaddada cewa duk hukumar da ke da alhakin tsare shi tana da nauyin kundin tsarin mulki na tabbatar da tsaronsa da mutuncinsa da samun kulawar lafiya, da kuma damar ganawa da iyalansa da lauyoyinsa.
Ya ƙara da cewa "rahotannin da ke cewa ya samu haɓo wato zubar jini ta hanci tare da zargin hana iyalansa ganinsa abin damuwa ne ƙwarai kuma ba abin amincewa ba ne a tsarin dimokuraɗiyya."
Ya ce idan hukumomi ba za su iya tabbatar da lafiyarsa da haƙƙoƙinsa ba, to hanyar da ta dace bisa doka da jin ƙai ita ce a ba shi beli ba tare da ɓata lokaci ba.
A cewarsa, "idan wani abu ya same shi, alhakin hakan zan kasance a kan gwamnati ne."

Asalin hoton, El-Rufai/X
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci babban kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da hukumar tsaro ta DSS daga ci gaba da tuhumarsa, yana mai cewa zarge-zargen da ake masa ba su da inganci kuma sun saɓa wa doka da tsarin shari’a.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata ƙara da ya shiga a gaban kotu ta hannun mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye ya fitar.
Ƙarar ta ce El-Rufai ya nemi a soke tuhumar da DSS ke yi masa gaba ɗaya bisa hujjar cewa ba ta bayyana wani laifi da ya aikata da doka ta tanada ba kuma ba ta nuna hujjar farko ba, kuma cin zarafin tsarin kotu ne.
Ya kuma buƙaci kotu ta wanke shi gaba ɗaya daga zargin da ake masa.
Bugu da ƙari, El-Rufai ya kuma nemi kotu ta umarci DSS ta biya shi diyyar Naira biliyan biyu, yana zargin hukumar da amfani da tsarin shari’a wajen tsangwama da muzanta shi a bainar jama’a.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Ƙasashen Musulmai ta Duniya (OIC) ta yi Allah-wadai da kisan gillar fararen hula da satar mata da yara da aka yi a jihar Zamfara, arewa maso yammacin Najeriya, a ranar 21 ga Fabrairu, 2026.
Sanarwar da ƙungiyar ta fitar ta bayyana cewa "wannan hari na ƴanbindiga na da muni matuƙa kuma ya saɓa wa dukan ka’idojin ɗan adam."
Ta ƙara da cewa "ƙungiyar ta nuna cikakken goyon baya ga gwamnatin Najeriya da mutanen ƙasar, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa, da fatan Allah ya ba waɗanda suka ji rauni lafiya.
"Ƙungiyar ta buƙaci a sako mata da yara da aka sace ba tare da wani sharaɗi ba, domin dawo da su gida lafiya," in ji sanarwar.
Ƙungiyar ta sake jaddada cewa "dukan ayyukan ƴanbindiga ba za su taɓa samun goyon bayan ƙungiyar ba," kuma za ta ci gaba da tallafawa ƙasashen membobinta wajen yaki da irin waɗannan mummunar annoba.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Human Rights Watch ta soki hukuncin da wata kotun soji a Kamaru ta yankewa sojoji uku da wani ɗan ƙungiyar sa-kai da aka tabbatar sun kashe aƙalla fararen hula 21 a yankin Arewa maso Yamma a 2020 inda ta ce hukuncin bai dace da mummunan laifin da suka aikata ba.
Ƙungiyar ta ce hukuncin ɗaurin shekaru biyar zuwa goma da kotun ta yanke musu “yayi sauƙi dayawa” kuma bai dace da laifin da suka aikata ba.
Lamarin ya faru tun watan Fabrairun 2020 inda sojojin Kamaru tare da taimakon wasu masu tayar da ƙayar baya suka kai hari ƙauyen Ngarbuh, inda suka kashe mutane 21, ciki har da yara 13 da wata mata mai juna biyu. Sun kuma azabtar da mazauna ƙauyen tare da ƙone gidaje da kuma sata.
An same su da laifukan kisa da ƙone dukiya da lalata kadarori, inda aka yanke musu hukuncin zaman gidan yari tsakanin shekara biyar zuwa goma.
Ilaria Allegrozzi, babban mai bincike kan Afirka a ƙungiyar, ta ce kotun soji ta gaza gurfanar da manyan kwamandoji da suka ba da umarnin harin.
Ta ce gazawar masu shari’a da masu gabatar da ƙara wajen bincikar waɗanda ke da alhakin jagorancin aikata laifin tare da rashin bai wa iyalan waɗanda abin ya shafa diyya, yana ƙara wahala a lamarin.
Ƙungiyar ta yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayar da taimako na shari’a da fasaha ga iyalan waɗanda abin ya shafa domin su iya neman diyya.

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar wakilan Amurka ta kammala tare da miƙa rahoton binciken da ta yi kan zargin muzgunawa da kashe Kiristoci a Najeriya, lamarin da ya daɗe yana jan hankali tare da haifar da zazzafar muhawara.
Ɗanmajalisar wakilan Amurka, Riley M. Moore ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, wadda ya bayyana da rahoton da za su miƙa ga Shugaban Amurka Donald Trump.
More ya ce rahoton ya ƙunshi cikakken bayanin kan abin da ka bankaɗo da kuma wasu matakan da suke so a ɗauka domin "kawo ƙarshen muzgunawa Kiristoci a Najeriya."
Sauran ƴan majalisar da suka taya Moore aikin sun haɗa da wasu ƴan kwamitin majalisar kan kasafin kuɗi da na harkokin ƙasashen waje, inda suka je tare zuwa fadar gwamnatin Amurka domin miƙa rahoton a hukumance.
Sun yi wannan aikin ne bayan an kafa kwamitin bincike a majalisa, biyo bayan ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ke buƙatar sa ido da Trump ya yi a ranar 31 ga watan Oktoban 2025.

Asalin hoton, Bayo Onanuga/X
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya ce dole ne a gyara abubuwan da ba sa aiki a ƙasar tare da haɗin gwiwar ƴan kasa domin tabbatar da ci gaban al’umma da tsaron rayuka.
Tinubu ya fadi hakan ne a walimar buɗe baki da ya shirya wa gwamnoni da sauran muƙarabban gwamnati a fadar shugaban ƙasa.
Tinubu ya ce "Dole ne mu kasance masu ƙarfin hali wajen gyara abin da ba ya aiki kuma mu haɗa kai wajen kare darajarmu, ƙasar sai ta fi zama mafi aminci kuma mafi ƙarfi idan aka haɗa hannu wajen cimma waɗannan manufofi."
A jawabin sa, Tinubu ya bayyana shirinsu na kafa ƴansandan jihohi domin magance matsalolin tsaro yana mai cewa "tsaro shi ne ginshiƙin arziki, domin idan babu tsaro, noma ba zai bunƙasa, kasuwanci ba zai girma, kuma iyalai ba za su sami natsuwa ba."
Shugaban ya kuma yi kira ga gwamnonin da su ƙara ƙarfi wajen ayyukan jin kai a wannan watan mai tsarki inda ya ce "akwai buƙatar tallafa wa matasa da mata da ke ɗaukar nauyin iyalansu, da kuma zuwa ga al’ummomin ƙananan hukumomi inda fata kan samu rauni."
Tinubu ya kuma jaddada cewa alkawarin da ya yi wa ‘yan Najeriya ba zai samu jinkiri ba. Ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da aiki tukuru wajen samar da fata da dama, da tsaro ga kowa da kow

Asalin hoton, Getty Images
Rasha na ci gaba da yin luguden wuta a kan Ukraine, yayin da ƙasar ke cika shekara huɗu tun bayan ƙaddamar da mamaya kan Ukraine.
Jami'an Ukraine sun ce mutane biyar, ciki har da yaro guda sun ji rauni kuma an lalata gidaje da dama a hare-haren jirage marasa matuƙa, musamman a birnin Zaporizhzhia.
An tsara gudanar da tarukan tunawa da ranar mamayar a wurare da dama, kamar Bucha, inda dakarun Rasha suka kashe sojojin Ukraine da dama.
Ana sa ran shugabanni da 'yan siyasa daga faɗin Turai za su halarci Kyiv babban birnin Ukraine din don halartar tarukan.

Asalin hoton, Getty Images
Sabon harajin kashi 15 cikin 100 da shugaban Amurka, Donald Trump ya laftawa dukan ƙasashen duniya ya fara aiki.
Ya sanar da matakin ne, bayan hukuncin da Kotun ƙolin ƙasar ta yanke ranar Juma'a, inda ta ayyana haraje harajen da yake sanyawa a matsayin waɗanda suka saɓa wa doka.
A yanzu dai sabon harajin na kaso 15 da ya sanya ƙarƙashin wata dokar ta daban ya shafi hatta ƙawayen Amurka, ciki har da Birtaniya da Australia.
To amma duk da haka zai kasance wani sauƙi ga wasu ƙasashen kamar China da Brazil waɗanda ke takun sakar tattalin arziki da gwamnatin Trump.
Hukuncin da kotun ƙolin ta yanke ya janyo dakatar da yarjejeniyoyi da dama na cinikayyar ƙasa da ƙasa da aka amince da su ko kuma ake ƙoƙarin cimma matsaya kansu da Amurkar.

Asalin hoton, El-Rufai/X
Mai taimakawa tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, Muyiwa Adekeye ya ce hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya ICPC har yanzu ta ƙi amsa buƙatar bayar da belinsa da lauyoyinsa suka nema duk da cewa wa’adin awanni 48 na tsare mutum ba tare da tuhuma ba ya cika.
Muyiwa ya sanar da hakan ne a shafinsa na X.
Sanawar ta ce "Har yanzu ba a nuna wa lauyoyin El-Rufai wata takardar umarnin kotu da ta ba da izinin ci gaba da tsare shi ba.
Wannan na zuwa ne bayan an miƙa shi daga hannun hukumar EFCC zuwa ICPC a daren 18 ga Fabrairu, bayan ya kai kansa ofishin EFCC da safiyar 16 ga watan domin amsa gayyatar da suka yi masa..
A makon nan ne kuma ake sa ran kotu za ta saurari wasu ƙararraki biyu da suka shafi lamarin.
Ɗaya daga cikinsu ita ce karar take hakkinsa na dan Adam da ya shigar kan Gwamnatin Tarayya da hukumomin bincike ciki har da hukumar ICPC, wadda za a saurara a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja ranar 25 ga Fabrairu.
A cikin ƙarar, yana neman kotu ta umarci a sake shi bisa beli, yana mai cewa tsare shi da aka yi ba tare da cika sharuɗɗan doka ba ya saɓa haƙƙoƙinsa a matsayin ɗanadam.
Ana kuma sa ran a rana guda za a gurfanar da shi kan tuhume-tuhumen da DSS ta riga ta shigar.
Lauyoyinsa sun jaddada cewa rashin amsa buƙatar belin da kuma rashin nuna takardar umarnin tsarewa na daga cikin abubuwan da suke ƙalubalanta a shari’a, yayin da suke jiran matakin kotu kan buƙatunsu.