Gwamnatin Jigawa ta karɓi Walida Abdulhadi

Asalin hoton, FB/Umar Namadi
Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da cewa an miƙa mata matashiyar nan mai suna Walida Abdulhadi, wadda ake zargin wani jami'in rundunar tsaro ta farin kaya (DSS) da "ajiye ta a wurin shi" na tsawon shekaru.
A wata tattaunawa da BBC a yammacin yau Alhamis, kwamishinan yaɗa labarai na jihar Sagir Musa ya ce an miƙa matashiyar ga gwamnatin Jigawa ne da misalin ƙarfe biyu na ranar Alhamis.
Kwamishinan ya bayyana cewa a daren ranar jiya Laraba ne gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi ya samu sahhalewar shugabannin hukumar DSS domin karɓar matashiyar.
"Da rana, ƙarfe biyu mai girma gwamna ya kira shugaban DSS, sannan ya tura wakilci ƙarƙashin kwamishinan shari'a a na jihar da kwamishinar mata da kuma sakataren yaɗa labaran gwamnan, suka je ofishin DSS, kuma a yanzu maganar da muke yi zan iya tabbatar muku cewa wannan yarinya tana ƙarƙashin kulawar gwamnatin Jigawa," in ji Sagir.
Ya ƙara da cewa ya zuwa yammacin Alhamis Walida tana Abuja, inda za a kai ta asibiti domin duba lafiyarta.
An kwashe makonni ana kai-komo game da batun matashiyar, wadda kotu ta bayar da umarnin miƙa ta ga iyayenta.
Lauyoyin da suka shiga batun sun zargi jami'in na DSS da "sacewa tare da yin kwanciyar aure da matashiyar har ta haifa masa ɗa".




















