Rufewa
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na labari kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Haruna Kakangi, Ibrahim Yusuf Mohammed, Aisha Babangida da Ahmad Bawage
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na labari kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.

Asalin hoton, REX/Shutterstock
Firaministan Greenland ya ce ba shi da masaniya game da abin da ke ƙunshe a wata yarjejeniya kan makomar yankinsa.
Kalamansa sun biyo na Trump a Davos ranar Laraba, inda ya ce ya amince da tsarin yarjejeniyar da za a samar nan gaba, bayan ya gana da shugaban ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO.
Ministan harkokin wajen Denmark ya ce babu wakilan Greenland ko na Denmark da suka halarci ganawar, kuma NATO ba ta yi wata tattaunawa a madadinsu ba.
A gefe guda kuma, Firaministan Denmark, ya ce nahiyar Turai na samun sakamako mai kyau ne idan ta kasance tsintsiya maɗaurinki ɗaya.
Ya faɗi hakan ne gabanin taron gaggawa da shugabannin ƙasasehn Turai za su yi domin tattaunawa kan batun taƙaddamar Greenland.

Asalin hoton, Reuters
Fasinjoji da dama sun jikkata a hatsarin jirgin ƙasa na uku cikin mako ɗaya a Sifaniya.
Jirgin ya buge wata mota a kan layin dogo a yankin Murcia, sai dai bai sauka daga kan layi ba, kuma fasinjoji shida ne suka samu raunuka.
Adadin mutanen da suka mutu a hatsarin da aka samu lokacin da jiragen ƙasa biyu suka yi taho mu-gama a ƙasar ranar Lahadi ya kai 45.
A ranar Talata kuma, wani matuƙin jirgin ƙasa ya mutu bayan jirginsa ya sauka kan layi a lokacin da wani gini ya faɗo kan layin dogo a kusa da birnin Barcelona.
Ƙungiyar masu tuƙin jiragen ƙasa ta sanar da yajin aiki na kwanaki uku daga ranar 9 ga watan Fabrairu saboda rashin tsaron layukan dogo da sauran kayyayakin jiragen ƙasa.

Asalin hoton, Getty Images
Ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar a garuruwan Kauran Fawa da Unguwar Jika, da wasu garuruwa a ƙaramar hukumar Ɗan Ɗume a Jihar Katsina, bayan wani hari da wasu ’yan bindiga suka kai inda ake fargabar sun kashe mutum tara, tare da jikkata wasu 13.
Harin wanda aka kai cikin daren Alhamis na zuwa ne duk da sulhun da masu ruwa da tsaki a yankin suka jagoranta da ’yan bindigar, a wani yunƙuri na dawo da zaman lafiya da kare rayuka da kuma dukiyoyin al’umma.
Sai dai, hukumomin yankin sun ce sun halarci jana’izar mutum biyar, kuma suna ci gaba da ɗaukar matakai domin dawo da zaman lafiya.
Wani mazaunin ɗaya daga cikin garuruwan da abin ya shafa, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC cewa ƴanbindigar sun shiga garin ne a ƙafa inda suka yi ta harbi.
"Mutum tara ne suka mutu sakamakon harbin da yanbindigar suka yi, sannan 13 ne suka samu raunuka inda muka kai su asibiti domin samun kulawa. Sun ɗauki mutum aƙalla goma amma sai suka yi ta sakin mutanen sakamakon artabu. Mutum ɗaya ne ya rage a hannun su," in ji shi.
Shugaban karamar hukumar Ɗan Dume, Bishir Hadi, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce tare da shi aka yi jana'izar mutanen da aka kashe.
"Mun yi sulhu kuma mun samu nasara, tsawon wata biyar ba a kawo hari ba sai yanzu. Kafin yanzu babu ranar da ba a kawo mana hari," in ji Bishir.
Jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya ta daɗe tana fama da hare-haren ’yan bindiga.
Duk da sulhun da gwamnatin jihar ta yi da ƴanbindigar tare da sakin wasu da aka kama, amma hukumomin na cewa matakin na daga cikin yarjejeniyoyin da wasu al’ummomin jihar suka amince da su domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta zama ƙungiyar Premier da ta fi samun kuɗi karo na farko, a cewar kamfanin haraji na Deloitte.
Ƙungiyar ta lashe gasar Premier karo na 20 a bara, inda ta samu kuɗaɗen shiga da suka kai yuro miliyan 836 - wanda ya zarta na kowace ƙungiyar kwallon kafa a Ingila.
Yayin da Manchester United kuma ta faɗi zuwa mataki na ƙasa, a cewar Deloitte Football Money League.
Real Madrid ta sake ɗare wa saman jerin ƙungiyoyin da suka fi samun kuɗi a duniya, inda ta samu kuɗin shiga yuro biliyan 1.2, duk da cewa ba ta lashe Champions League ko La Liga ba a bara, sai kuma ƙungiyoyin birnin Manchester da suka rikito daga saman jerin zuwa ƙasa.
Latsa nan don karanta cikakken labarin...

Asalin hoton, Reuters
Afirka ta Kudu ta kaddamar da asusun tara kuɗi don sake gina gandun dajin Kruger wanda ambaliya ya lalata.
Hukumomin gandun dajin sun kiyasta cewa kuɗin aikin zai laƙume kusan dala miliyan 30, don haka ne suke neman gudummawar mutane.
An rufe sansanonin masu yawon buɗe ido 15 kuma har yanzu ruwa na mamaye da wasu sassan gandun dajin, kusan mako ɗaya bayan afkuwar ambaliyar.
Babu asarar rai da aka samu cikin gandun dajin, kuma yawancin dabbobi sun matsa zuwa wani wuri domin kauce wa ambaliyar.
Mamakon ruwa na tsawon makonni, ya kashe gomman mutane tare da ɗaiɗaita dubbai a Afirka ta Kudu.

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa sama da ƴan Najeriya miliyan 30 za su fuskanci matsalar yunwa a wannan shekara, saboda rage tallafin da ake bayar wa a duniya.
MDD ta ce kusan yara miliyan uku na barazanar rasa abinci mai gina jiki, inda tuni ake cikin mawuyacin hali a jihohin Borno, Yobe da kuma Adamawa waɗanda rikici ya ɗaiɗaita.
Kodinetan hukumar ba da agaji na MDD a Najeriya, ya ce yanzu ba za a iya dogaro da agajin da aka saba bayar wa ba.
Hukumar ta ce yanzu za ta mayar da hankali ne kawai kan ayyukan ceton rai, inda za ta samar da kusan dala 500,000 don taimakawa mutane miliyan biyu da rabi.

Asalin hoton, SUPPLIED
Kotun Koli da ke karkashin ikon Taliban a Afghanistan ta saki wata matashiya ƴar wasa, kwanaki 13 da ƴansandan Hisbah suka kama ta da laifin koya wa maza da mata wasan Taekwondo cikin sirri.
An tsare Khadija Ahmadzada a birnin Herat da ke yammacin ƙasar yayin da take koya wa mutane wasan.
Wani mai magana da yawun ma'aikatar ɗaɓɓaka ɗabi'u masu kyau, ya ce an kama matar ƴar shekara 22 da laifin saɓa wa dokokin shari'a bayan da aka ga mata ba tare da hijabai ba suna horo tare maza. An kuma saka kiɗa.
Taliban ta saka wa mata matakai da dama tun komawa kan mulki a Agustan 2021.

Asalin hoton, RIVERS STATE ASSEMBLY
Babban alƙalin jihar Rivers, Mai Shari’a Simeon C. Amadi, ya ƙi amincewa da buƙatar majalisar dokokin jihar na kafa kwamitin bincike mai mambobi bakwai domin binciken zargin aikata manyan laifuka da ake yi wa gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Nma-Odu.
Babban alƙalin ya bayyana cewa akwai umarnin kotu da har yanzu ke aiki, tare da ƙarar da ke gaban kotu ta ɗaukaka ƙara.
Matsayar mai shari’a Amadi na ƙunshe ne cikin wata wasika ta hukuma da ya aikawa kakakin majalisar dokokin jihar, Martin Amaewhule, inda ya tabbatar da karɓar buƙatu guda biyu daga Majalisar da ke ɗauke da kwanan watan 16 ga Janairu, 2026.
An miƙa buƙatun ne bisa tanade-tanaden Sashe na 188(4) da 188(5) na ƙundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima bayan Majalisar ta yanke shawarar fara shirin tsige gwamnan da mataimakiyarsa daga muƙami.
Sai dai a cikin wasikar, Babban alƙalin ya ce, “Dole ne ɓangarorin da abin ya shafa da kuma kotu su jira sakamakon ƙarar da ke gaban kotun ɗaukaka ƙara.”
Ya ƙara da cewa, “Saboda haka hannuna a ɗaure yake, kasancewar akwai umarnin wucin-gadi na kotu da kuma ɗaukaka ƙara kan waɗannan umarni. Don haka a wannan lokaci, doka ba ta bani damar aiwatar da aikina a ƙarƙashin Sashe na 188(5) na Kundin Tsarin Mulki ba.”

Kotun ƙolin Najeriya ta yi watsi da shari’ar da ake yi wa tsohon dogarin tsohon shugaban Najeriya, Janar Sani Abacha, wato Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya a kan kisan Kudirat Abiola, matar tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar.
A yayin zaman kotun, an shirya cewa jihar Legas za ta sake buɗe shari’ar, amma babu lauyan da ya wakilci jihar, sannan babu wata takarda da aka shigar tun daga shekarar 2014 lokacin da aka bayar da umarnin sake buɗe shari’ar a madadinta.
Lauyan Al-Mustapha, Paul Daudu ya shaida wa alƙalai cewa Legas ba ta ɗauki wani mataki don aiwatar da umarnin da aka ba ta a 2014 don sake buɗe shari’ar ba.
Lauyan ya kuma bayyana cewa a shekarar 2014, lokacin da aka ba da umarnin sake buɗe shari’ar, an bai wa Legas kwanaki 30 kacal don shigar da sanarwar ɗaukaka ƙara.
Ya ce sama da shekara tara bayan haka, ba a ɗauki wani mataki ba. Don haka, ya yi kira ga kotun da ta yi watsi da shari'ar gaba daya.
Mai shari'a Uwani Aba-Aji, wadda ke jagorantar zaman, ta nemi a tabbatar mata ko an sanar da Legas kan zaman kotun sai magatakardar kotun ya amsa da 'e'.
A wani matakin na bai-ɗaya, kotun ta amince cewa jihar Legas ba ta da niyyar ci gaba da shari'ar, kuma a sanadiyyar haka ne ta yi watsi da ita.
Daga nan ne sai kotun ta yi watsi da shari'ar.
Kudirat Abiola mata ce ga hamshaƙin ɗan kasuwan Najeriya MKO Abiola. wanda ake kyautata zaton cewa shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993, wanda tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Babangida ya soke.
An kashe ta ne a Legas sa'ilin zanga-zangar adawa da soke zaɓen na 1993.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka, Donald Trump ya jagoranci taron sanya hannu domin ƙaddamar da ''shirinsa na samar da zaman lafiya a duniya'.
A yayin jawabin da ya gabatar a taron Davos, Trump ya bayyana cewa yana da cikakken yaƙini shirin zai taimaka wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa a Gabas ta Tsakiya da kuma sassan duniya baki ɗaya.
Ya ce shirin na da damar zama ɗaya daga cikin muhimman tsare-tsare mafiya tasiri da aka taɓa ƙirƙira a tarihi.
Aƙalla mutum 20 daga cikin mahalarta taron ne suka sanya hannu kan shirin, ciki har da shugabannin ƙasashen Uzbekistan, Argentina da Azerbaijan, da kuma wakilai daga Turkiyya da wasu ƙasashen yankin Gulf.
Trump ya ƙara da cewa shirin zai yi aiki tare da Majalisar Ɗinkin Duniya, duk da cewa wasu masu suka na ganin an tsara shi ne domin ya maye gurbin wasu daga cikin ayyukan Majalisar.

Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin haƙar uranium na ORANO mallakin Faransa da ke aiki a ƙasar Nijar ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da kalubalantar ƙasar a gaban kotu kan rikicin da ya kunno kai tsakaninsu.
Haka kuma kamfanin ya gargaɗi duk wata ƙasa da za ta kuskura ta sayi uranium ɗin da ake takaddama a kai, to zai ɗauki matakan shari’a a kanta.
Shugaban kamfanin ORANO ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, yayin da yake jawabi a gaban sanatocin ƙasar Faransa.
Wannan mataki na ORANO na zuwa ne a daidai lokacin da ake yaɗa jita-jitar cewa mahukuntan mulkin sojan Nijar sun fitar da uranium ton dubu, tare da shirin sayar da shi ga wata kasa, duk da rikicin da ke tsakaninsu da kamfanin.
A baya-bayan nan kuma, gwamnatin mulkin sojan Nijar ta kafa wani kwamitin ƙwararru a farkon makon nan, wanda aikinsa shi ne tattara hujjojin doka da na kimiyya da za su taimaka wa ƙasar wajen kare kanta a rikicinta da ORANO.
Haka kuma kwamitin zai tantance haƙiƙanin farashin uranium din Nijar, domin kare muradun kasar a harkar kasuwancin ma’adinan ta

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wata ganawa mai muhimmanci da takwaransa na Ukraine, Volodymyr Zelensky a Davos, wanda ake sa ran zai gabatar da jawabi nan ba da jimawa ba.
Trump ya shaida wa manema labarai cewa wajibi ne a kawo karshen yaƙin Rasha da Ukraine, duk da cewa tun da farko ya ce saura kiris a cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ƙasashen.
Wakilinsa na musamman Steve Witkoff ya ce wani abu guda daya ne kawai ya rage, wanda ake ganin wataƙil batun buƙatar Moscow ce ga Ukraine na ta sallama ƙarin yankunanta.
Idan an jima a yau Witkoff da surukin Trump Jared Kushner za su tattauna da Shugaba Putin a Moscow.

Asalin hoton, Getty Images
Akwai rahotanni da ke nuna cewa sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu na ficewa daga babban birnin ƙasar, Juba, suna nufar arewa zuwa Jihar Jonglei, inda aka shafe kwanaki ana fafatawa da dakarun ‘yan adawa.
A jiya, babban ƙungiyar ‘yan adawa masu ɗauke da makamai a ƙasar, wato SPLA-IO, ta bayyana cewa ta ƙwace wani muhimmin gari a wani sabon farmaki da take cewa an ƙaddamar da shi ne domin matsawa zuwa Juba.
Sai dai hukumomin yankin sun ce sun fatattaki ƴan ƙungiyar SPLA-IO.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya ƙara ƙamari ne bayan da aka tsare shugaban ƙungiyar ‘yan adawa, Riek Machar, a gidan yari tare da gurfanar da shi a gaban kotu a watan Maris na bara.
Ana tuhumar Machar da cin amanar ƙasa da wasu manyan laifuka, kuma har yanzu yana tsare a hannun gwamnati.

Asalin hoton, X/Nentawe Yilwatda
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa duk naɗe-naɗen siyasa bayan zaɓukan 2027 za su kasance ne ga masu biyayya ga jam’iyyar APC kawai, ba ga ƙwararru ko mutanen da ba ƴan APC ba.
Nentawe ya faɗi hakan ne a Abuja, yayin wani taro wanda ƙaramin ministan ayyuka, Bello Goronyo, ya shirya.
Shugaban na jam'iyyar APC na ƙasa ya jaddada cewa "mulki lamari ne na siyasa, kuma duk wanda aka naɗa dole ne ya kasance yana goyon bayan jam’iyyar da ta kawo shi kan mulki".
Wani bidiyo na jawabin nasa ya bazu sosai a kafafen sada zumunta a ranar Laraba, lamarin da ya haifar da muhawara mai zafi a tsakanin ‘yan siyasa da mambobin jam’iyya da ƙungiyoyin farar hula a faɗin ƙasar.
A cewar Nentawe, "Duk wanda aka naɗa a gwamnati dole ne ya kasance a fili yana shiga harkokin siyasa tare da yin aiki kafada da kafada da jam’iyya."
"Ya ce babu wani batun 'ƙwararre' idan ana magana kan muƙaman siyasa."
Ya ƙara da cewa zai tsaya tsayin daka wajen kare matsayinsa na cewa duk wanda bai shirya yin aiki tare da APC ba, bai kamata a ba shi muƙami ba.

Ƴansanda a New Zealand sun ce an gano gawarwaki biyu a wani gida da ya ruguje sakamakon zaftarewar ƙasa a tsibirin ƙasar na arewaci.
Iftila'in ya faru ne a Papamoa, bayan mamakon ruwa da ambaliya.
An kuma samu wata zaftarewar ƙasar a wani wurin shaƙatawa da ke tsaunin Maunganui.
Wani mutum da ya tsira ya ce suna cikin ɗakin da ake yin tausa, kuma shi ne ɗakin da ya fi kusa da tsaunin, daga nan suka soma jin ginin ya na girgiza sosai.
Har yanzu ana neman mutane da dama, ciki har da kananan yara. Ana kuma ci gaba da gudanar da aikin ceto.

Asalin hoton, Getty Images
Mutane da dama, ciki har da aƙalla ƙaramin yaro guda, sun ɓace bayan zaftarewar ƙasa a wani sansani a da ke kusa da Dutsen Maunganui, na ƙasar New Zealand.
Masu aikin ceto suna wurin, suna ta ƙoƙarin tono waɗanda suka maƙalae a ƙarƙashin tarkace.
Wasu mutum biyu kuma sun ɓace sannan mutum ɗaya ya samu munanan raunuka bayan zaftarewar ƙasa a kusa da Papamoa.
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya yi ɓarna a akasarin yankunan tsibirin da ke arewacin ƙasar, inda bidiyo da aka wallafa a intanet ke nuna ɗimbin wuraren da ambaliyar ruwa ta mamaye.
An ayyana dokar ta ɓaci a yankin Bay of Plenty da sassa daban-daban na tsibirin, da suka haɗa da Northland da Coromandel da Tairāwhiti, da Hauraki.
An umurci waɗanda ke zaune a wuraren da lamarin ya shafa da su hanzarta ficewa daga yankunan.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban gwamnatin sojin ƙasar Guinea-Bissau, Janar Horta N’Tam, ya sanar da cewa za a gudanar da zaɓukan shugaban ƙasa da na majalisar dokoki a ranar 6 ga Disamba.
An bayyana hakan ne ta cikin wata dokar shugaban ƙasa da Janar N’Tam ya rattaɓa wa hannu a ranar jiya, Laraba.
Wannan sanarwa ta biyo bayan juyin mulkin da aka yi a watan Nuwambar 2025, wanda ya kai ga kifar da tsohon shugaban ƙasa, Umaro Sissoco Embalo, a daidai lokacin da ake shirin bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.
Wasu masu sa ido daga yankin, ciki har da tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, sun yi zargin cewa an shirya yunƙurin juyin mulkin ne tun da farko.
A baya, ƙungiyar ECOWAS ta ƙi amincewa da shirin gwamnatin sojin na miƙa mulki cikin shekara guda, inda ta nemi a gaggauta komawa mulkin dimokraɗiyya.
Yanzu da aka saka ranar zaɓe a 6 ga Disamba, ana sa ido ko hakan zai haifar da sauyi mai ma’ana a ƙasar da ta shahara da yawan juyin mulki.

Mazauna yankin Kurmin Wali da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna sun zargi hukumomi da ƙoƙarin hana yaɗuwar bayanai bayan sace mutane 177 daga coci uku da aka yi a ranar Litinin.
Wasu mazauna yankin sun shaida wa BBC a ranar Laraba cewa jami’an gwamnati sun hana mutane magana da kafafen yaɗa labarai, tare da ƙoƙarin toshe hanyoyin shigar ‘yan jarida zuwa cikin al’ummar.
Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce jami’ai sun gargaɗi jama’a da su yi shiru kan harin.
Haka kuma, BBC ta fuskanci matsala wajen isa Kurmin Wali, bayan da jami’an tsaro da na gwamnati suka fara ƙoƙarin hana su shiga yankin.
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ziyarci Kurmin Wali kwana uku bayan harin, inda ya yi alƙawarin kafa sansanin soji a yankin.
Ya kuma sanar da wasu matakan tallafi ga waɗanda abin ya shafa.
Sai dai iyalan waɗanda aka sace da al’ummar yankin sun ce suna cikin firgici da tashin hankali.
Da farko dai, ‘yan sanda da jami’an ƙaramar hukuma sun musanta faruwar hare-haren da sace mutanen, kafin daga bisani suka tabbatar da cewa lamarin ya faru.

Asalin hoton, Getty Images
An samu wata ƴar jarida a ƙasar Philippines da laifin bayar da kuɗaɗe dominj tallafawa ayyukan ta'addanci tare da yanke mata hukumcin ɗaurin aƙalla shekara 12 a gidan yari, a wani lamarin da ƙungiyoyin kare ƴancin ƴan jarida suka bayyana a matsayin rashin adalci.
An kama Frenchie Mae Cumpio, ƴar shekara 26 a watan Fabrairun 2020 bayan da sojoji suka kai farmaki gidanta da tsakar dare inda aka yi zargin sun samu gurneti da bindiga, da kuma tutar ƴan gurguzu a ƙarƙashin gadonta.
Ƙungiyoyin kare haƙƙi sun yi watsi da tuhume-tuhumen inda suka ce an kama ƴa jaridar ne saboda ta kasance mai sukar ƴan sanda da sojoji.
Masu lura da al'amura dai na cewa, an ƙara ƙaimi wurin take haƙƙin ƴan jarida da masu fafutuka a ƙarƙashin shugabancin Rodrigo Duterte, wanda ya ƙaddamar da mummunan shirin yaƙi da miyagun ƙwayoyi daga shekarar 2016 zuwa 2022.
A ranar Alhamis, bayan shafe shekara shida a gidan yari ba tare da shari’a ba, an wanke Cumpio daga tuhumar da ake mata na mallakar makamai da bama-bamai ba bisa ƙa’ida ba, amma an same shi da laifin bayar da kuɗaɗe domin tallafawa ayyukan ta’addanci.