Ana ci gaba da ƙirga ƙuri'u a zaɓen Uganda

Asalin hoton, Getty Images
Ana ci gaba da ƙidayar ƙuri'u a ƙasar Uganda, bayan da aka gudanar da zaɓen da ya fuskanci tsaiko sakamakon tangarɗar na'urori.
Shugaban ƙasar mai ci Yoweri Museveni da ke neman wa'adi na bakwai bayan shafe shekaru arba'in yana mulki, ya zuwa yanzu ya samu fiye da kashi 74 cikin 100 na ƙuri'un da aka ƙirga.
Babban abokin hamayyarsa fitaccen mawaƙi Robert Kyagulanyi wanda aka fi sani da Bobi Wine na biye masa inda ya samu kusan kashi 20 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa.
Tuni dai jam'iyyar Wine ta National Unity Platform (NUP) ta nuna shakku kan sahihancin sakamakon.
NUP ta kuma ce an yi wa Bobi Wine ɗaurin talala, inda jami'an tsaro suka kewaye gidansa da ke Kampala.
A gefe guda kuma, wani ɗan majalisar adawa ya zargi jami'an tsaro da kashe mutane goma a gidansa da ke tsakiyar ƙasar Uganda.
Ƴan sanda dai sun musanta wannan iƙirarin, suna masu cewa jami'an na mayar da martani ne kan wani yunƙurin kai hari a wata cibiyar zaɓe.
Tun da farko, Bobi Wine ya buƙaci magoya bayansa da su yi zanga-zanga idan an sace ƙuri'un.
Yayin da aka kidaya fiye da rabin ƙuri’un da aka kaɗa, hukumar zaɓen ƙasar ta ce tana sa ran bayyana wanda ya lashe zaɓen a ƙarshen ranar Asabar.




















