Hotunan ziyarar da Sheikh Dahiru Bauchi ya kai wa Buhari

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Bauchi, ya kai wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ziyara ranar Lahadi.

Hotunan da mai taimaka wa shugaban kasar kan kafafen sadarwa na zamani, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na Twitter sun nuna shugaban kasar da Sheikh Bauchi da dansa da ma wasu 'yan rakiyarsa a fadar Aso Villa da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, A nan shehin malamain ne da Shugaba Buhari suke musabaha.

Ko da yake ba a fadi dalilin kai ziyarar ba, amma malamin ya je fadar shugaban Najeriyar ne a yayin da matsalar tsaro ke ci gaba da ta'azzara a sassan kasar.

Malamin ya yi shuhura wajen gaya wa shugabanni gaskiya.

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, Ga dukkan alamu nan kuma suna wata magana ce mai muhimmanci.

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, A tawagar malamin har da wasu daga cikin 'ya'yansa.

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, Ministan ilimi na Najeriya Malam Adamu Adamu kenan yake gaisawa da Sheikh Dahiru Bauchi

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, Shugaba Buhari yayin da yake wa malamin rakiya inda suke sallama.

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, A nan kuma Sheikh Dahiru Bauchi ne yake jan addu'a, Shugaba Buhari na amsawa.

Asalin hoton, Buhari Sallau

Asalin hoton, Buhari Sallau