Hotuna: Yadda sarkin Hausawan Turai ya nada hakimansa

Bayanan hoto, Sarkin Hausawan Turai, Alh Sirajo Jan Kado ya nada hakimai takwas a masarautarsa da ke Paris
Bayanan hoto, Sarkin Hausawan Turai tare da Marafan Hausawa kuma Hakimin London, Alhaji Muhammadu Sanusi da kuma Dan Isa, Dr Usman T Shehu
Bayanan hoto, Hakimai takwas Sarki Jan Kado ya nada a ranar Asabar a fadarsa da ke Paris
Bayanan hoto, Wadanda aka nada sun fito daga kasashe daban-daban na Turai
Bayanan hoto, Sarki Jan Kado Na kokarin raya al'adun Hausawa a Turai
Bayanan hoto, Akwai masu rike da sarautar Dan buran, da Sallama, Da Falaki da Shamaki da kuma Uban Doma
Bayanan hoto, Masarautar na da Jakadiyar Sarki, da Giwar Sarki da kuma Gimbiyar Mawaka
Bayanan hoto, An baiwa Fati Nijar sarautar Gimbiyar Mawakan Hausawan Turai
Bayanan hoto, Baya ga wadanda aka nada sarautar, wasu sun halarci bikin nadin daga kasashe daban-daban na nahiyar Turai
Bayanan hoto, An nada Jakadiya da kuma Giwar sarki
Bayanan hoto, Masu rike da sarauta a masarautar kan sanya kaya irin na al'adar kowace masarauta da ke kasar Hausa
Bayanan hoto, Wadanda aka nada wa sarauta sun hada da mata da maza daga yankuna daban-daban
Bayanan hoto, Sarki Jan Kado Na kokarin raya al'adun Hausawa a Turai
Bayanan hoto, A makonnin baya, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ziyarci masarautar a Paris inda ya jadadda sarautar Sarkin Hausawan Turai, Alhaji Surajo Jan Kado
Bayanan hoto, Daya daga cikin kofofin shiga fadar sarkin Hausawan Turai da ke Paris a kasar Faransa.