Ana zanga-zangar da ba a taba yin irin ta ba a Sudan
Asalin hoton, AFP
Jami'an tsaro sun yi arangama da masu zanga-zanga a Khartoum, babban birnin Sudan a yayin da ake gangamin kyamar gwamnati a duk fadin kasar.
'Yan sandan kwantar da tarzoma sun jefa kwanso-kwanson hayaki mai sanya kwalla da zummar tarwatsa masu zanga-zangar.
Kungiyoyin likitoci da injiniyoyi da kuma malaman makaranta wadanda ke cikin masu zanga-zangar sun ce suna gudanar da ita a akalla wurare 50 a duk fadin Sudan.
A watan jiya ne aka soma zanga-zangar a kan matsin tattalin arziki, sai dai yanzu masu yin ta sun mayar da hankali ne kan bukatar sauke Omar al-Bashir daga mulki.
'Yar jarida Zeinab Mohammed Salih ta shaida wa BBC ranar Alhamis cewa wannan ita ce zanga-zanga mafi muni da aka yi a kasar a tarihinta.
Rahotanni sun ce 'yan sanda sun jefa hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa masu zanga-zangar a wurare daban-daban da ke da makwabtaka da Khartoum.
Tun lokacin da aka soma zanga-zangar, jami'ai sun ce akalla mutum 26 ne suka mutu, amma kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce fiye da mutum 40 ne suka mutu.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai