Za mu yi amfani da na'urar Card Reader a 2019- INEC
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar zaben Najeriya wato INEC ta bayyana cewa za ta yi amfani da na'urar tantance sahihancin mazu zabe, wato Card Reader a zabukan da ake shirin yi a watannin Faburairu da Maris, kamar yadda aka yi a zabukan 2015.
Mai magana da yawun hukumar, Mallam Aliyu Bello ya ce ganin yadda na'urar ta taimaka wajen gudanar da sahihin zabe a shekarar 2015, ya sa a yanzu ma za a yi amfani da ita.
To amma hukumar ta ce ba za a yi amfani da na'urar ba wajen aikewa da sakamakon zaben shugaban kasa daga jihohi zuwa hedikwatarta dake Abuja - sai dai a kai sakamakon a takarda.
INEC ta yi wannan bayani ne makwanni bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi watsi da wata doka da majalisar dokokin kasar ta amince da ita wadda ta nemi a wajabta wa hukumar amfani da na'ura, a dukkan tsarin zabukan.
Mallam Aliyu Bello ya ce a cikin shirye-shiryen da hukumar ke yi don ganin an yi sahihin zabe, ta kara inganta sauri da kuma nagartar na'urar yadda ba za a samu wata matsala ba.
Ana dai amfani da na'urar Card Reader ne wajen tantance katin zaben masu kada kuri'a.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai