Hotunan bikin nadin Atiku sarautar Wazirin Adamawa

Asalin hoton, Twitter/@atiku

Bayanan hoto, An yi bikin nada dan takarar shugaban kasar Najeriya na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin Wazirin Adamawa na bakwai ranar Lahadi

Asalin hoton, Twitter/@atiku

Bayanan hoto, Tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo na cikin manyan bakin da suka halarci bikin wanda aka yi a Yola, babban birnin jihar Adamawa

Asalin hoton, Twitter/@saraki

Bayanan hoto, Shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki (dama) na cikin manyan bakin da suka halarci bikin

Asalin hoton, Twitter/@saraki

Bayanan hoto, Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan (tsakiya) ya halarci bikin

Asalin hoton, Twitter/ @YakubDogara

Bayanan hoto, Kakakin majalisar wakilan Najeriya Yakubu Dogara (tsakiya) da sanata Nazifi Gamawa(dama) da kuma tsohon shugaban hukumar kare hadurra ta kasar, Osita Chidoka (hagu) wurin nadin sarautar Alhaji Atiku Abubakar

Asalin hoton, Twitter/@benmurraybruce

Bayanan hoto, Sanata Ben Murray Bruce (na dama a tsaye) a wurin bikin nadin sarautar Alhaji Atiku Abubakar

Asalin hoton, Twitter/ @YakubDogara

Bayanan hoto, Manyan baki a jere wurin nadin sarautar Wazirin Adamawa na bakwai

Asalin hoton, Twitter/@basheer_is1

Bayanan hoto, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso lokacin da ya sauka a filin jirgin birnin Yola domin halartar bikin nadin Wazirin Adamawa