Da alamu raguna za su yi kwantai a Nigeria
Asalin hoton, Getty Images
A dai-dai lokacin da ya rage kasa da kwana bakwai a gudanar da bukukuwan babbar sallah, a Najeriya raguna na nan jibge a kasuwanni babu masu saya .
A wannan shekarar, da dama daga cikin masu sayen Raguna da wuri-wuri kamar yadda aka saba a baya, ba su halarci kasuwa ba har zuwa yanzu.
Masu sayar da dabbobi a kusuwanni sun ce, duk da kudaden ragunan sun banbanta da na bara, ba a zuwa ana saya sosai.
Masu sayen ragunan da yanzu suka siya, sun shaidawa BBC cewa, farashin ragunan a bana da sauki idan aka kwatanta da na bara.
A bara dai sai da aka kai raguna sayarwa a kasuwanin Jamhuriyar Nijar daga Najeriya sanadiyar tabbarbarewar darajar da kudin kasar wato Naira ya yi.
Tambayar ita ce, shin ko a bana ma saboda rashin cinikin raguna yayin da Sallah ke karatowa zai sa 'yan kasuwa fita da ragunan nasu zuwa kasashen waje?
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai