Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda wasu kurame suka gudanar da aikin Hajji
Jani Hussain ta tuna ruɗanin da ta shiga lokacin aikin Hajjin ta na farko zuwa Makkah tana da shekara 13.
"Na tuna lokacin na ga mahaifiyata na kuka," in ji ta, amma na kasa gano abin da yake sa ta kuka, abin tausayi ne."
A kowace shekara, miliyoyin mutane kan je Saudiyya domin yin Umrah, wato ibadar da Musulmi ke iya yi a kowane lokaci, saɓanin Hajji wanda wajibi ne sau ɗaya a rayuwa kuma yana gudana a watan ƙarshe na kalandar Musulunci.
Dukansu ibadu ne da suka haɗa da yin ɗawafi sau bakwai a Ka'aba, wadda ita ce mafi tsarkin wurin ibada a Musulunci.
Ga yawancin mutane, wannan tafiya tana cike da imani da farin ciki inda za a ji sautin kiran sallah a Masallacin Harami tare da sautin takun kafafu da kuma addu'o'in dubban-daban na mahajjata.
Amma ga waɗanda ba sa ji, wato kurame, aikin hajjinsu yana gudana cikin shiru.
Ba sa jin irin sautin da sauran mahajjata ke ji kamar wani rukunin mahajjata masu lalarar ji da suka fito daga Birtaniya zuwa Saudiyya tare da ƙungiyar Al Isharah, wata ƙungiyar da ke taimaka wa masu lalurar ji su fahimci addinin Musulunci.
Ana ganinsu suna riƙe da laima ja domin su riƙa gane juna kada su ɓace a cikin taron mahajjata.
Tare da su akwai mai fassarar harshensu ta hanyar yin wasu alamomi da hannaye, Zainam Bostan, wadda ke taimaka musu wajen fahimtar abin da ke faruwa yayin ibada.
An haifi Jani Hussain a kurma, kuma tun tana ƙarama ba ta yawan zuwa masallaci domin ba ta iya jin huɗuba, ibadu ko addu'o'i.
Saboda haka, lokacin da iyalanta suka kai ta Makka tana matashiya, ta ce tafiyar ta zama kamar babu inda ta je domin ba ta fahimtar abin da ke faruwa.
Har ma ta ce ba ta san menene Ka'aba ba a lokacin.
Alaƙarta da addinin Musulunci ta canza ne daga baya, tana da shekara 25, lokacin da ta samu damar halartar ibada da ake gudanarwa gaba ɗaya da harshen kurame.
A nan ne ta fara fahimtar Alƙur'ani da addu'o'i cikin sauƙi.
Haka ma wasu daga cikin rukunin, Riaz Rafiq da Zahid Nasser, sun bayyana daidai abun da ta faɗa.
Nasser ya tashi yana zuwa makarantar addini ta masu ji, amma ya kasa koyon karatun Alƙur'ani ta hanyar da aka saba, wato ta karatu da maimaitawa.
Shi kuwa Rafiq ya ce fahimtarsa game da addini ta fara ne bayan ya haɗu da wani kurma Musulmi a kwaleji.
Kafin haka, ya ce bai ma san irin abincin da ya halatta ko bai halatta ba.
Rafiq ya sha ƙin amincewa da gayyata zuwa Hajj ko Umrah daga iyalinsa saboda lalurarsa.
Amma lokacin da ya samu labarin wannan tafiya da ke ba da cikakken tallafi na harshen kurame, domin fahimtar da masu lalurar ji, sai ya yarda ya tafi.
Abokansa ma sun ƙarfafa shi da cewa: "Ka tafi kawai."
Fara aikin hajji
Da isowar rukunin Makka, tasirin wurin ya bayyana a gare su nan take.
Jani Hussain ta sha ruwan Zamzam, ruwan albarka kafin ta matsa kusa da Ka'aba.
Da ta ɗaga kai ta kalli Ka'abar, sai ta fashe da kuka.
Zahid Nasser kuma ya ji farin ciki a ransa sosai lokacin da ya fara hango Ka'aba a karon farko.
Tare da taimakon na'urar jinsa, yana iya jin girgizar taron jama'a da ke kewaye da shi.
Amma yayin da ya fara ɗawafi, sai ya kashe na'urar domin ya mai da hankali kan addu'arsa.
Riaz Rafiq ya ce yana jin kamar "zuciyarsa ta manne" da wannan wuri mai tsarki.
Hussain ta yi tafiya tare da 'ya'yanta da mijinta mai ji, Lukman.
Ta ce bayan shekaru takwas tana mai da hankali ga tarbiyyar 'ya'yanta, ta ji kamar ta ɗan nesanta daga Allah, don haka ta so ta "sake sabunta ruhinta."
Aikin ɗawafi, wato zagaye Ka'aba sau bakwai, yana da wahala sosai a jiki.
Wurin da ake yin ibadar an tsara shi ne domin ɗaukar fiye da mahajjata 100,000 a kowace sa'a.
Zuwa zagaye na huɗu, 'ya'yanta suka fara kuka suna roƙon su koma gida.
Akwai wani lokaci ma da mijinta ya ɓace mata tare da jaririn da yake riƙe da shi.
Hakan ya sa ita ma ta fashe da kuka lokacin da ta sake ganinsu daga baya.
Samun sabbin abokai
A ƙarshe dai iyalin sun kammala ɗawafi tare kuma sun ji daɗin nasarar kammalawar.
Daga baya, Hussain ta sake yin wani ɗawafin na mata ita kaɗai tare da sauran mata kurame.
A wannan karon, mijinta yana kula da yara, don ta samu damar jin daɗin nata lokaci na musamman.
Mijinta Lukman ya lura da canji a gare ta, ya ce ya gan ta a mafi kyawun yanayinta yayin da take mu'amala da sauran kurame.
Haka kuma, Rafiq da Nasser sun sami sabbin abokai.
Nasser ya ba da misali yadda ya taimaka wa wani kurma ɗan Saudiyya fahimtar sallar Juma'a ta hanyar amfani da alamu daban-daban.
Ya ce suna taimaka wa juna duk da bambancin ƙasashe da launi, kuma hakan ya ba shi farin ciki sosai.
A Birtaniya kuma, Al Isharah na wani aikin fassara Alqur'ani cikakke zuwa Harshen Kurame tare da taimakon kurame masu ba da shawara, masana tauhidi da masu fassara.
Zuwa yanzu an fassara surori 64 daga cikin surorin Alqur'ani 114, tare da wallafa bidiyoyi a tashar YouTube ta ƙungiyar agajin.
Wannan dai na daga cikin manufofin ƙungiyar na kawar da matsalar da kurame ke fuskanta na rashin samun damar koyon addinin Musulunci, wani abu da duka mahajjata uku suka bayyana bayan komawarsu gida.
Nazeer ya ce "A karon farko da gaske na ji kamar ana ganina, ana fahimta ta kuma na shiga cikin masu ibada''.
''Hakan ya tuna min cewa kasancewata kurma bai hanani ibada ba, haka Allah ya ga damar halitta ta'', kamar yadda ya bayyana.
Ga Hussain kuwa, ziyarar ibadar ta sa zuciyarta ta ji kamar ''ta samu nutsuwa''.
"Na daɗe ina jin rashin nutsuwa da yin gagaramba, amma kasancewata kusa ta Ka'aba, ya sanyani nutsuwa, fiye da yadda kalamai za su bayyana'', in ji ta.