Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Asabar 18/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Asabar 18/04/2026

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. 'Iran ta buɗe wa wani jirgi wuta a mashigar Hormuz'

    Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta Birtaniya (UKMTO) ta ce dakarun juyin juya halin Iran sun buɗe wa wani jirgin dako wuta a mashigar Hormuz.

    Lamarin ya faru ne kimanin mil 23 daga arewa maso gabashin Oman.

    UKMTO ta ce ma'aikatan jirgin sun samu kuɓuta daga harin.

    A wani labarin na daban, wasu jiragen ruwan ƴan kasuwa biyu sun ce an kai musu hari yayin da suka yi yunƙurin wucewa ta mashigar, kamar yadda wasu majiyoyi uku suka shaida wa kamfanin dillancin labari an Reuters.

    Ɗazu ne dai rundunar sojin Iran ta sanar sake rufe mashigar Hormuz kwana guda bayan buɗe ta, saboda zargin Amurka da ci gaba da rufe tasoshin ruwan ƙasar.

  2. 'Iran ta fara buɗe sararin samaniyarta'

    Kamfanin dillancin labaran Iran na IRNA, ya bayar da rahoton cewa ƙasar ta fara buɗe sararin samaniyarta ga jiragen daga wasu ƙasashe.

    Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta ƙasar ta bayar da sanarwar cewa an buɗe sararin samaniyar ƙasar da wasu filayen jiragen saman ƙasar da misalin ƙarfe 7:00 na safe agogon ƙasar, kuma sannu a hankali za a ci gaba da jigilar jirage.

    Tuni dai aka buɗe hanyoyin jiragen sama a wasu sassan gabashin ƙasar ga jirage da ke jigila tsakanin ƙasashe.

    Sararin samaniyar Iran ta kasance a rufe tun bayan fara hare-haren Amurka da Isra'ila kan ƙasar a ranar 28 ga watan Fabrairu.

  3. Sojojin Amurka sun hana jirage 21 shiga tasoshin ruwan Iran tun bayan fara rufe su

    Kamar yadda muke kawo muku rahoto a baya cewa, Shugaban Amurka, Donald Trump ya dage cewa matakin rufe tasoshin ruwan Iran zai ci gaba har sai bayan cimma yarjejeniyar dindindin ta kawo ƙarshen yaƙin Iran.

    rundunar sojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya ta ce rufe tasoshin ruwan da aka fara a ranar litinin, 13 ga watan Afrilu, ta tilasta wa jiragen ruwa 21 juyawa tare da komawa cikin Iran, bayan da aka hana su shiga tasoshin jiragen ruwan da ke cikin teku.

  4. Ƙasarmu ta shiga wani sabon babi bayan tsagaita wuta - Shugaban Lebanon

    Shugaban Lebanon ya bayyana cewa ƙasarsa na shiga wani sabon mataki, domin mayar da tsagaita wuta ta wucin gadi tsakaninta da Isra'ila zuwa ta dindindin.

    A jawabin da ya gabatar ta talabijin kwana guda bayan tsagaita wutar ta fara aiki, Joseph Aoun ya ce Lebanon ba za ta sake zama “ƴar amshin shatan kowa ba''.

    Mista Aoun ya ce ''burinmu a bayyana yake, kawo ƙarshen mamayar Isra'ila, da kuma janyewarta daga yankunanmu, da ba wa mutane damar komawa gidajensu don zaunawa lafiya kamar kowa''.

    Ya ƙara da alƙawarin cewa rundunar sojin Lebanon za ta karɓe iko da yankunan kudancin ƙasar da zarar Isra’ila ta janye dakarunta.

    Tun da farko, shugaba Trump ya ce ya haramta wa Isra'ila sake kai hari Lebanon, sai dai bayanai na cewa tun daga lokacin ta kashe mutum guda, sakamakon wani harin jirgi maras matuƙi da ta kai.

  5. Ina ce mashigar Hormuz, kuma me ya sa take muhimmanci?

    Tun bayan da Iran ta sanar da sake rufe mashigar Hormuz ƙasa da sa'o'i 24 bayan buɗe shi, sakamakon yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran ɗin, mutane na ta tambayar ina ne mashigar, kuma ma ya sa take da matuƙar muhimmanci.

    Duk da cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yana samun nasara sosai a yaƙin, wani abu da ake ganin tamkar ya tsaya masa a wuya shi ne batun datse mashigar ta Hormuz.

    Trump ya sha nanata cewa zai tura sojojin ruwan Amurka, sannan ya nemi taimakon wasu ƙasashen domin tabbatar da cewa an buɗe mashigar domin a ci gaba da tafiyar da ɗanyen mai

    Kusan kashi biyar na ɗanyen man da ake amfani da shi a duniya yana bi ta mashigar ne mai girman kilomita 40.

  6. Iran ta musanta iƙirarin Trump na mayar da uranium ɗinta Amurka

    Iran ta musanta kalaman shugaban Amurka, Donald Trump cewa ƙasar za ta yi aiki da Amurkar don gano sinadarinta na Uranium da kuma mayar da shi Amurka.

    Wani jami'in Iran mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ya ce ba a ma taɓa kawo batun a tattaunawar da ake yi ba.

    A ranar Juma'a ne Trump ya yi iƙirarin cewa Amurka za ta yi aiki da Iran don gano duka sinadarin uranium na ƙasar domin tattara shi da kuma mayar da shi Amurka.

  7. Iran ta sake rufe mashigar Hormuz saboda toshe tasoshin ruwanta da Amurka ke yi

    Rundunar sojin Iran ta ce ta sake rufe mashigar Hormuz saboda ci gaba da toshe tasoshin ruwanta da Amurka ke ci gaba da yi, kamar yadda kafofinyada labaran kasar ta Iran ta rawaito.

    Kamfanin dillancin labaran Fars da ke da alaka da dakarun juyin juya halin ƙasar, da kamfanin dillancin labarai na Iran Students da kuma kafar yada labarai ta kasar IRIB, sun rawaito wata sanarwa daga rundunar ta IRGC na cewa mashigin ruwan zai koma "irin yadda yake a baya", inda dakarun sojin za su ci gaba da tsare mashigar.

    A baya mun ga wasu jiragen ruwa na jigilar kaya zuwa hanyar ruwan - amma babu tabbas ko jiragen ruwan soji sun bi ta mashigar ba.

    Sanarwar da sojojin ta fitar ta zargi Amurka da "fashin teku", tana mai cewa "abin da ake rufe mashigar da Amurka ke yi" ya kai fashin teku.

    Tun d afarko Iran ta yi barazanar janye matakin da ta ɗauka na buɗe mashigar ga jiragen ruwa, matuƙar Amurka ba ta kawo ƙarshen takunkumin hana jiragenta wucewa da ta sanya a tekun gabas ta tsakiya ba.

    Sai dai Shugaba Donald Trump ya dage cewa matakin zai ci gaba da kasancewa har sai an cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya, yana gargaɗin cewa watakila ba zai sake tsawaita tsagaita wutar da ake ciki ba idan ta kare ranar Laraba.

  8. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hantsi.

    Abdullahi bello diginza ke muku lale maraba a daidai wannan lokaci, domin kawo muku halin da duniyar ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.