Ƙauyen da ake zargin ƴansanda sun ƙona a Kano
Ƙauyen da ake zargin ƴansanda sun ƙona a Kano
Al'ummomin wasu garuruwa a yankin ƙaramar hukumar Wudil a jihar Kano, da ke Najeriya, sun zargi ƴansanda da ƙone musu gidaje da wuraren sana'a da kayan abinci da kuma dabbobi a sanadiyyar wata hatsaniya kan mallakar gonaki.
Rikicin, wanda yanzu haka yake gaban ƙotu, na da alaƙa da batun mallakar gonakin wata fadama a yankin ƙananan hukumomin Wudil da Bunkure.