Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
City na son Fernandez, Villa na harin James Trafford
Manchester City na duba yiwuwar siyen ɗan wasan Chelsea da Argentina Enzo Fernandez, a wannan kaka. (Athletic - subscription required)
Aston Villa na son mai tsaron raga Ingila da Manchester City James trafford, a mastyin wanda zai maye gurbin Emiliano Martinez, idan dan wasan ya zaɓi barin ƙungiyar. (Times - subscription required)
Liverpool, da Manchester United, da Machester City, da Real Madrid na ci gaba da tattaunwa da AC Milan wajen ganin sun siyi ɗan wasan ƙungiyar Rafeal Leao, kan kuɗi fam miliyan 60. (Mail)
Manchester United na sa ido kan dan wasan Tottenham da Netherlands Micky Van de Ven, da na Brighton Calrlos Beleba. (Athletic - subscription required)
Manchester City ta dage wajen siyen ɗan wasan Nottingham Forest Elliot Anderson, duk da sha'awar da ƙungiyoyi ke nunawa kan ɗan wasan ciki har da Manchester United da Arsenal. (Sky Sports)
Ɗan wasan Manchester United Jadon Sancho, da ke taka leda a Aston Villa a matsayin ɗan wasan aro, sai dai ya bayana amincewar sa na komawa Borussia Dortmund a wannan kaka, yayin da dukkan ɓangarorin suka fara tattaunwa mai ƙarfi kan komawar ɗan wasan. (Sky Sport - in German)
Wakilan ɗan wasan gefe na Ivory Coast Yan Diomande, ya tattauna da Liverpool da Paris St-Germain, sai dai RB Leipzig na son ɗan wasan ya ci gaba da zama a tsohuwar ƙungiyar aƙalla a ƙarin wasu kakkanin wasannin. (Bild - in German)
Ɗan wasan bayan Brighton Igor Julio, zai iya komawa Brazil, yayin da Cruzeiro ke duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan, inda dan wasan ya taka leda a farkon rabin kakar nan a matsayin ɗan wasan aro a West Ham. (ESPN - in Portuguese)
Athletic Club na dab da ɗauko tsohon mai horar da ƴan wasan Borussia Dortmund Edin Terzic a msatyin kociyan su, don maye gurbin Ernesto Valverde. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Wolves, da Bournemouth, da Sunderland na cikin ƙungiyoyin da suka nuna sha'awarsu na siyen ɗan wasan Queens Park Rangers, Rumarn Burrell. (Football Insider)
Brentford na harin dan wasan Dynamo Kyiv Matviy Ponomarenko, a matsayin wanda zai maye gurbin ɗan wasan Brazil Igor Thiago, da zai iya zama daya daga cikin ƴan wasan da Chelsea da Tottenham ke harin ɗaukowa. (Teamtalk)
Nottingham Forest na duba yiwuwar ɗauko ɗan wasan Celtic Arne Engels, a wannan kaka, bayan da da ƙungiya rta sa ta ƙi amicnewa da tayin da aka yi masa na Fam miliyan 25., a watan Fabarerun da ya gabata na 2026. (Teamtalk)
Tottenham na tattaunwa da Sebastian Kehl kan zama sabon daraktan wasannin su, bayan ya bar Borussia Dortmund a watan da gabata. (Sun)