'Tsadar fom ɗin takara na APC illa ne ga cigaban ƙasa'

Lokacin karatu: Minti 3

Kungiyoyin farar hula na ci gaba da bayyana damuwa game da tsadar kudin sayen takardun neman tsayawa takarar mukamai daban-daban da jam'iyyar APC mai mulkin kasar ta kayyade.

A jadawalin da jam'iyyar ta fitar ta sanya mai neman tsayawa takara zai biya naira miliyan 100 don sayen takardar takara da bayyana aniyar tsayawa takarar kujerar shugaban kasa.

Takardar neman takarar mukamin gwamna Naira Miliyan 50, yayin da ta Sanata (Majalisar Dattawa), take a Naira Miliyan 20.

Sai ta dan Majalisar Wakilai wadda ta sanya a Naira Miliyan 10, sannan ta dan Majalisar Jiha kuwa za a saye ta ne a kan Naira Miliyan 6.

Kungiyoyin na ganin hakan na cike da illoli ga tsarin dimokuradiyya da cigaban kasa, tare da habaka matsalar cin hanci da rashawa.

Kungiyar CISLAC mai sa ido a harkar majalisu, da yaki da cin hanci da rashawa, na daya daga cikin kungiyoyin farar hular da ke kallon tsawwalar farashin takardun neman tsayawa takarar, da jam'iyyar ta APC, ta sanya, a matsayin wata gagarumar matsala, ga sahihan masu neman tsayawa takarar mukamai daban-daban a jam'iyyar ta APC a zaben da ke tafe na 2027.

Shugaban kungiyar a Najeriya, Awwal Musa Rafsanjani, ya bayyana damuwarsu game da hakan: ''Damuwarmu ita ce yanzu za a dinga amfani da kudi don a dinga shiga takara ko kuma a nemi mukami.

''Illar hakan kuma ita ce wadanda suka cancanta, suna da ilimi, suna da kwarewa, suna da gaskiya da tausayi, da kishin kasa ba za su iya samun wadannan kudade ba da za su biya na sayen fom, da kuma sauran kudade da ake bukatar su biya ga jam'iyya. A don haka ba za su samu damar tsayawa takara ba.''

Rafsanjani ya kuma kara da cewa: ''Wani abin da kuma zai iya kawo cikas shi ne cin hanci da rashawa za a dada aiwatar da shi a harkar zabe da siyasa a Najeriya. Saboda mutane suna ganin cewa ta nan ne kawai za su shiga su azurta kansu ko kuma su azurta wadanda suke so su azurta.

''Bayan haka kuma siyasar ubangida za ta ci gaba da aiwtuwa, inda wadanda ba su da kudin iyayen gidansu za su ba su kudaden, kuma idan sun ci zaben a ci gaba da rigima, kamar yanda muka gani a jihar Ribas.''

Shugaban na kungiyar ta CISLAC, yana ganin abin da ya kamata a yi a kauce wa shiga matsalolin da ke tattare da tsawwala kudin takarar shi ne.

''Na daya dai muna ganin ya kamata jam'iyyun su dinga sanya kudin da ya dace, ba a tsawwala ba, ta yanda mutane za su iya amfani da kudinsu na halal su saya, ba a dinga amfani da kudin sata ba.''

''Sannan na biyu kuma ya kama a zauna a tabbatar da cewa jam'iyyu suna bin dokar da ta kayyade yawan kudin da mutum zai yi amfani da su a harkar zabe, ba a wuce gona da iri ba, tun da muna da dokar,'' in ji shi.

To, sai dai daraktan yada labarai na kasa na jam'iyyar ta APC, Bala Ibrahim, ya ce tsadar farashin takardun tsayawa takarar kamawa ta yi: '' A harka ta siyasa, harka ce mai cin kudi ainun. Ita kanta jam'iyya da irin wadannan kudade take yin ayyukanta na yau da kullum.''

Dangane da yadda ake ganin yawan kudin ka iya hana nagartattun jama'a shiga siyasa har ma su nemi takara, sai darektan ya ce: ''Nawa ne kudin da aka saka? Za ka ga kudaden nan ba su taka kara sun karya ba, idan ka dubi ainahin mukamin da ake nema.''

''Idan ba kamar mukamin gwamna da na shugaban kasa ba, wanda suka kama daga miliyan hamsin zuwa miliyan dari, sauran za ka ga miliyan ashirin ne, miliyan goma, miliyan biyar ko miliyan shida,'' a cewarsa.

Duk da ire-iren wadannan bayanai dai, masu lura da al'amuran siyasa a Najeriyar, na ganin ya zama wajibi a saukaka kudaden da akan kashe a tsayawa takara da yakin neman zabe, don karfafa samar da shugabanci mai tsafta da nagarta a kasar.