Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman bayanai dangane da yaƙin Iran da ma sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na 23/04/2026

Rahoto kai-tsaye

Aisha Aliyu Jaafar da Isiyaku Muhammad

  1. An mayar da gawar tsohon shugaban Zambia Edgar Lungu ƙasarsa

    Gwamnatin Zambia ta ce an dawo mata da gawar tsohon shugaban ƙasar Edgar Lungu, bayan watanni goma ana taƙaddama kan dawo da gawar daga Afirka ta Kudu.

    Gwamnatin Zambia na so a gudanar da janaizar girmamawa ga Mista Lungu a babban birnin ƙasar Lusaka, wani abu da iyalan sa suka nuna ƙin amincewa.

    Rahotanni sun bayyana cewa an ɗauki gawarsa ne daga wani wurin ajiyar gawa a daren Laraba ba tare da sanin iyalansa ba.

    Babban lauyan gwamnati na Zambia ya ce babbar Kotun Pretoria ce ta miƙa gawar mista Lungu ga gwamnati, bayan da iyalan sa suka yi watsi da batun ɗaukaka ƙarar da suka shigar na buƙatar a soke hukuncin cewa a binne tsohon shugaban ƙasar a Lusaka.

  2. Harin Isra'ila "da gan gan" a kudancin Lebanon ya hallaka wata ƴar jaridar ƙasar

    Firaministan Lebanon, Nawaf Salam, ya zargi Isra'ila da aikata laifukan yaƙi bayan an sake kashe wata 'yar jarida 'yar Lebanon a kudancin kasar.

    Wani harin Isra'ila ta sama ne ya samu Amal Khalil a lokacin da ake cewa tana kokarin tsira a wani gida.

    Jami'an Lebanon sun ce, da niyya Isra'ila ta kai harin kan 'yar jaridar.

    Firaministan ya ce sojin Isra'ila sun hana ma'aikatan agaji kaiwa ga wajen da suka kai harin.

    Ya ce kasarsa za ta kai batun gaban taruka na duniya.

    Sojin Isra'ila sun musunta kai hari kan 'yan jarida ko hana ma'aikatan agaji kai dauki wajen, kuma sun ce suna gudanar da bincike.

  3. Sojojin Najeriya sun kashe gomman ƴan bindiga da lalata jiragen ruwansu a Tafkin Chadi

    Rundunar haɗin gwiwa ta arewa maso gabashin Najeriya, Operation haɗin kai, ta yi nasarar hallaka aƙalla ƴan bindiga talatin, tare da lalata jiragen ruwansu da dama, a yayin wani aiki da suka yi a kan Tafkin Chadi, kusa da yankin tsibirin Kaniram a jihar Borno.

    A cikin sanarwar da kakakin Operation Hadin Kai, Lt. Col Sani Uba ya fitar, sojojin sun kai harin ne cikin daren Talata zuwa safiyar Laraba.

    A cewar sa, ''Jiragen saman sojin rundunar sunyi sintiri tare da tabbatar da kasancewar jiragen ruwan ƴan ta'adda fiye da talatin da suke amfani da su wajen safarar kayayyaki a yankin.''

    Ya kuma ce bayan tabbatar da sun tantance su wane ne, kuma bisa dokokin aikin soji, jami'an rundunar sun kai hare hare ta sama wanda ya lalata jiragen, ya kuma kawo cikas ga ƙoƙarin sufurin kayayyaki.

    Uba ya kuma ce hare haren da suka biyo baya, sun kai su ne kan yan bindigar da ke ƙoƙarin tserewa, wanda ya kai ga kashe kusan mayaƙa 30.

  4. Afirka ta Kudu na bincike kan hare haren da ake kai wa ƴan Ghana a ƙasar

    Gwamnatin Ghana ta ce hukumomin Afirka ta Kudu sun kaddamar da bincike kan jerin hare-haren da ake kaiwa na ƙyamar baƙi a kan 'yan Ghana da ke zaune a Afirka ta Kudun.

    A kwanakin nan hotunan bidiyo da ke nuna yadda ake cin zarafin 'yan Ghana a Afirka ta Kudu sun yaɗu sosai.

    Harin kyamar baki abu ne mai sarkakiya - wanda matsala ta tattalin arziki, da yaɗa bayanai na ƙarya, da sauran wasu matsaloli ke kara rura wutarsa.

    Ana ta samun ƙaruwar zanga-zanga da tashin hankali, inda ake harar baƙi waɗanda ba 'yan ƙasar ta Afirka ta Kudu ba, yayin da ake shirin gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi nan gaba cikin shekarar nan.

    A watan da ya gabata Najeriya ta yi kira ga 'yan kasarta da su yi kaffa-kaffa, sakamakon wata zanga-zanga kan baƙin haure da ta rikiɗe ta zama tashin hankali.

  5. Trump ne zai yanke shawara kan lokacin da za a ƙare yaƙin Iran- White House

    Fadar gwamnatin Amurka ta ce babu wani wa'adi na kawo ƙarshen dakatar da buɗe wuta da Iran, wanda Donald Trump ya tsawaita ranar Talata da daddare.

    Sakatariyar yaɗa labaran fadar, Karoline Leavitt ta shaidawa manema labarai cewa shugaba Trump, zai yanke shawara kan lokacin da za a kare yakin.

    Haka kuma ta kafe cewa datse tashoshin jiragen ruwa na Iran da Amurka ta yi na samun nasara, ta hanyar yi wa tattalin arzikin Iran din abin da ta kira ''KANSHIN MUTUWA''.

    Wakiliyar BBC ta ce Amurka na fata ne na ganin datsewar da ta yi wa Mashigar Hormuz ta sa tattalin arzikin Iran ya jigata yadda hakan zai sa Iran din ta je teburin tattaunawar.

    Shugaban kasar Iran din Masoud Pezeshkian, ya bayyana wannan datsewa a matsayin daya daga cikin manyan abubuwan da suka haifar da tarnaki ga tattaunawar zaman lafiya.

    Ya ce kasarsa a shirye take a tattauna, amma ya zargi Amurka da - da kalamai na munafurci da ba sa karewa.

    A gefe guda kuma, Iran ɗin ta sha alwashin ba za ta sake buɗe Mashigar Hormuz ba.

  6. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar shafinmu na BBC Hausa kai-tsaye, barkanmu da safiyar yau Alhamis, inda yau ma kamar kullum za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Za kuma ku iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa, da kuma kallon bidiyo.

    Da fatan za ku kasance tare da mu.