Abin da Kotun Ƙoli ta ce kan rikicin Masarautar Kano

Lokacin karatu: Minti 5

Kotun ƙoli ta dage sauraron shari'ar rikicin masarautar Kano da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tsakanin Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero da Sarki Muhammad Sanusi kan wane ne halastaccen Sarkin na Kano.

A wani zaman da ta yi a Abuja, kotun ta ƙoli ta ɗage zaman sauraron shari'ar zuwa ranar 19 ga watan Afrilun 2027, wato kimanin shekara ɗaya daga yanzu.

A watan Mayun 2024 ne dai Gwamna Abba Kabiru Yusuf ya rushe tsarin masarautar Kano na lokacin wanda ke da sarakuna biyar ciki har da Sarki Aminu na Kano, bayan sauya dokokin da suka kafa masarautun na jiha.

Tun lokacin ne Sarki Aminu Bayero ke ƙalubalantar sauye-sauyen inda suka je kotuna daban-daban kafin zuwa kotun ƙolin da ta ɗage zaman har na tsawon shekara biyu.

Aminu Babba Ɗan Agundi ne yake jagorantar ƙarar a madadin ɓangaren Sarki Aminu Ado Bayero wajen ƙalubalantar matakin gwamnatin na Kano na rushe masarautun, musamman ma Sarki Aminu.

Abin da ya wakana a kotu

Barista Bashir Yusuf Muhammad, shi ne lauya mai wakiltar Sarki Muhammadu Sanusi II, ya bayyana wa BBC cewa yanayin aikin kotu ne ya sa kotun ta ɗage shari'ar zuwa baɗi.

"Ka san asalin shari'ar, Aminu Babba Ɗan Agundi ne ya shigar da ƙara, yana ƙalubalantar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara wadda ta ce kotun tarayya da ke Kano ba ta da hurumin sauraron ƙarar tun a farko," in ji shi.

Lauyan ya ce a zaman kotun ne hukumar DSS suka ce sun bayar da bayanansu a ranar 14 ga watan da ake ciki.

"A ƙa'ida lauyoyin Babba Ɗan'agundi na da kwana 15 domin mayar da martani, amma kwana 5 ne kawai ke tsakani daga ranar da DSS ta yi bayani. Sai suke nemi kotu ta ɗage shari'ar domin su samu damar mayar da martani."

Barista Bashir ya ce sun yi ƙoƙarin jan hankalin kotu kan cewa lauyoyin sun gabatar da bayani a watan Disamban bara, amma ya ce kotun ta ce doka ce ta ba lauyoyin damar kwana 15.

"Wannan ne ya sa kotun ta auna yanayin lokacin da take da shi na zama, sai ta ɗage shari'ar har zuwa Afrilun baɗi."

Za a iya dawo da shari'ar baya?

Ganin yadda lokacin da aka ɗauka domin cigaba da sauraron shari'ar ya ɗauki hankali, Barista Bashir ya ce kotun ƙoli na da aikace-aikace da yawa.

"Ka san damar bayar da lokacinn zama dama ce ta kotu, kuma Kotun Ƙoli na da aikace-aikace da yawa. Mu kanmu mun yi mamaki, kasancewar shari'ar na da ɗaukar hankali sosai," in ji shi.

Ya ƙara da cewa babu yadda za su yi saboda sun san kotun ƙolin na da aiki da yawa. "Ba za ta neman shawarar lauyoyi ba wajen bayar a lokaci," in ji shi.

Sai dai ya ce za su yi yunƙurin neman kotun ta ƙoli ta rage yawan lokacin na cigaba da sauraron shari'ar.

"Za mu rubuta a rubuce domin mu nemi idan akwai hali a dawo da shari'ar baya. lallai akwai buƙatar a kammala shari'ar nan," in ji shi.

Waɗanda Babba Ɗan'agundi ke ƙara

  • Gwamnatin jihar Kano
  • Majalisar dokokin jihar Kano
  • Ofishin Atoni-Janar na Kano
  • Kwamishinan ƴansanda
  • Hukumar DSS
  • Rundunar civil defence
  • Babban sufeto-janar na ƴansanda

Yadd rikicin ya samo asali

A watan Mayun shekarar 2024 ne majalisar dokoki ta jihar Kano ta amince da rushe duka masarautun jihar bayan soke sabuwar dokar da ta ƙirƙiri sababbin masarautu ta shekarar 2019.

Majalisar ta bayyana cewa rushe sabuwar dokar na nufin cewa za a koma amfani da tsohuwar dokar da ta kafa masarautar Kano.

Sabon matakin da majalisar ta ɗauka ne ya rushe sarakunan jihar biyar na Kano, da Bichi, da Ƙaraye, da Gaya, da Rano.

A lokacin ne kuma majalisar ta gabatar da sabuwar dokar da za ta ƙirƙiri sabbin sarakuna masu daraja ta biyu.

A sabuwar dokar, gwamnatin Kano ta tsara masarautun kamar haka:

  • Masarautar Kano: Masarautar Kano ita ce mai daraja ta ɗaya, inda sauran sarakuna masu daraja ta biyu za su zama ƙarƙashin ikon sarkin Kano mai daraja ta ɗaya. Masarautar mai daraja ta ɗaya na da iko na kai tsaye da hakiman ƙananan hukumomi 36 daga cikin 44 na jihar.
  • Masarautar Rano: Sarki mai daraja ta biyu na wannan masarauta na da ƙananan hukumomi uku wato Rano da Bunkure da Kibiya.
  • Masarautar Ƙaraye: Ita kuma wannan masarautar mai daraja ta biyu ta ƙunshi ƙananan hukumomi guda biyu na Ƙaraye da Rogo.
  • Masarautar Gaya: Ita ma wannan masarautar mai daraja ta biyu ta ƙunshi ƙananan hukumomi uku na Gaya da Ajingi da kuma Albasu.

Shari'o'i kan rikicin sarautar Kano

A ranar Litinin, 15 ga watan Yuli ne mai shari'a Amina Aliyu ta babbar kotun jihar Kano ta umarci sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗu na Rano, Ƙaraye, Bichi da Gaya da su daina ayyana kansu a matsayin sarakai.

Kotun ta kuma umarci sarakunan biyar da su miƙa duk wasu kaya na sarauta mallakar masarauta ga gwamnatin jiha.

Majalisar dokokin jihar Kano ce dai ta shigar da Aminu Ado Bayero da ƴan sanda da sojoji a gaban kotun.

To sai dai kuma kafin hukuncin, babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta yanke hukuncin cewa dokar da ta rushe masarautu a jihar na nan daram amma kuma ta soke aiwatar da dokar wadda gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.

A lokacin yanke hukuncin, Mai Shari'a Abdullahi Muhammad Liman ya ce ba daidai ba ne gwamnan jihar Kano ya aiwatar da dokar soke masarautun saboda akwai umurnin kotun da aka bayar da ya dakatar da duk wani yunƙuri na gwamnan Kano wajen aiwatar da sabuwar dokar da ta cire rawanin sarakuna biyar a jihar ta Kano.

Mai shari'a Liman ya ce "A don haka na bayar da umurnin cewa dukkan matakan da gwamnati ta ɗauka na soke su amma hakan bai shafi sabuwar dokar masarautu ba. Amma sun shafi matakan da gwamna ya dauka ciki har da sanya hannu a sabuwar doka da kuma sake nada Sanusi".

Kotun ta ce "An soke dukkan matakan da masu kare kai a shari'ar suka ɗauka, amma kuma hakan bai shafi dokar ba."

Bisa dokar ne dai gwamna Abba Kabir Yusuf ya rushe sarakunan biyar ciki har da Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma sake naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin sarki na 16, bayan da tsohon gwaman jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tuɓe shi a 2020.

A ranar 23 ga watan na Mayu ne ɗaya daga cikin masu naɗa sarkin Kano, Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi ya ƙalubalanci dokar a babbar kotun tarayyar da ke Kano, sannan ya ce za su garzaya kotu na gaba.