Yadda bukatar sabon bashin Tinubu ke tayar wa da wasu Sanatoci hankali

Asalin hoton, @officialABAT

Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci majalisar Dattijan ƙasar ta amince masa ya amso bashin dala miliyan 516 daga Babban Bankin Jamus domin gudanar da aikin gina babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry da ke jihar Legas, wasu Sanatoci na nuna damuwa kan yawan basin da Shugaban ke ci.

Yayin da wasu ke nuna goyon bayansu ga bukatar Majalisar ta amince wa Tinubun ya karbo bashin, wasu 'yan hamayya na ganin aikin da ake cewa za a yi da kudin, ko a baya ma an taba ware masa kudi har cewa aka yi an kaddamar da shi.

Shugaban ya miƙa buƙatar ne ta hanyar wata wasiƙa da ya aikewa shugaban majalisar Dattijan Godswill Akpabio kuma ya karanta ta yayin zaman da aka ta yi a jiya.

Shugaba Tinubu ya nemi karɓar bashin ne domin gina kashin farko na hanyar da ta tashi daga Badagry a jihar Legas zuwa Illela da ke jihar Sokoto.

Hanyar wacce za ta haɗa yankin Arewa maso yamma da Kudu maso yammacin Najeriya za ta fara ne daga Sokoto ta ratsa ta cikin jihar Kebbi da Neja da Kwara da Oyo da kuma Ogun.

Sannan ta ƙare a jihar Legas, kuma an tsara aikin ne kan tsawon kilomita dubu ɗaya.

Tuni wasu daga cikin 'yan majalisar dattijan suka goyi bayan wannan buƙata ta Shugaba Tinubu, cikinsu har da Sanata Muhammad Adamu Aliero wanda ke wakiltar Kebbi ta tsakiya, wanda ya ce aikin zai samar da damarmakin ayyukan yi da kuma sawwake wahalhalun sufuri.

Sai dai a gefe daya kuma 'yan hamayya irin su Sanata Rufa'i Sani Hanga da ya fito daga Kano, ya ce a matsayinsu na 'yan adawa babu abin da za su iya yi tun da an rinjaye su a zauren majalisar, amma dai abin yana tayar musu da hankali.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

''Ai wannan bukata kusan kullum a cikinta muke. An sha yinta. Kusan duk shekara za ka ga an yi sau biyu, sau uku wannan bukatar ta a sahale za a yi kaza,''in ji shi.

Ya kara da cewa: ''Ni ba na mantawa kwanakin baya ko 'yan shekaru ko watannin baya, an karbi kudi bashi a kan wannan dai aikin da ake cewa za a yi. Har zuwa aka yi aka ce an kaddamar da aikin.

''Ni basukan da ake karba a wajena suna tayar min da hankali, saboda sai in ga kamar yaushe za a biya basukan nan?''

''Ina ayyukan da ake yi da basukan nan?''

''Yaushe za a warware su?''

Titin da ake son a yi ya shafe kimanin shekara 50 cikin taswirar titinun da ake son yi don bunkasa ayyukan sufuri da na kasuwanci a Najeriya sai dai har yanzu hakar masu ikon ƙasar ba ta cimma ruwa ba.

Bashin dala miliyan 516 da Shugaba Tinubu zai ciwo za a biya shi ne cikin shekaru tara masu zuwa kodayake akwai ƙofar ƙarin shekara uku cikin sharaɗinsa kuma akwai kuɗin ruwa da ya kai kashi 5.3 a kowace shekara.