Abin da ya faru lokacin da Sarkin Haɗejia ya gwabza yaƙi da Turawa

Asalin hoton, FB/HADEJIA EMIRATE

Bayanan hoto, Kofar fadar sarkin Hadejia
    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

A ranakun 24 da 25 ga watan Afrilu ne mutanen masarautar Hadejia da ke jihar Jigawa a arewa maso yammacin Najeriya suke tunawa da ranar arangamar masarautar da Turawan mulkin mallaka.

A wannan shekarar, masarautar za ta yi bikin cika shekara 120 da gwabza yaƙin, wanda aka yi a zamanin Sarki Muhammadu Haru Mai-Shahada.

Sukan gudanar a taruka domin tuna irin jarumtar da kakanninsu suka nuna a ranar wajen nuna turjiya ga turawa a zamanin mulkin mallaka a ƙasashen Hausa.

Masana tarihi sun bayyana cewa ranar na da matuƙar muhimmanci, sannan za ta iya koyar da matasa darasi a kan muhimmancin dagiya a tsayawa a kan gaskiya da jarumta.

Farfesa Tijjani Muhammad Naniya na Jami'ar Bayero ta Kano, fitaccen masanin tarihi ne, ya bayyana cewa rana ce da ke da alaƙa da ƙoƙarin Turawa na kafa mulkin mallaka a yankin arewacin Najeriya.

Yadda aka yi arangamar

Asalin hoton, Buhari Sani/Lugude

Bayanan hoto, Gidan Turawa da ke Bariki a Haɗejia

Farfesa Tijjani Muhammad Naniya ya ce, "wato abin da ya faru shi ne yana da alaƙa da ƙoƙarin Turawa na su kafa mulkin mallaka a wannan yanki da ake kira yanzu Najeriya musamman yankin daular Sokoto wato waɗanda suka yi jihadin Usman Ɗanfodiyo," in ji shi.

Farfesa Naniya ya ce Turawa sun yi hikima sun kuma kasance suna kama gari bayan gari, "wato ba su kawo wa yankin farmaki lokaci guda ba. Sai dai in suka kama wannan gari ne, bayan lokaci sai su kama wannan gari."

"Saboda haka ɗauki dai-dai suka yi. To aka zo ko'ina suna kamawa, ba a samun rigima sosai, amma da suka zo Hadejia wato bayan shekara uku da kafa mulkin mallaka."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya ce a lokacin da Turawa suke garin ne aka fara zaman doya da manja, inda ake yi wa juna kallon kallo.

"To sai a shekarar 1906, shi Sarkin Hadejia na lokacin mai suna Sarki Muhammad Bin Haru, wanda ake kira da Mai-Shahada ya fahimci zaman ba zai yiwu ba saboda haka sai ya bijire wa irin wannan yaudara da Turawa suke yi."

Masanin tarihin ya ce a lokacin ne su ma turawa a ƙarƙashin wani kwamandansu da ake kira Captain Phillip suka riƙa amfai da hanyoyi daban-daban ta lumana ta yaudara da sauran su, amma suka kasa samun kan sarkin.

"To kawai sai suka yi a-yi-ta-ta-ƙare wato a yi fito na fito. Shi kuma sarkin Hadejia da kwamandojinsa suka ce, da su ba da kai bori ya hau, a kan a yi wa addininsa hawan ƙawara a karya su, to gwanda su yi shahada ya fi, gwanda a kashe su."

Farfesa Naniya ya ce saboda haka ne suka fito da ƙarfinsu aka gwabza faɗa tsakaninsu da turawan.

"A wannan faɗa ne Sarki Muhammadu Haru Allah Ya yi rasuwarsa. Shi ya sa ma ake yi masa laƙabi da Mai Shahada, wato ya rasu ne yana ƙoƙarin kare mutuncin ƙasarsa da kuma addinin Musulunci, wanda shi Ɗanfodiyo ya sa shi jaddadawa a ƙasar Hausa."

Masanin na tarihi ya ce bayan sarkin, shi ma an kashe kwamandan turawan mai suna Captain Phillip.

"Yanzu haka kabarinsa na nan a Hadejia ɗin. Su ƴan Hadejia ne suka hana a ɗauke gawar domin ya zame wa ƴaƴansu da jikoninsu darasi kuma su tsaya a kan abin da Mai Shahada ya yi don su ma nan gaba su ƙara ganin darajar ƙasarsu da mutuncinsu da kuma addinin Musulunci," in ji Farfesa Naniya.

Hadejia kafin yaƙin da bayansa

Asalin hoton, Buhari Sani/Lugude

Bayanan hoto, Wani ɓangare na gidan na Turawa a Hadejia

Naniya ya ce bayan wannan arangama da aka yi ne Hadejia ta faɗa hannun Turawan, inda suka kafa mulki

Ya ce bayan sun kafa mulki ne a tsarin NA, inda a cewarsa suka kafa gwamnati a Kano, wato Kano Province.

"Sai Hadejia ta zama tana daga cikin Kano Province. Da Hadejia, da su Kazaure da su Gumel duk suka zama suna ƙarƙashin Kano."

Ya ce kafin yaƙin, Hadejia zaman cin gashin kanta take yi, inda ya ƙara da cewa a baya ma manyan garuruwan biyu sun kasance suna yi wa juna kallon kallo.

"Saboda haka, Hadejia tana ganin cewar ita ma fa ta bunƙasa. Kano kuma tana ganin ita wajen tattalin arziki ta bunƙasa."

"Shi ne ma har aka samu saɓani wani lokaci a bayan yakin basasa a nan Kano, Hadejia ta kawo kutse, ta kama wani yankuna a Kano, wanda aka yi ta taƙaddama a kan wannan. Ba a dawo wa Kano waɗannan yankunan ba sai dai Turawan da suka zo suka dawo mata da su."

Darasi ga ƴan baya

A game da irin darasin da ya kamata ƴan baya su ɗauka daga gumurzun da aka yi ɗin, Farfesa Naniya ya ce yana matuƙar muhimmanci a fahimci cewa rayuwa ba jin daɗin duniya ba ce kawai.

"Ƙyale-ƙyale da tara dukiya ba su ba ne rayuwa. Rayuwa ita ce ka san matsayinka a zamanka ɗan'adam kuma a ƙasarka. Ka san gudumawar da za ka bayar, kuma ka san abin da ya kafa ƙasar ka, kuma ka yi ƙoƙari ka kare wannan. Haka ne za ka kare mutuncinka da darajarka, shi ne kowa zai so ka kuma ba zai yi maka hawan ƙawara ba."

Masanin na tarihi ya ce yadda ake yi a ƙasashe da ake rikici duk akan irin wannan matsalar ne.

"Kamar zamantakewa ce a tsakanin mutane: idan ka duba zamantakewa kullun wani ƙoƙari yake ya ga sai ya danne wani. To za ka cika mutum ne idan ka nuna cewa a tsaye kake da ƙafarka babu wanda ya isa ya danne ka," in ji shi.

Ya ƙara da cewa Sarki Mai Shahada ya ce da ya ba da kai wajen Turawa, gara ya mutu.

"Yau ga shi dai kashe shi aka yi, amma yanzu sarakunan da Turawa suka kama ko suka je suka tsare su ko suka kwace mulkin ko kuma suka bar su ma a kan mulkin, babu wanda ya yi suna ya shahara kamarsa, kuma babu wanda yake zama ake la'akari da shi a ƙasar daular Usmaniyya wajen kare mutuncin Musulunci sai shi da na biyunsa Sultan Attahiru na Sokoto wanda shi ma shahadar ya yi."

Ko Kano ta taka rawa a yaƙin?

A game da akwai rawar da Kano ta taka a lokacin yaƙin ko dai ta taimakon Turawa ko masarautar Hadejia, Farfesa Naniya babu wannan maganar.

"Babu wani tarihi da ya nuna Kano ta taimaka domin ita ma kanta Kano ai ta kanta take yi a lokacin. Daidai lokacin da aka yi yaƙin Hadejia ai Kano tana cikin rikici. Sarki Abbas na lokacin a Kano yana cikin rikici. Rikici ya fara faruwa tsakaninsa da wani babban mai taimaka masa ko kuma bawansa da ake kira Ɗan Rimi Allah Bar Sarki." Naniya ya ce wasu sun ce a lokacin turawa sun so ne su canja gidan surautar Kano kwata-kwata kamar yadda suka canja gidan na Katsina.