Liverpool na harin Muani, Mainoo zai ci gaba da zama a United

Lokacin karatu: Minti 1

Liverpool na son ɗauko dan wasan Farasa da Paris St-Germain Kolo Muani a matsayin wanda zai maye gurbin Mohammad Salah, sai dai tana fuskanatar gogayya wajen ɗaukar ɗan wasan daga Juventus. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Ɗan wasan tsakiyar Ingila da Kobbie Mainoo, 21, ya ambata da fatar baki cewar ya amince da sabutan kwantaraginsa na tsawon shekaru biyar da Manchester United. (Sun)

Arsenal da Barcelona na iya zama inda ɗan wasan tsakiyar Portugal Bernardo Silva, idan zai bar Manchester City a ƙarshen wannan kakar. (ESPN Brazil - in Portuguese)

Ɗan wasan Nottingham Forest Elliot Anderson, da na Real Madrid Aurelien Tchouameni, na cikin ƴan wasan da Machester United ke dubawa a matsayin wadanda za su maye gurbin Casemiro. (Telegraph - subscription required)

Brighton na harin mai tsaron ragar Ingila James Trafford, 23, daga Manchester City a kakar wasannin nan. (Florian Plettenberg)

Manchester United da Galatasaray sun shirye suke su shiga gogayya kan danwasan tsakiya na Juventus da Netherlands Teun Koopmeiners. (Tuttosport - in Italian)

Barcelona ce kan gaba wajen ganin ta ɗauki Eduardo Conceicao, yayin da Manchester City, da Manchester United, da Newcastle su ma ke harin ɗan wasan gaba na Palmeiras. Dukkan wani yunƙurin na komawarsa Turai ba zai yiwuwa ba, har sai ya kai shekaru 18 a shekara mai zuwa.(TeamTalk)

West Ham na son ɗaukar mai tsaron bayan Girka Konstantinos Mavropanos, duk kuwa da sha'awar ɗaukarsa da yake samu daga ƙungiyoyin da ke buga Bundesliga, sai dai yana neman a biya kudi masu tsoka (Football Insider)

Chelsea da Manchester United na cikin ƙungiyoyin da ke sa ido kan ɗan wasan Bournemouth da Ingila Alex Scott. (Caught Offside)

Leeds na shirye-shiryen miƙa sabon kwantaragi ga ɗan wasan tsakiya na Wales Ethan Ampadu, 25, idan kwantaraginsa ya ƙare a ƙarshen kakar wasannin nan. (Teamtalk)