Hotunan bikin auren gata a jihar Kebbi
Bayanan hoto, Gwamnatin jihar Kebbi ta gudanar da auren 'yan mata da na zawarawa kimanin 300 a jiharBayanan hoto, Angwayen sun caɓa ado a wajen auren gatan da aka gudanar a jihar KebbiBayanan hoto, An bai wa ma'auratan kayan abinci a matsayin gayan garaBayanan hoto, An kuma samar wa amaren da kayan ɗaki da kujeru Bayanan hoto, Gwamnatin jihar ce ta biya sadakin duka amarenBayanan hoto, Gwamnatin jihar ta ce an zaɓo ma'auratan ne bisa sahalewar iyayensuBayanan hoto, Sarkin Gwandu, Alhaji Dr. Muhammad Iliyasu Bashar ne ya bayar da auren amaren a matsayin waliyyinsuBayanan hoto, Bayan ɗaura auren mai ɗakin gwamnan jihar, Hajiya Nafisa Nasir ta haɗa wa angwayen da amaren walimaBayanan hoto, Kakakin majalisar dokokin jihar Hon Ankwe Zuru ne ya wakilci gwamnan jihar a wajen ɗaurin aurenBayanan hoto, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Mansur Isah Yelwa na daga cikin malaman da suka halarci auren