Seyi Makinde ya lashe zaɓen gwamna a jihar Oyo
Asalin hoton, Seyi Makinde/Facebook
Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya, INEC ta ayyana Seyi Makinde na Jam'iyyar PDP a matsayin ɗan takarar da ya lashe zaɓen gwamna a jihar Oyo a zaɓen ranar Asabar da aka gudanar.
Makinde wanda shi ne gwamna mai ci a jihar ta Oyo ya samu ƙuri'u mafi yawa inda ya bai wa babban ɗan adawa a jihar, Teslim Folarin na Jam'iyyar APC tazarar ƙuri'u dubu 300.
INEC ta ce Seyi Makinde ya samu ƙuri’u 563,756 yayin da Teslim Folarin na APC ya samu ƙuri'u 256,685.
Za mu kawo muku ƙarin bayani nan gaba.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai
{{rankTranslation}}