Martanin da Abba Kabir ya mayar wa Kwankwaso

Lokacin karatu: Minti 3

A karon farko gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusf ya mayar da martani ga tsohon ubagidansa na siyasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso tun bayan raba gari da mutanen guda biyu suka yi.

A watan Janairun ne Gwamna Abba Kabiru Yusuf ya koma jam'iyyar APC mai mulki bayan ficewa daga jam'iyyar NNPP bisa dalilin rikicin da jam'iyyar take ciki.

Watanni biyu kuma bayan nan sai shi ma sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya fice daga jam'iyyar zuwa jam'iyyar haɗaka ta ADC.

Tun bayan raba garin ba a ji bakin Abba Kabir ba kan tsohon ubangidan nasa. Sai dai kuma a ranar Alhamis an jiyo gwamna Abba yana kakkausan martani ga maganganun da Kwankwaso ya yi kan fitarsa daga Kwankwasiyya.

Yayin wata ziya da ƙungiyar mawaƙa da ake kira da mawallafan Abba Gida-Gida suka kai masa ranar Alhamis a gidan gwamnati, gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kakkausan martanin irin wanda ba a taɓa zata ba daga wurinsa kan Kwankwaso.

'An ci amanar ƴan Kwankwasiyya'

Gwamna Abba Kabir Yusuf cikin yanayi na fushi da karsashi ya bayyana mamaki dangane da yadda aka rinƙa ce kururuwar cewa ya ci amanar Kwankwasiyya saboda ya sauya sheƙa.

"Yau maganar da muka faɗa dalilin da ya sa muka bar NNPP aka ce mana maciya amana. Irin wannan hanyar dai aka bi aka fita daga NNPP. To da ƙoli da ta bar NNPP da ƙasa tsakiya da su aka jagoranta suka bar NNPP, su waye suka ci amana?

Yanzu ƴan Kwankwasiyya da suke ƴan Kwankwasiyya da za a bar NNPP ko faɗa musu ma ba a yi ba. An ci amanarsu ko ba a ci amanarsu ba?

Duk wani abun da ya taso a waccan tafiya tamu wallahi ba mu da lefi ko ɗaya. Mun faɗi halin da jam'iyya ta dosa. Mun gano ƙaton dutse ya tunkaro mu. Mun bayar da shawarar yadda za a kauce masa."

'Tsakanina da Ganduje sai dai shawara'

Gwamna Abba Kabir ya kuma taɓo batun da ake yi cewa ya koma gidan Ganduje wanda shi ne mutumin da zai juya gwamnan. Sai dai Abba ya ce al'amarin ba haka yake.

"An ce Abba ya bi Ganduje wato an kwashe akushi an kai wa Ganduje. A Kano Abba ne jagoran (jam'iyyar APC) ko kuma Ganduje ne? To wane ne shugaba? ...ina so na faɗa tsakanina da Ganduje sai dai mutunci amma ba Ganduje ne zai ban umarni ba. Ni ne lida," in ji Abba.

Gawuna ya koma ga Kwankwaso

Dangane kuma da komawar Nasiru Gawuna zuwa jam'iyyar ADC kuma ƙarƙashin Kwankwaso, Abba Kabir ya ce abin ya ɗaure masa kai.

"Yanzu shi kuma wanda yake maƙiyin namu nada wanda ya ba mu wahala a lokacin zaɓe wanda shi Gandujen nan dai shi ne ya jawo shi ya dora shi yau kuma an janyo shi an ce shi ne masoyi. Shin an ci amanar Kwankwasawa ko ba a ci ba?"

Me martanin na Abba ke nufi

Masu fashin baƙin siyasa da ƴan siyasa sun yi hasashen cewa za a kai matakin da mutanen biyu za su yi tankiya musamman idan kakar zaɓen 2027 ta kawo kai.

Kafin wannan lokaci dai an sha ji da ganin wasu muƙarraban gwamnan na fito su yi habaici da gugar zana ga sanata Rabi'u Musa Kwankwaso amma ba a taɓa jin Abba ba.

A farko-farkon fitar Abba daga NNPP, a wani taro na masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Gwale, an ga yadda gwamna Abba ya nemi a ƙwace abin magana daga hannun Farfesa Hafizu Abubakar wanda ya fara tonan silili kan sanata Kwankwaso.

"Wannan na nufin an raba gari kuma lokaci ya yi na fara amayar da abubuwan da ake rufewa. Kuma ai ba ma a fara ganin komai ba sai idan an fara yaƙin neman zaɓe inda kowane ɓangare zai fara tona asirin ɗaya. To lokacin ne komai zai fito fili," in ji wani mai nazarin siyasa da ba ya son a ambaci sunansa.